e take tafiyar bacci ne sosai a idonta.
Suna barin bangaren HAILE na isowa sedai ko data shiga bacci yakeyi Wanda tasan batada ikon ko dogon motsin dazai tadasa amma zuciyarta na cikin mummunan halin da bazata iya riqe kanta ba matiqar da gaske ne imebētinsa da gaske ta wuce lokacinda kowace mace take dauka a tirakarsa,
Juyawa tayi ta fice zuciyarta na Wani irin cizo kaman zata feso wuta dan kuwa kishinta batajin ko yayan daya Haifa bazata iya hallakawa Akan sultan din ba dan haka gabaki daya a yanzu tinaninta da hankalinta zai koma Akan imebētinsa ne da haryanzu bata taba ganinta ba.
Ayanah tinda suka dawo a ranar kwance ta wuni cikin rashin kuzari da dumin jiki na alaman zazzabi kadan kadan dan haka babu hayaniya kwata kwata a bangaren sbd bata damar hutawa,
Inda Allah ya taimaketa ranar ce karshen kwanakinta dan haka zata huta Sosai kafin satikan su dawo.
Da daddare sosai tenya ta iso da masu duba Ayanah din sbd batason wasa da duk abinda zai taba lafiyar Ayanaah dan kuwa Ayau datakai har safe tirakar sultan labarin zai isa kunnen matansa harma da imebētis dinsa dan haka hakan zai iya zama hadari gareta sosai sbd kishin mata masu hadarin gaske ne zai rufeta tako Ina Wanda ta hakanne imebētis da dama suka rasa ransu Shiyasa duk yanda sultan keda imebētis da yawa kalilan ne a raye wainda suma kadan kadan kake Jin Ana cewa an wayi gari kawai sun mutu,
Akwai Wani irin qalubale da hadari mai girman gaske a zama imebētin da zata samu ciki a masarautar BOYEM dan haka a yanzu indai zarginta ya tabbata ciki ne da Ayanaah tabbas zata bata kariya kota halin yaya saita Haifa abinda ya dauka bazata Bari kasheta a banza ba dan hakanne ta Nemo masu dubawar cikin dare sbd Hana maganar cikin fita.
Koda masu dubawan suka shigo da Daren tenya ce a gaba su suna bayanta har zuwa Dayan lafiyayyan palon hutawar Ayanaah din suka zauna ita kuma ta kalli sakinah tace a fito da Ayanah din.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
35
*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Bononza bononza
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah
Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k.
Zuzeam ventures
08144015291
*******
Sakinah dake tsaye kanta qasa zuciyarta na cikin yanayin dayake na sallar tsoro da fargaba harma da tashin hankalin abinda yake shirin faruwa dan kuwa har abada bazaso Ayanah ta dauki cikin sultan din BOYEM ba sbd mummunan hadarin da zata shiga harma ta iya rasa rayuwarta dan kuwa babu wata rai datake da mahimmanci a BOYEM Bayan ta asalin jinin BOYEM din,
Ta ina ta yaya zata iya bawa Ayanah kariya tana matsayin baiwa Bayan tana ganin yanda imebētis ke qasqantarciyar mutuwa ta rashin mahimmanci kuma sun mutu kenan a banza a wofi babu me sake tinasu sai ‘yaya idan sun haifa,
Wani irin nauyi kirjinta yayi lokacinda tenya tace ta korawo ayanah tanajin gabobin jikinta na sanyi idanuwanta na cikowa da hawayen fatar ba abinda ake tinanin bane,
Dakin Ayanah din ta nufa ta taddata kwance ba bacci takeyiba amma idanuwanta a rufe suke tayi shiru lafe a lallausan gadon zuciyarta a narke da damuwan data zamar mata jiki,
Zuba mata ido sakinah tayi tana qure kallanta akanta zuciyarta na sake shiga matsanancin tsoro da tausayi me karfin daya saka hawayen idonta fara gangarowa ta saka hannu ahankali ta shafe hawayen tana kallan sauyi sosai dayake bayyane a jikin Ayanaah din.
Ayanaah din ce ta bude idanuwanta masu haske ahankali kan sakinar sbd taji shigowanta hakama tanajin idanuwanta akanta dan haka a sanyaye ta bude ido ta saukewa sakinar batareda tace komai ba.
Itama sakinar qasa tayi da kanta sbd bazata iya cigaba da kallan Ayanaah ba zata iya fasa kukan dayake cizon zuciyarta,
Numfashi mara sauti ta sauke ahankali tareda bude Baki a natse da sanyi ta sanar da ita kiran tenya.
Tana fada ta juya ahankali ta fice daga dakin sbd kallan da Ayanah ke mata na karaya da rayuwa koyaushe.
Sai datai mintina biyu a kwancen tana kallan kofar da sakinah ta fice k