NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 57 of 146

qasa sakinah ta bude dakin. Tenya ce da kanta tareda masu Binta a baya kaman zasu mata sujjada, Shigowa tayi tana kallan fuskan Ayanaah din wadda fuskanta ta kumbura sosai tayi jajir alaman kuka me karfin gaske tayi, Ajiyan zuciya ta sauke a natse tana sake kallan Ayanah din cikeda mamaki da tinani Kala Kala sbd tinda aka kafa tarihin masarautar babu macen data taba kuka akan zaa kaita shimfidar sarki duk kuwa tsoro da fargaban da matan suke shiga babu wadda ta taba kuka na bayyane sedai na boye na zuci amma Ayau idanuwa da komai na jikin Ayanah bayyanarda tsananin qiyayyrt da hakan yakeyi. Numfashi ta sake saukewa tanajin haka kawai Ayanah din takeson ma idan sultan YASAR ya sauko a Daren ya fara tarawa da ita tsawon sati guda kafin ma a sake kai wata. Murmushi me kyau ta sauke ahankali tana sake qarewa zallan kyau da wani irin sanyi da nitsuwan Ayanah din ido ta bude Baki tace ‘Yaya sunanki?? Sai a lokacin Ayanah ta motsa tareda dago manyan idanuwanta ta sukai jajir ta bude bakinta da sauti me tsananin sanyi da mutuwan jiki tace ‘AYANAH GHAZ’ maimaita sunan tenya tayi cikin kulawa da jin Ayanaah din na shiga tinani da zuciyarta tareda jin tabbas da tanada ‘da namiji yanta Ayanaah din zatai ta aura masa sbd tanada abubuwan da duk takeson mace ta mallaka dan haka koma yayane Ayanah sultan YASAR sai ya maidata cikakkiyar mace. Take ta bada umarnin duk abinda aka kawo na Shan a bawa Ayanah a gabanta ta shanye, Hakan kuwa akai haka aka fara dauko su daya bayan daya Ana bawa Ayanaah din tana shanyewa hawaye masu tsananin zafi suna gangarowa daga idanuwanta Wanda ya saka tenya sake jin Ayanah na zama dole imebēti. Su tenya na ficewa Ayanaah ta darare ta zauna bakin gado tana kallan koina na dakin babu kowane irin abu dazai Baka ikon daukan rayuwanka dan haka zame wa tayi qasa tana jin kaman zata Amayar da zuciyarta. Sakinah na gefe ta rasa abin yi itama se zuru tayi idanuwanta jajir sukai shiru, Zuhrah ma koda aka tafi nata dakin idanuwanta sosai suka nuna abinda idanuwan Ayanah suka nuna amma ita tayi kokari ta hana a gane sbd tasan a duk inda Ayanah take zaa gane yanayinta. A wannan Daren tin daga Ayanaah har Zuhrah babu Wanda ya rintsa a suka kwana cikin tashin hankali da mugun yanayi, Sakinah ma bata rintsa ba a Zaunen ta kwana sbd babu mafita tako Ina a masarautar BOYEM din da gaske komai naka a tafin hannunsu da ikonsu yake, Washe gari yanayin Ayanah sake munana yayi sbd idanuwanta da sukai wani irin mummunan kumburin daya sauya kamannin fuskarta gabaki daya dan haka kai tsaye tenya da kanta yau ta tsaya akan jiqon lallen da akai musu har aka gama tana tsaye ta saka ido babu ta inda ko kallan juna suka samu sukai dan haka suka sake shiga tashin hankali sbd suna tsananin son magana da juna sbd Neman mafitar wannan masifar, Washe gari ma haka tenya ta tsayu sosai da kanta tayi musu komai aka qara tsananta kulawa akansu, Tashin hankali da tsananin tsoronsu koyaushe qaruwa yakeyi sbd kwanakin dake kusanto su, Ayanah gabaki daya rayuwanta ne take jin ta gaji da ita sbd ba iya hadasu da zaayi gurin biyawa Sarkin qasar buqataba da yar uwarta uwa daya uba daya ita kanta batajin har abada zata iya rayuwa a matsayin baiwar biyan buqata a duk lokacinda aka biqaci hakan, Ta zabi mutuwarta a daidai wannan gabar sbd rayuwar da zata yi a yanzu batada banbanci da abinda akaiwa Nurat dinta kafin rasuwarta, Bazata iya zama abinda aka zabeta ta zaman ba dan haka rayuwa gabaki daya ta fita kanta Hutu kawai take buqata daga duniyar. Wannan tinanin ne yake fitar da ita hayyacinta da rashin magana da Zuhrah wadda itama take ficewa nata hayyacin, Wani irin sauyin kamanni ta fara samu Wanda ya saka attention din tenya dawowa kanta sosai ta dauketa ta sauya mata guri kwata kwata aka fara hada mata da maganin saka bacci a cikin abincin da ake bata Wanda bata ma iya ci Sai an tsareta. Fara bata maganin bacci ya saka tinaninta tsayawa cak batada lokacin tinanin komai koyaushe cikin bacci take sbd anason ta samu baccin da zai bawa jikinta lafiya. Zuhrah da baa Ankara da nata tinanin na ganin da gaske babu sauyi a wannan mummunan kaddarar dake tinkaro su hakama kwata kwata ta Dena ganin Ayanah wadda aka kebe daban dan haka zuciyarta ta rasa tinanin kanta batada Wanda zatai magana dashi taji sanyi,batada Sauran hope na rayuwa ko kadan dan haka ta yanke shawarar itama hakura da rayuwan gabaki dayanta dan mutuwarta ce kadai zata hanasu hada wannan kaddarar. A cikin Daren ta cire Kayan jikinta ta saka farcen hannuwanta biyu duka tafara yagar fatar fuskarta da karfin gaske cikin wata irin azaba me tsananin wuyan hadewa tana kukan azaba mara sauyi jini sosai yana fita daga duk inda ta yaga da karfi, Fuskanta da fatar wuyanta zuwa kirjinta da hannuwanta tareda bayanta take yaga tana buga kanta jikin bango sbd azaba, Take jini me yawa yafara lalata inda take karfinta na ragewa ahankali. A daidai wannan lokacin itama Ayanah ta farfado cikin Daren ta tashi
🏠