NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 60 of 146

aici da ukuba wannan shine hukuncinta…… Wani irin Juyawa duniya tayi da Ayanaah wadda ta bude baki da karfin gaske ta fasa Ihun kiran Zuhrah cikin rikitaccen kukan daya saka sakinah sake saka karfinta duka tana danneta tareda rufe bakinta d karfin gaske itama tana hana nata Ihun gunjin kukan fidda sauti. Fizge fizge Ayanah keyi tana dukan hannuwan sakinah son qwacewa ta tafi ga Zuhrah kome zaayi musu Ayi tare amma Sam sakinah ta saka karfi sosai ta danneta da gaske sbd tana fita dukansu su ukun rasa rayuwarsu zasuyi dan haka dole ta hana Ayanah dan yanzu ita da zata zama imebēti itace hope dinsu harma dana fiddo Zuhrah cikin wannan mummunan hukuncin na qarshen rayuwa. Gap da su aka kawo Ana wucewa fuskan Zuhrah dake jina jina da jini tana fuskantar saitinsu idanunwata a rufe Wanda ya saka zuciyar Ayanah kasa dauka ta daga hannu tana miqawa zuciyarta na rage bugawa tana sake kokarin fizgewa tana ihu sosai a zare amma Sam babu sauki a riqon da akai mata tana kallo har aka bace da Zuhrah zuwa inda bazata sake ganinta ba har karshen rayuwarsu kila. Wata irin jijjiga takeyi tana Ihun Wanda har jikinta ya fara sakewa ahankali ta some a jikin sakinah din gaba daya numfashinta na tsayawa. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 29 *_ZUZEAM VENTURES_* 08144015291 Bononza bononza Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah -Da 5k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani, -Da 10k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 3k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma, Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k Idan kin kawo mutun goma suka shiga na 5k kinada package din 3k. Zuzeam ventures 08144015291 ******* Cikin tsananin sabon tashin hankali da tsananin tausayin Ayanah dake kashe duka jiki da zuciyarta ta fara girgiza Ayanah din da dan karfi tana ambatar sunanta da sauti qasa qasa amma ba alaman Ayanah din zata motsa ko alamar akwai Sauran rai a jikinta dan haka da sauri ta saka qarfinta ta daukota a bayanta tana waiwayen hanya dan gudun a Gansu ta ringa bin bango a tsorace da firgici ta koma har dakinsu ta fada gado da ita tana sauke wani wahalallen numfashin gajiya da tsoro da firgici, jikinta na rawa ta miqe tazo kofa ta rufe da sauri hadda saka keyi kafin ta dawo inda Ayanaah din tana sake girgiza ta tana ambatar sunanta da sauti mai bayyanar da tsoronta na rasa Ayanah din ga kuma tausayin Zuhrah dake sake sako mata kukan daya kasa ma fitowa zuwa lokacin sedai jan ido da rawar jiki, Ruwa ta dauko hannuwanta na rawa ta zubawa Ayanaah din wadda bata motsa ba saida ta zuba mata ruwa sosai tukuna ta motsa kadan idanuwanta da sukai mummunan ja suna budewa ahankali ta saukewa sakinah su batareda ta kyafta ba ko motsawa tamkar gawar da baa shafe wa idanuwa ba, Hawaye ne masu tsananin zafi suka gangarowa sakinah ta sunkuyar da kanta qasa tana dauke kallanta daga kan fuskan Ayanah da ko kyaftawa idanuwanta basu yi ba tana mata kallan da batasan na menene ba amma dai koma na menene tasan akwai kallan yanke kauna a cikinsa dan haka jikinta yayi sanyi hawayenta na tsananta gudu ta bude baki koina na jikinta na qara sanyi tace ‘Allah ne ya kaddaro muku hakan da gani har ke har Zuhrah babu Wanda zai iya sauya hakan, Allah ya fini sanin dalilinsa na yin haka hakama yafi ki sani yafi Zuhrah sani harma da duka masarautar BOYEM din, Ga dukan alama kaddararki ce ta sako mu halinda muke ciki sbd Allah ya riga kila ya kaddara tarayyarki da sultan YASAR Wanda matiqar akwai rabo a tsakaninku to shine yayi sanadin komai daya faru dan zuwanmu nan, Komai daya faru ya samu yan uwa da iyayenki ki yadda da rabo mai karfin dayake tsakaninku ke kila ya haddaso hakan dan haka ko a yanzu rabon ke dince ya saka yar uwarki sadaukar da rayuwarta sbd bazata iya qazantar dake shirin shiga tsakaninku ba ta hada shimfida daya da Mutum daya ku haifa masa yaya ku hada yayanku uba daya Kina raye tana raye, Kinyi kokarin daukan taki rayuwan Amma Allah ya Hana hakan sbd kece wadda kila ya kaddarowa hakan, A yanzu Zuhrah ta Riga takai karshen tata kaddarar kila dan kuwa har abada mutuwarta ce kadai zata fiddo da ita inda aka kaita waton gawarta ce kadai zata fito idan zaa rufeta
🏠