da tenya ta yadda ta Barwa hidimart sbd labarin Kyan Ayanah GHAZ na isa gurin HAILE zata iya yanke mata hukuncin Kisa Kai tsaye tin kafin sultan ya mallaketa a shimfidarsa dan haka tenya ta saka ido sosai da tsaro akan AYANAH GHAZ kaman yanda take kiranta kafin ta hau shimfidar sarki sunanta ya tashi daga hakan.
Tsaro sosai Ayanah GHAZ take samu daga tenya wadda daga qarshe dauketa tayi daga bangaren gabaki daya ta dawo da ita gurinta sbd barazanar datake ji a jikinta na kusanto Ayanah din sbd kyanta da yayi Wani irin yawan da itama idan ta kalleta Jin takeyi gabanta ma faduwa.
Dawowan Ayanah gurin tenya ya sakata sake shiga ran tenya sbd shirunta daya zamo tamkar nutsuwar datafi ta kowa data sani a rayuwarta hakama hakanan takejin a ranta Ayanah zata iya sauya musu kaddara dan yanda take Jin nacin son kasancewanta imebēti kota halin yaya dan haka ta matsu safiyar Washe garin ranar ta wanye dan sultan YASAR na kan jirgin sauka BOYEM Wanda a Daren goben ne zata isar da Ayanah shimfidarsa da insha Allah take masa fatar samun rabon haihuwa da ita.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
30
*_ZUZEAM VENTURES_*
08144015291
Bononza bononza
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba,
wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online
Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah
Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k.
Zuzeam ventures
08144015291
*******
A Daren Ayanah bata rintsa kona minti daya ba kwance kawai take amma babu ta inda bacci ya tinkaro idanuwanta sbd koda Yazo na iya ido ne babu kowane sauki da sassaucin dayake bawa ruhi da zuciyarta sbd a daidai wannan gabar ta rasa nutsuwa da farin ciki tareda walwala ko sakewa har abada sai kuma ranar data iya saka daya daga cikin jininta biyu da suke raye a idonta dan haka zata rayu ne kawai gangar jikinta na aiki amma Banda zuciya wadda itama bugawa kawai take amma duk abinda zata samu a duniyar nan yanzu bazai taba bata farin ciki Kona seconds ba sbd ta gama rufe babin rayuwarta babu farin cikin dazai shigo bayan qarasa rayuwa da qunci daddabe a ranta kuma a hakan zata bar duniya.
Daga Daren yau shima tana kwana a shimfidar ‘da namiji zata tashi daga AYANAH GHAZ dinta zuwa macen da batada Sauran amfani a duniya Bayan biyawa namiji buqata,
Zata tashi daga Ayanar Ammanta da Abaa dinta harma da Abaas dinta Wanda ya gwammaci mutuwansa akan ganin an keta haddinta Shiyasa ubangiji ya rabasu sbd kada yaga wannan mummunan ranar da Ayanaah bazata taba aure ba har abada,auren dayake fata tayi ya hada zuria da ita,auren dayake da mafi girman Buri akansa sbd shine yayi alkawarin bada aurenta ya karbi zinariya da azurfar sadakin aurenta a hannunsa koda yana qaninta wannan Alkawari ne daya dauka kuma mahaifinsu ma ya yaddar da cika masa wannan burin na shine zai bada auren Ayanah dinsa,
Duka wannan Buri kashe a iya mafarki da Buri zai tsaya,
Aurenta a matsayin ‘ya babba ga shugaban ANJOM kuma mace mafi kyau a GHAZ shine abinda garin ANJOM gabaki daya da ahalinta suke jira sbd sake daukaka darajarsa a garin gabaki daya,
Ashe kaddararta ma babu aure a cikinta kwata kwata Ayau gata zaa kaita a matsayin abar biyan buqata da sauke shaawa batareda daraja ko daya ba,
Ayau itace ranar yancin jiki da sunanta na qarshe sbd daga yau din bazata sake sunanta Ayanaah ba dayake da daraja sosai ga iyayenta da yan uwanta daga yau sedai a kirata da imebēti Ayanah har karshen rayuwarta,
Daga yau ta haramta ga kowane irin namiji har karshen rayuwarta dan haka aure sedai taji sunansa kokuma taga Ana yinsa……
Lumshe idanuwanta tayi ahankali radadin dayake cikinsu ya ratsa har zuciyarta yana sauka maqoshinta ta hadiyesa zuwa cikinta da babu komai a cikinsa sai tarin quncin da dashi zata mutu.
Har asuba bata rintsa ba bata kuma iya dogon Motsi sbd Sam hanayaniya ya dade da fita rayuwarta bare doguwar magana dan haka sai hakan yake sake qara mata kaman aji da nutsuwa,
Nafila tayi kafin lokacin sallar asubar yayi tayi sallah ta sake miqa dukkanin lamarinta ga ubangiji har gari ya waye sosai tana Zaune kan