Wata Mutum daya ce aka sake shigowa da ita ta karshe kafin aka taho da wani sabon lallen mai dan yawa aka zuba a cikin ruwan tareda ruwan zafi dazai qarawa ruwan nasu dumi sosai ta yanda lallen zai ratsa koina a jikinsu sosai.
Ana gama zuba musu komai Juyawa maaikatan sukai gabaki dayansu suka fice daga gurin tareda rufe kofar suka tsare bakin kofar sbd bazaa taba budewa ba sai lokacin fitowansu ruwan yayi.
Daga Ayanah har Zuhrah babu tinanin dayake ransu Bayan son kasancewa a tare daidai wannan lokacin tareda son jin junansu dan haka gabaki daya sun manta da mummunan qazamin lamarin daya sakosu gurin fatansu daya kawai su kasance tare.
Shiru gurin yayi kowacensu su taran da abinda yake ranta na wannan nannauyan kaddarar data hau kansu,
Ratsasu ruwan dumin lallen keyi tako Ina suna jin dumin me zafi har cikin zuciyarsu sbd tsoron d suke ciki yafi komai yawa a cikin zama imebēti sbd kowane lokaci zasu iya rasa rayuwarsu dan haka kowa shiru yayi jiki a sanyaye ba kowane irin dogon motsi.
Ayanaah ce ta bude idanuwanta da sukai jajir ahankali batareda ta juyo gefenta ba ta kalli Zuhrah da suke shaqan Numfashin guri daya ta miqa hannunta dake wata irin rawa sbd shauqin samun abinda zuciya ke so ta cikin ruwan ta Dora tafin hannunta ahankali kan na Zuhrah wadda tana jin saukan hannun Ayanah a kan fatar hannunta rintse idanuwanta tayi wasu hawaye masu tsananin zafi na gangarowa daga idanuwanta kanta na yin qasa ta damqa hannun Ayanah din tana qanqamewa cikin nata hawayenta na tsananta gudu cikeda shauqi da tsananin farin cikin data manta yaya dandanonsa yake a zuciya,
Itama Ayanah hawayen ne ke ciko idanuwanta da sukai jajir tana hana nata hawayen sauka sbd kada a gano halinda suke ciki sedai tata zuciyar harma tafi ta Zuhrah karaya da samun wata irin nutsuwar ruhi da bata taba samu ba tinda rayuwarsu ta wargaje,
Qanqame hannun juna sukai batareda sun juyo sun kalli juna ba ko motsin da zaa gane kowa da abinda yakeji a zuciya da gangar jiki,
Zuhrah kuka takeyi sosai tana sake sunkuyar da kanta qasa sosai tana rokon Allah kada ya raba hannunta dana Ayanah har sai ranta yabar jikinta.
Ayanah ma da kukanta ke komawa zuciyarta kukan zucin takeyi sosai jikinta na wata irin rawa tana sake qanqame hannun da shine hasken rayuwarta.
A wannan yanayin suka share duka awannin da aka dibar musu a cikin ruwan har saida ruwan ya wuce salap suna cikinsa tukuna aka bude kofar tareda shigowa da wasu irin tsaftaccin towels masu dan girma farare qal a basket me kyau kowannensu da baiwar da zata basa nasa.
A cikin wata irin saa me girman gaske saiga sakinah a cikin masu kawowan wadda kai tsaye gurin Ayanah ta nufa a natse kanta a qasa tana isa ta durqusa gaban a hankali tareda dago mata kyakkyawan kwandon da towel din yake ciki yana fidda qamshi me dadi.
Cikin karfin Hali zuciyarsu na yanka suka raba hannuwansu kowacensu na Juyawa ta fice batareda kowa yaji muryan kowa ba sbd basuda daman magana baa basu damar ba.
Towel din Ayanah ta dauka ahankali ta daura a jikinta Bayan sakinah ta miqe a natse ta tayata zare halfvst din jikinta,
Juyawa sakinah tayi zata bar gurin kanta a qasa idanuwanta suka sauka akan Zuhrah wadda ke fitowa daga ruwan itama take jiri me karfin gaske ya dibeta saura kiris ta kife Allah ya bata ikon tsayawa dakyau tana hana firgicinta bayyana sbd zata iya rasa rayuwarta.
Tsurawa Zuhrah idanuwanta tayi tana tafiya kanta na tsananin sarawa da abinda take gani,
‘Zuhrah da Ayanah a matsayin imebēti na Mutum daya?’
Wace irin mummunan qazamiya kuma haramtacciyar kaddara ce wannan?
Tayaya Mutum daya zai kusance su kuma su samu cikinsa su haihu?
Tayaya ma wannan tashin hankalin kaddarar zata fara?
Shin Ayanah da Zuhrahn sunga junansu kuwa?
Idan sun gani sun kuwa San menene yake shirin faruwa dasu?
Idan har sun sani tasani zasu gwammaci su mutu su dukan dasu yadda da wannan mugun tashin hankalin’
Koda sakinah ta fito daga gurin bata ganin gabanta sosai sbd tama kasa yadda da Zuhrah ce idanuwanta suka gano mata dan bama zai taba yiyuwaba wannan kaddarar a yanzu kam tayi nauyin da kila dole zaa iya rasa dayansu biyun.
Su kuwa suna gama daura towels din daya bayan aka nuna musu wata kofa suka shiga toilet ne masu kyau da tsari a jere dan suyi wanka da ruwan dumi sosai kafin su fito kowacensu akaita sabon gurin da zata zauna,
Suna shiga gurin a kebe yake dan haka rufe su akai sbd su ayanzu ba kowa akeso yaga jikinsu ba dan kuwa sun zama tamkar Al’aurar da haramun ne ganin jikinsu,
Ana rufe su kowacensu ta nufi toilet daya ta shige aka bar Ayanah a tsaye tareda Zuhrah wadda itama take tsaye cak babu Wanda ya motsa a cikinsu tsawon mintina uku,
Tsit gurin yayi sai motsin ruwan daya fara tashi ahankali na fara wankan da Sauran sukai,
Sai a lokacin Ayanah ta dago ahankali cikin wani irin slow na tsananin mutuwan jiki ta Dora fararen idanuwanta masu kyau da kashe jiki akan fuskan Zuhrah wadda itama dagowan tayi ahankali.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamu