NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 59 of 146

ady mistress ita ta wuce matsayin imebēti hakama bata zama matarsa ta aure ba amma kuma matsayinta daya da matansa a duniya a zuciyarsa kuma tama fi matan matsayi, Dan haka a koyaushe burin da tenya take kwana dashi take tashi tayi rayuwa dashi shine ta tabbatarda ta samar da wishmah a BOYEM din yanzu wadda zata ruguza power din HAILE koba duka kwata kwata ba to ta tabata sosai dan babu macen datai darajar HAILE a qasar BOYEM yanzu sbd itace mata kuma uwargidan sultan YASAR haka kuma macen datafi kowace macen kyau da iko a qasar. Duk da Ayanah baiwa ce wadda bauta ta sauya mata abubuwa da dama ita ta hango asalin sirrin kyanta Wanda zai fito fiyeda na HAILE idan ta samu gyara da hutun da fata da gangar jikinta suke buqata ga wata irin sanyi da nutsuwa a tattare da ita wanda zai iya sanyaya zuciya mai Zafin gaske irin ta sultan jinin masu BOYEM da kansu dan haka Ayanah tayi mata tako Ina kuma taci burin fiddo da dukkanin kyanta da kwarjininta da bauta ta boye zata fiddota a matsayin sabuwar wishmah ta BOYEM da aka shide qarnika baa samu ba sbd yawancin sarakunan BOYEM basa soyayya dan bata tsarinsu Sarkin uku ne kadai suka taba wishmah Sai a yanzu datake fatan hakan ga sultan YASAR. Umarni ta bada aka tada Ayanah Zaune wadda take kwance kaman babu inda baya aiki a jikinta, Sakinah ce ta saka mata pillows biyu a bayanta suka tareta aka fara bata maganin masu dumi da wani qamshin nutsuwan dayake ratsa hancinta zuwa cikinta, Gabaki dayansa aka sakata shanyewa kafin suka ajiye cup din akan tray din da aka jero cup da bowl din Dayan maganin masu kyau. Dayan maganin aka Dora mata a baki yafara shiga maqoshinta ta rufe idanuwanta ahankali tana Jin taste din maganin na ratsa bakinta aka buga kofar dakin da nutsuwa Wanda ya saka dukansu kallan kofar Banda Ayanah din dake Jin zuciyarta na Wani irin nauyi ta sake rintse ido. Da ido tenya ta basu umarnin su bude dakin dan haka daya daga cikin bayinta ta juya ta nufi kofar dakin a natse ta bude Kai tsaye tana kallan wadda ta bude dakin kanta a qasa ta bude baki da taushin murya tace ‘Daya daga cikin sabbin imebētin da zaayi ta illata kanta harma tana gap da rasa ranta amma……. Wani irin fesowa abinda yake cikin bakin Ayanaah yayi da karfin gaske idanuwanta na budewa jajir sbd abinda taji Wanda zuciyarta ta tabbatar mata da Zuhrah ce, Wata irin rawa hannuwanta da kafafunta suka fara ta yunqura da karfin gaske tana Miqewa tsaye harshenta karyewa sbd mummunan tashin hankali ko magana ta kasa sai idanuwanta dake rikidewa jajir b Kyan gani……… Sakinah ma da jikinta ya dauki wata irin rawar tashin hankali saurin dafe Ayanah itama tana Jin tabbacin Zuhrah ce dan haka hawaye suka fara ciko idanuwanta sbd Zuhrah tayi hakan ne sbd yar uwarta Ayanaah… Ayanah fizge wa tayi daga riqon Sakinah tana Miqewa jiri mai karfi na dibarta tabi bayan su tenya da suka fice dakin batareda sunsan halinda Ayanah din ta shiga ba. Ko ganin gabanta Ayanaah batayi jiri na dibarta na maganin da aka bata Wanda karfinsa yake dan bugarwa sbd na gyaran mace ne, Wani dishi dishi take gani a idanuwanta da duhu duhu amma a hakan take jefa kafarta duk inda ta samu ta nufi hanyar da Batama San Ina zata samu Zuhrah dinba, Sakinah d gudu taje biye da ita tanason ambatar sunanta amma ta kasa sbd kada wani ya jisu asan sun fito komai y qarasa lalacewa dan haka biye take da ita tana wasu irin hawayen tausayi da tashin hankali tareda baqin ciki tana kokarin kamata amma Ayanaah dinba taqi Bari fizge wa takeyi sbd ko zata rasa ranta Ayau sai taje ga yar uwarta. Ragaita Ayanaah din ta ringa yi tana zagayen Neman inda Zuhrah taje amma koina tsit babu Zuhrah ta zube a tsakiyar gurin qasa tareda dafe kirjinta dake mata Wani irin azababben radadi ta fasa wani irin kuka mai karfi da taba zuciyata tareda ambatar sunan Zuhrah da karfi tana sake dafe kirjinta dake Neman bugawa da sauri sakinah ta zube qasa din itama tana rufe mata baki da hannuwanta biyu tana kukan itama mara sauti jikinsu na rawa su dukan, Kuka sosai Ayanaah keyi mai tsananin karfin sautin gaske amma Sakinta ta riqeta jikinta da karfi ta toshe mata baki sautin kukan baya fita sbd idan batai hakanba koina zai amsa karar kukan nata Wanda takeyi d karfin gaske tana ambatar sunan Zuhrah. Motsin tahowa suka Ji Wanda ya saka sakina janta da karfi cikin tausayawa ta boye bayan wani dakin da ita har lokacin riqe take da ita bakinta a toshe. Zuhrah ce aka dauko tamkar gawa a kan wani qaramin gadon marasa lafiya koina jikinta ba Kyan gani jininta ne yake fita sosai Wanda ya sauya kamanninta dana Kayan dake jikinta, Babu alaman rai a jikinta idanuwanta a rufe hannuwanta a sake Mutum hudu ne maza dauke da ita jini na bin hannuwanta zuwa yatsar hannunta yana diga qasa, Tenya ce ta bude baki Kai tsaye cikin iko da bada umarni mai Zafin gaske tace ‘A kaita kurkukun bauta da ukubar da bayi acan zatai jinya t warke tayi rayuwa har qarshen rayuwarta bazata taba fitowa ko wuya ta dauki ranta ko kad
🏠