NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 76 of 146

ko wa kafafunta sun mata Wani irin nauyin gagarumar damuwan data kame duka gabban jikinta da idanuwanta tareda kwakwalwanta ko gani sosai batayi take isowa. Kyallin dayake haskowa daga hannuwan Ayanah dan dake gaba ya saka tenya bude idanuwanta da kyau cikeda tsananin tsoro da mamaki sbd babu macen data taba samun ciki ta koma shimfidarsa a tarihi idan ba matansa ba dan haka ganin silallan zinari kaya guda a hannun Ayanah dake gap da rasa ranta sbd tashin hankali da qunci ya sakata Jin kaman tsoro n kamata sbd alamar cigaba da zuwanta tiraka kenan maana indai tenya ta fahimci sakonsa daidai kariya ce ga Ayanah da cikinta dan kuwa cigaba zuwanta na nufin babu Wanda zai zan da akwai ciki a jikinta kenan. Rawa kafafun tenya suka fara dan kuwa wannan lamari ne me girma ke shirin faruwa boyon ciki a masarautar har zuwa haihuwansa. Zufa ta sharce tana tare Ayanaah data kusa faduwa sbd jiri take suma Sauran bayin suka matso dan gaggawar barin gurin da ita, Sakinah kuwa tinda idanunwata suka sauka Akan tukuicin kwanciya da ake bada wa kullum taji zuciyarta tana sanyi da samun nutsuwa godia ta ringa jero wa sbd babu ciki kenan a jikin Ayanah din. Cikeda kulawa aka isa da ita bangarenta daqyar tayi sallah ta sunkuyar da Kai ta fasa kuka mai cin zuciya tana dagawa Allah hannuwanta biyu da Neman sassaucin wainanna kaddarorin nata da basa qarewa daga wannan se wannan dan ayanzu bata San ta ina zata faraba da ciki a jikinta, Bata taba Jin zata iya cigaba da rayuwa a BOYEM ba daga ranar da Allah ya bata ikon fiddo da jininta Zuhrah daga kurkuku, Bata taba Jin kaunar cigaba da rayuwa anan din ba daga ta samu yancin fidda tata yar uwar amma yanzu ga jinin BOYEM a jikinta datasan babu ta yanda jinin BOYEM zai taba barin BOYEM hakama itama batajin zata iya Hana kanta tsananin son abinda zai fito daga cikinta ba, Wace irin kaddara ce wannan zata kawo yarta duniya ta fuskanta a matsayin yar imebeti. Kuka takeyi sosai tana Neman sassauci a gurin ubangiji tareda Neman zabi mafi alkhairi, Haka ta wuni batareda barin kowa ya ganta ba ko sakinah sedai ta kawo mata abinci ya juya babu wata magana fata shiga tsakaninsu sbd ita sakinah samun nutsuwarta shine koma menene tinda ba cikine da Ayanaah ba to da sauki, ita kuma Ayanaah bata iya maganar cikin kwata kwata da kowa ma dan kuwa zata sakawa ranta babu komai a jikinta tabarwa Allah zabi Akan zuwansa duniya yayi rayuwa ko kuwa sabanin hakan Allah zai zabar mata. Da daddare cikeda farin ciki da Wani irin shauqi tenya da kanta ta shirya ta na musamman takaita tiraka, Shi kansa sultan din Ayau wasu shafikan gamsashiyar alaqa ya bude musu daga shi har Ayanah din wadda batada zabin daya wuce duk yanda yayi da ita, Haka ta share sati tana basa sabuwar nutsuwar da bai taba samuba sbd baya kusantar macen dayake ciki koda matarsa dake haihuwa ce Hutu yake bata saita haihu yana yarta tayi wayonda baa zuwa da ita shimfida tukuna take dawowa. A sati Dayan nan ya samu sauyi da sabbin feelings da dama Akan mace haka ya barta ta tafi hutunta. Batareda sanin kowaba Ayanaah ta fara Renan cikinta da ko sakinah batasan dashi ba sbd Sam kwata kwata tenya kowa duniya Bayan ita bata Bari yasan da cikinba sbd tsaro da tsananin kiyayewa. Ana hakan ne faree ta rasu batareda ta haifi abinda yake cikintaba hakan ne ya saka tenya tsananta kariyarta Akan Ayanah, Abinci da ruwa da duk abinda indai Ayanah ce zata ci sa sakinah kadai ce ta yadda da ita kuma ita tabawa babban matsayin da komai na Ayanah itace kadai yake da haqqin kulawa dashi. Ita kanta Ayanah Wani irin yanayi yafara sauyawa a rayuwarta na tsananin son abinda yake cikinta dayake shigarta ahankali Wanda a lokaci daya kuma tsoro yake shigarta dan kaman yanda bata iya rabuwa da yan uwanta yake tsananin sonsu fiyeda kanta ko Bayan baya tareda dasu haka takejin bazata taba iya rabuwa da abinda zata haifaba koda hakan na nufin bada rayuwarta. A Dayan bangaren sakinah ta samu sanin cikin dayake jikin Ayanah sbd fitowan daya fara yi dan a yanzu yana cikin wata na shida harda kwanaki kuma har lokacin tsananin tsaro take cikinsa na rashin sanin cikin Wanda sultan din da kansa ne bai bata Sallamar da zaa San tana dauke da ciki ba, Babban gagarumin abin mamakin dayake sake saka tenya da MARAKI ma tsoro sosai shine tsawon watannin shida kenan da HAILE ta bugaci samun hutu daga sultan sbd rashin lafiya dan haka tsawon wannan lokacin babu Wanda yake ganinta tana bangarenta a killace tana hutawa, Sultan ya bata hutun datake buqata batareda ya buqaci wasu sabbin imebētis dinba sbd samun kwanaki masu yawa na kasancewa sa AYANAH GHAZ wadda cikinta yake girma a hannunsa da jikinsa dan kuwa sati biyu cif yakeyi da ita kafin yayi sati uku da maraki, HAILE ciki ne da ita da manyan bokayen qasa suka tabbatar mata da haihuwar da zaayi a yanzu kafin kowace haihuwa a BOYEM ta ‘da namiji ce Wanda taurari biyu suke gani a duk lokacinda suka duba da Wanda yake a miqe da Wanda ya karkace amma basu samo maanar hakan ba
🏠