NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 54 of 146

suka rasa, Ayau zuciyarta ta samu abinda ta rasa na haske da bugawa daidai Bayan shekara guda, Ayau dukkanin duhu da yanar dake zuciyarta sun haskaka da ganin gudan jininta ruhinta Zuhrah wadda itama Zuhrah dake cikin tsananin qunci da baqin ciki komai nata sakewa yayi da ganin Ayanaah dinta rayuwarta,kuzarinta,gangar jikinta,bugun zuciyarta harma ganinta sbd a tsawon wannan lokacin ita ko na minti daya bata taba walwala ko farin ciki ko misqala zarratan sbd da gaske Ayanah ce rayuwarta hakama bata tareda kowa da zai kaunace ta ko kulawa da ita ko Wanda zatai wa magana ko kalla taji sassaucin komai ita kadai take rayuwarta babu kowa a cikinta Wanda hakan ya taba rayuwarta da zuciyarta sosai harma da kanta sbd babu abinda take ako Yaushe koda da dare ne Bayan zubawa guri daya idanuwa tana ganin duka ahalinta a idanuwanta ba kamar Ayanaah ba datake tareda Sakinah, Ganin Ayanah a gabanta yau cikin idanuwanta ya gama cike dukkanin gurbin matacciyar zuciyarta da bugawa kadai takeyi babu abinda ya rage a cikinta, Ganin Ayanah Ayau ya farfado da rayuwarta dake gap da barin duniya sbd tana cikin tsananin qunci da azaba sbd a inda take babu sauki ko kadan ta rame sosai tayi Wani irin fayau alaman kowane lokaci ciwon dake zuciyarta zai buga zuciyarta ta tafiyarta itama, Kokarin gazawa kafafunta sukeyi dan mutuwan da duka jikinta keyi yana sanyi amma a hakan take daga kafafunta ahankali tana tako wa ahankali sbd wainda suke tareda ita, Qasa tayi ahankali da idanuwanta a daidai lokacinda suka iso gurin da su Ayanaah din suke tanajin zuciyarta na Wani irin yanka da radadin dayafi na kullum babu abinda ruhinta da gangar jikinta da zuciya ke tsananin so a lokacin Bayan jin jikinta dana Ayanaah ya hadu sun rungume juna sunji dumin juna sun Ambaci sunan juna sun Shafa fuskan juna sunji muryoyin juna, Da zata samu hakan tabbas da ciwon dayake cin zuciyarta zai warke koda kuwa warkewan tafiya ce to tabbas zata so hakan, Ayanaah ma da zuciyarta ke wata irin bugawa kaman zata faso kirjinta ta fado sbd tsananin so da kaunar yar uwarta daya taso mata ahankali ta sauke kanta tana Jin kowane sautin takun Zuhrah na sauka kunnuwanta yana dukan kirjinta a lokacinda suke kokarin wucewa ta gefensu sunaji suna gani kowannensu ya sauke kansa daga kallan junansu, Rintse idanuwa Ayanah tayi ahankali wani radadi na sake cikesu suna yin jajir duk abinda ta juyo tayi magana akansa bace wa yayi daga kanta da tinaninta sbd ganin Zuhrah Ayau ya tsima duka abinda take danne wa da jurewa, Kamannin Zuhrah dinta sun sauya sosai ta koma tamkar ba ita ba duk da tayi haske sosai amma babu abinda kai tsaye yake bayyane a jiki da fuskanta sai damuwa da qunci me tarin yawan gaske da tabbas zata iya rasa ranta da bugawan zuciya, Bude idanuwanta tayi ahankali radadin cikinsu na qaruwa tanajin takunsu har lokacin a bayanta suna tafiya suna nisantar ta. Rufewa idanuwanta da zuciyarta sukai babu abinda take so Bayan sake saka Zuhrah a cikin idanuwanta dan haka ahankali ta juya batareda karfin jiki ba ta nufi cikin itama tana mantawa duka kwata kwata da abinda yasa aka kawo su gurin, Taku sukeyi suna qarasa shiga ahankali a bayansu Zuhrah din Wanda Zuhrah na jin sautin saukar kowane takun Ayanaah din dake bayanta yana karya zuciyarta tana jin a daidai wannan lokacin ma Allah ya cika mata burinta tana taka guri daya tareda Ayanah tana shakar numfashin guri daya da Ayanah,jajir idanuwanta sukai itama tana ci gaba da taku mai sanyi batareda alaman ko juyowa ba kaman yanda itama Ayanah bata dago kai ba kanta a qasa yake tana bin sawun da Zuhrah ke wucewa da idanuwanta kaman ta durqusa ta sumbaci gurin, Ciki gabaki daya inda wani fadeden gurin gyaran jiki da wankan asalin lalle da qamshi dayake cike da pool din ruwan dumi da har wani hayaqi me qamshi yake tashi a cikinsa, Su tara ne cif aka zaba dan haka duk wadda aka shigo da ita ahankali ake tayata zare Kayan jikinta ta shiga ruwan Lallen da qamshi masu dumi Wanda zaa jiqa su a cikinsa tsawon wuni guda kullum haka zaa musu tsawon kwana uku sbd lalle yana tsotsewa da kashe kowace irin cuta dake jikin dan Adam dan haka sai an riqa jiqa su tsawon kwana uku sun rabu da kowace irin cutar wahala dake jikinsu tsaf kafin a fara jiqasu cikin ruwan madarar nonon raqumi shima. Zuhrah dake gaba bayin dake tareda ita ne ahankali suka zare mata Kayan jikinta daga ita sai kamfai irin na jikin kowa Wanda ake raba musu tareda uniform sai qarama rigar halfvest datake kame nonuwansu qarama ce sosai, Kama hannunta sukai suka isa bakin pool din da ita suna riqe da hannuwanta duka biyu ta zura kafafunta ahankali ta shige ruwan idanuwanta da zuciyarta babu inda suke Sai a tinanin Ayanaah dake bayanta wadda itama ahankali aka zare mata nata Kayan take gashinta ya sauka bayanta aka sakota cikin ruwan ahankali ta tako ta iso gefen Zuhrah wadda itace karshen shiga ruwan a tare suka zauna cikin ruwan ahankali gabaki daya jikinsu na shigewa har zuwa sama kirjinsu iya inda ruwan ya tsaya kenan.
🏠