ta wartsake kafin ya fita ruwan yayi wanka da shower da ruwan dumi har suna fidda hayaqi tukuna ya dauro towel me kauri da girma ya fito wani irin qamshi na biyosa daga toilet din.
Koda yayi fito HAILE na dakin ta iso tana Zaune haskenta na daukan ido qamshinta me sanyi ya gauraye dakin daya sakasa dan Lumshe ido yana qarasowa ya zauna a kujeran dake gaban dresser Sai a lokacin ya dago fararen idanuwansa tas masu girma da tsananin kwarjinn dayake tsinkar da duk Wanda ya kallesu ya sauke a fuskarta ya mata kallan nutsuwa yana sake yadda da babu mace mai kyanta duk da babu soyayya a ransa ta kowace mace amma yadda da HAILE itace mace mafi daraja a Masarautar BOYEM yanzu.
Bude baki yayi ya amsa gaisuwarta a taqaice yana maida kallansa ga madubin dake gabansu ta saka towel ahankali tana goge masa jikinsa a natse da kulawa tareda tsananin sonsa datake Jin koyaushe kaman zai kasheta,
A rayuwarta bata taba rasa komai datake so ba,
Babu abinda batada dashi a rayuwarta tin daga kan dukiya da mulki da kyau da iko amma sultan YASAR BOYEM shine abinda ta kasa mallaka ita kadai yanda take so,
Shine Wanda takejin tana yiwa so kamar ma fiyeda yayanta sbd babu namiji a cikinsu,
Shine Wanda take iya yin komai a Kansa ciki kuwa harda daukan rayukan mutane datake Jin ba komaiba,
Shine Wanda bazata iya taba barin ya San soyayya ba idan ba akanta ba dan kuwa ita kanta haryanxu tasani sultan yasar bai taba son kowace mace ba harsu da suke matansa babu asalin soyayya a tsakaninsu kawai dai yana aurensu kuma yana samun yanda yake so a tattare dasu hakama yana tareda dasu ne sbd sanin kowane sarki baya taba cika ko zama Sarkin saida mata da iyali a kansa,
Idan har sultan Yasar ba ita ze so ba har abada bazata taba barin ya dandana menene soyayyar gaskia da gaskia dan kuwa a littafinta baa ma haifi macen da duk duniya sultan Yasar zai so ba Bayan ita.
Harta gama goge jikinsa ta dauki mai me Laushi da qamshi tana shafa masa bata Dena kallansa ba kaman zata hadiyesa kaman zata bude zuciyarta ta sakasa ta rufe kowa a duniya ya Dena ganinsa Bayan ita kadai.
Cikin Kayan Shan iska da hutawa ya shirya ya Dora jallabiya milk me kyau da tsada tareda santsi ya nufi gurin sallar dake cikin dakinsa ya tada sallar laasar,
Yana idarwa abincin dayafi karfin cikin kusan Mutum goma aka kawo aka jere reras a makeken dining table din dake palon sa na biyu acan ya isa yaci abinci daidai cikinsa,
Yana gamawa Maraki na shigowa itama da tata hidimar dole HAILE ta fice tabar bangaren,
Baccin nutsuwa da sake samun wartsakewa yayi nai dadin gaske har yamma sosai tukuna ya farka yayi wanka ya sauya kaya zuwa jallabiya mai duhu da wata black and golden kyabba mara nauyi data fito da haske da zallan kyansa na asalin jinin BOYEM.
Sallar magrib ya fito a babban masalaccin dayake cikin fadarsa Wanda securities ne dashi shima masalaccin hakama manyan Masarauta ne suke sallah a cikinsa,
Koda ya fita baya dawowa ciki sai yayi sallan ishai Wanda yana shigewa kuma babu me sake ganinsa sai wata safiyar.
Karfe takwas da rabi harma da mintina ya shige kuma yana shigewa ake rufe kowane gate na Masarauta babu shiga babu fita sai kuma Washe gari dan haka koina y sake kamuwa da nutsuwan tsit dan kuwa dole kowa ya gama abinda yake ya shige ba hayaniya koda kuwa kana nesa ne.
****Adaidai wannan lokacin Ayanah ce a cikin pool din da zatai wankan zuwa tirakar Sultan a daren,
Bayi sama da hudu ne a kanta suna zuba mata ruwan dumi da qamshi a hankali tin daga kanta suna sauka kan fuskarta da gangarowa jikinta da santsi sbd fatarta datai Wani irin Laushi da santsi me yawan gaske,
Idanuwanta a rufe suke bata iya budewa ba sbd bata buqatan kallo ko ganin komai da ake mata,
Sakinah na cikin masu gagarumin shirin nata Wanda dukkanin kowane motsin sakinar jinsa takeyi yana yanka da Sosa zuciyarta sbd ganin yanda Ayanaah ta gama mutuwa daga gangar jiki har zuciya babu abinda ya rage hakama daga daren yau Ayanah ta tashi daga ayanarta sedai sabuwar uwargijiyarta a karo na biyu,
Koma dai menene yayane tana fatar daga Daren yau rayuwar Ayanaah tayi sauyi zuwa mafi alkhairin rayuwa da ci gaba tareda warakar dukkanin baqin cikin dayake dunqule a zuciyarta.
Mintina kusan arbain aka share zuwa awa daya aka gama wankan kafin aka bata damar datai wankan karshe da kanta tukuna ta fito daure da towel brown gashinta dayake a jiqe ya kwanta manne a fatar wuyanta zuwa bayanta hatta ruwan dayake diga daga gashin nata qamshi suke fiddawa sbd yanda akai mata wankan turare.
Sakinah ce ta riqo hannunta daya a cikeda tsantsar ladabi da kulawa kanta a qasa sbd daman jiran fitowarta suke jira bisa umarni.
Gaban babbar madubin dake dakin mai tsari da Kayan shirinta birjik jere a gabansa suka nufa ta zaunar da ita sbd Ayanah din ta koma tamkar makauniya sai yanda akai da ita kawai.
Goge mata kanta suka fara yi zuwa bayanta aka tsane ruwan kafin aka dauko handryr aka fara busar da gashin Ana turara masa turaren wuta masu qamshi na larabawan BOYEM tar