afin ta tashi Zaune a hankali tareda ziro kafafunta qasa ta miqe tsaye slippers masu taushi a kafarta ta nufo kofar ta fito sanye da doguwar rigar qasar me kyau black kanta rufe da qaramin Gyale me hade da niqap din dayake da adon sarka me rawa ta zinari sbd tasan da zaa kawo masu dubata sbd zazzabinta amma bata San abinda zasuyi Bayan hakan ba kuma doka ce me karfin gaske babu namijin dazai iya ganin fuskarta tinda ta zama imebētin sultan me BOYEM gaba daya.
Ko data sako Kai a palon Qamshinta ne ya fara cike palon kafin fitowanta data saka likitocin biyu dauke kansu gaba daya daga kallan hanyar datake tahowar,
Tenya ce take kallanta su sakinah ma gabaki dayansu ficewa sukai kansu a qasa zuwa kitchen ayyukansu,
Sakinah hankalinta gabaki daya kwata kwata yana kan abinda zai faru a palon tana tsananta adduar Allah yasa Ayanah bata dauke da jinin boyem a cikinta,
Cikin nutsuwa likitocin suka nutsu suka gudanar da bincikensu Akan Ayanah wadda dukkanin tambayoyinsu ta amsa a sanyaye.
Bayan dan lokaci suna bincike da bin harbawan jijiyanta suka bar bangaren dan tafiya da sample dinta da zaa auna dan tabbatarwa kafin bude baki ga fadar kowane irin sakamako ne.
Ayanah bata buqatan sanin menene yake damunta sbd ba damuwanta bane ta rayu ko sabanin hakan,
Tenya kuwa Miqewa tayi itama ta fice ta aika aka saka mata ido sosai a cikin sirrin dan tsaro da kiyayewa batason kowa ma yasan da duk abinda zaa fada.
Jiran wuni guda tenya tayi tana jiran sakamakon Wanda ya hanata dukannin sukuni da nutsuwan zuciya hankalinta na kan koma menene,
Daga qarshe tenya da kanta ta isa bangaren lafiyyyar clinic din dake cikin masarautar,
Sai dare ta isa batareda barin kowa yasan da inda ta nufo din ba sbd tasan sosai akwai Idon HAILE Akan duk wani motsinta da abinda ya shafi Ayanah.
Ko data iso Kai tsaye babban likitan ne da kansa ne ya zauna suna fuskantar juna ya sauke Numfashi ya koro mata bayani Kai tsaye ciki ne da Ayanaah qarami.
Ajiyan zuciya da Numfashi mai karfi tenya ta sauke tareda kallan likitan Wanda ta ciro silan danyan zinari ta ajiye gabansa matsayin tukuicin zancen sa ta miqe ta juya ta fice tana Jin yanayi na farin ciki da samun nutsuwa dan Kuwa adduarta a yanzu zata sauya zuwa Allah yasa wannan Karan haihuwan LEUL BOYEM ne tazo mai albarka dazai zamo abin alharinta da uwarsa dan kuwa shine karshen baqin ciki da haukar da zata Kama HAILE dan samun namiji a gurin wata macen da ba ita ba yana nufin zarewanta.
Koda tenya ta isa babu Wanda ta sanarwa da maganar cikin imebēti Ayanaah sbd fitar zancen cikin tamkar miqa rayuwar Ayanah ce ga halaka dan haka ta zabi tayi shiru ta Hana kowa sanin cikin saiya bayyana.
Sakinah Jin shiru kwana daya kwana biyu harma kwanaki babu sakon labarin samun ciki ga Ayanaah ya sakata Jin dan sassaucin abinda take ji na tsoro da tashin hankali ta dan kwantar da hankalinta duk da kullum sake sauyawa Ayanah ke yi alaman mace me ciki yana sake bayyana gareta batareda itama tasan cikin ne yake dauke dashi ba.
A haka satikan hutunta suka cika aka fara shirin fara zuwanta tiraka sedai wannan Karan tenya bata bada umarnin anyi mata shiri me karfi ba Wanda hakan ya tado tsoron sakinah sedai kuma indai har cikin ne da Ayanah dole Ayau zasu sani kuka kowa ma dake masarautar zai gane dan bazata qara zuwa ba,
A al’adance duk macen data samu cikin sultan matiqar an tabbatar tenya ce takeda ikon sanar masa idan takai mace kwanan karshe shi kuma daga wannan ranar zai sallamota ne ta hanyar alamar rashin bata tukuicin kwanciya Wanda hakan na nufin ya gama da ita kenan shikenan kota haihu kawai matsayinta dayane ta haifar masa jininsa,
To wannan alamar ce take sakawa kowa dake masarautar yake sanin mace ta samu ciki sai kuma Bayan lokaci nai dan tsayi kafin a fara shirin zabar masa wasu imebēti din,
Tenya duk wani shiri na nutsuwa da qamshi me sanyi na bankwana da tirakar sultan shi tayiwa Ayanah tanajin damuwan sanin cikin da zuwa yanzu kowa zaiyi,
Karfe goma sha Dayan dare suka iso tirakar tasa wadda kowannensu ya tsaya cak inda shine gurin tsayuwarsu,
Silan zinari dayake da adon hoton tafin kafar jariri a jiki tenya ta bude hannun Ayanah ta saka mata batareda cewa komaiba,
Wucewa ciki Ayanah tayi batareda ta bude hannunta ba bare tasan sakon menene amma dai sanin yawancin sakon masarautar da alama a silan zinari suke Aikasa dan haka a sanyaye ta isa dakin Wanda yayi sanyi sosai qamshin sa datai sati uku bata shaqa ba yayi shiga hancinta yana ratsa kanta cikin sanyi ta dan Lumshe idanuwanta t bude a natse kafin ta fara Takawa da sanyinta sautin karar sarkar kafarta dayake daban dana matansa yana tashi a kowane takunta yana shiga kunnensa da sautin yakewa dadi,
Isowa tayi har inda yake Zaune sanye da Riga da wando masu dan kauri farare qal d suka sakasa komawa tamkar matashin saurayi,
Kanta na qasa ta zube qasa ta miqa masa gaisuwanta da muryanta da babu hayaniya a cikinta ko kadan,
Amsa gaisuwar yayi yana kasa dauke idanuwansa daga k