ta akan kafafunta shiru idanuwanta Lumshe tamkar fresh fulawa sabon tsiro.
Karfe tara na safe aka shigo dakin nata aka sake hada mata wasu ruwa masu fitinanniyar qamshi da wani abu a cikinsu aka sakata cikinsu Zafin su na ratsata zuwa cikin jikinta take gashin jikinta suka miqe tanajin hatta kanta saida ya sara yayi mata nauyin daya sakata bude idanunwata data Lumshe ta rufe Bayan shigarta ruwan,
Ruwan ta kalla cikin sanyi kafin ta sauke Numfashi me dumi tana Ji suna sake shigarta sosai suna saka jikinta daukan dumi sosai,
Tsawon awa kusan biyu tayi a cikin ruwan kafin aka fiddo da ita aka fara shafe jikinta da Wani irin hadin danyar madarar datake hade da manshanu danye da baa rabasu ba,
Ahankali ake shafe jikinta Ana murzawa tamkar Ana gudun fatarta ta yage,
Ana gama shafe wa wani turaren hayaqi aka fara mata yana saka abinda aka Shafa mata kama fatarta da shiga tsigan jikinta dan kuwa hatta dogon gashinta saida aka shafe sa tas dashi,
Tenya ce da kanta ta shigo Ana biye da ita dauke da farar kakkaurar madarar shanu me Zafin gaske ta dauka da hannunta ta miqawa Ayanaah din wadda hannu kawai ta miqa batareda ta dago ba ta karba takai bakinta ba musu ba cewa komai ta fara sha a natse jikinta sanyaye.
Sai data shanye kafin aka kawo ruwa masu zafi da kyau da qamshi aka fara zubawa a jikinta Ana wankewa tana Zaune cikin pool din da babu ruwa daga ita sai abinda iya nonuwanta kadai ya rufe sai wandon da shima baida banbanci da pant Wanda shima kusan har ciki an shafa komai,
Wanketa tas akai kafin aka bata damar wanka da ruwan sabulu masu tsananin tsada da qamshi,
Ta jima a ciki gurin wankan kafin ta fito sbd acan din kukane mai tsananin karfi da sosa zuciya tayi sosai kafin tayi wankan ta fito.
Komai da a yanzu ake kawo mata tana amfani dashi na musamman ne dan haka body lotions ne masu tsada hadin qasar BOYEM da body oils tareda turaren da ya gama kama jikinta dan kuwa ko bata shafa komai ba ko batai wanka ba wani qamshi ne yake fitowa a jikinta Wanda ya gama kama koina har gashin jikinta dan yanda ake turara Kayanta haka ake tirara ta.
Bayan ta gama shiryawa cikin wata doguwar rigar qasar kuwait black da mayafinta a kanta daure kalan daurin al’adar qasar breakfast aka kawo mata Sai a lokacin tayi tana gamawa lokacin sallah yayi tana sallah batasan lokacinda bacci ya dauketa ba a kwance kan lafiyayyan gadon dakin sbd madarar da ake bata akwai maganin saka bacci dan samun nutsuwar gangar jiki data Kai gashi duk tsayin Daren bata rintsa ba dan hakanne baccin ya samu daman dauketa sosai.
**********Karfe hudu na yammar ranar motoci sama da goma ne suka isa airport din BOYEM dan dauko SULTAN YASAR ALMAZ BOYEM Wanda a duka kaf motocin babu Wanda bata haura mahaukatan millions ba kudin siyanta,
Ko motocin securities din masarautar ba qanana bane dan haka kusan 30 min kafin saukar private jet dinsa suka isa airport aka zagaye koina na hanyar fitowa da securities masu tsananin gaske hakama daga lokacin da jirginsa ya sauka airport din babu motar da zata bar airport din sai motocinsa da securities dinsa sun wuce sbd matsayi da tsantsan ikon da Masarautar BOYEM take dashi take kuma bugawa kaf zamanin babu me matsayin dayake bugasa komai muqamin kasar dakake dashi.
Jirginsa na sauka ba bata lokaci motoci suka iso har bakin jirginsa suka daukesa aka bar airport dashi cikeda tsaro ba hayaniya zuwa Masarauta,
Tafiya bame tsayi sukai ba aka iso gida tin daga nesa securities sukai saurin bude gate suna mimmiqewa tsaye qame a jere kansu a qasa.
Haka motocin suka wuce ciki kaf har zuwa gate na biyu Wanda taron yan fadarsa suke duk matsayin su da muqaminsu da suke dashi na masarautar matiqar sarki yayi tafiya ya dawo dole ne suka tarbesa duk da baa dawowa dashi ya tsaya koina sai cikin tirakarsa sai daga baya yake fitowa fada koma Washe gari ko Bayan kwana biyu amma duk da hakan dole ke duk tafiyar da yayi ya dawo duk wani me matsayi a Masarautar BOYEM sai ya fito ya tarbesa,
Ana isa gate na uku mota biyu ce kadai ta wuce ciki wadda daga wadda yake ciki sai wadda babban amintaccensa da securities dinsa na hanyar tirakarsa suke ciki.
Motocin na shigewa gate din na uku aka rufesa ruf babu kuma mai iya ganin sultan din sai ranar daya gama hutawa ya fito iyalansa kadai ke suke da ikon ganinsa a wannan gabar dan haka koina ya sake daukan tsit me qasar BOYEM ya dawo komai nisan kilometers din dake tsakaninka da ina yake matiqar kana cikin BOYEM palace din to Ka tsananta nutsuwa da kama jikinka dan kuwa yana dawowa akwai sautin da ake bugawa Wanda kusan duka babban garin saiya dauka.
Idan akace Aljannar duniya gurin tsara bangaren sultan YASAR to an taqaita ne kawai sbd Kai tsaye kana shiga tin daga hanyar da zata kaika palon farko na isa tirakarsa zakaji jikinka ya mutu ko kafafunka sai kayi daqyar kake dagawa,
Doguwar hanya ce datake tsit tiles din da zaka Dora kafafunka kayi tafiya ya dauki Wani irin sanyin da duk Taku kake jinsa har cikin qwaqwalwarka,
Qamshi da zakaji