wuya a kone ga zazzabin azabar wutar ga radadi haka suke aikin.
Kwana biyu konuwar tayi ta dan caccabe haka dan haka faree ta sake samun nutsuwa suka ci gaba da hidimarsu,
Sakinah da Ayanah take kulawa da ita sosai idan sun koma daki sai tata wutar ta Riga ta Sauran warke wa amma ba kwata kwata ba gashi kusan sati biyu kenan suma Sauran tasu ta warke sama sama,
Tsoro biyu ne damuwa biyu take cinsu akan konuwar sbd idan ranar zabar imebēti tayi aka sameka da tabon dayake sabo ba tsoho ba to tabbas kanada hukunci me tsauri dan hakan yana nuni da sakacinka dan kuwa ko yancin raunana Kanka baka dashi sam tinda jikinka ma ba ikonka bane dan haka suke cikin tsananin tsoron hukuncin hakan.
********A daren ranar da zaa tara bayi mata kaf kwana Ayanah tayi Zaune itada sakina cikin wata irin damuwa da sanyin jikin hukuncin da sakinah zata iya karba na qaton tabon konuwarta,
Dukansu damuwansu daya ne kada a sauyawa sakinah guri a cikin hukuncinta a rabasu,
Ta Dayan bangaren kuma acan qasan zuciyar Ayanah dake sosuwa sosai da qunci shine inama itace ta kone din,
Basu wani rintsa ba da damuwa me nauyi da sanyin jiki suka gama komai suka fito zuwa aikinsu.
A kaidar zabar imebēti daki daki ake bi dan haka Layi bai iso bangaren imebēti faree ba Sai dare Wanda tenya ce da kanta tareda bayinta kusan su goma biye da ita cikin nutsuwa da taqama da wani irin kwarjininta ta iso take dukansu suka zube qasa hadda faree wadda itama kanta yake qasa sbd ten’ya kwarjininta nada nasaba da matsayin datake riqe dashi na ita kadai ce takeda power ta zabawa sultan macen dazai kwanta da ita,ita kadai ce takeda power ta zabar wadda zata iya daukan cikin sultan ta haifar masa ‘yaya kuma itama tanaji a jikinta insha Allah a cikin zabinta ne zaa samu macen da zata kafa tarihin haifar LEUL na wannan zamanin dan hakanne ma wannan Karan mata shida zata zabar masa lokaci daya yana dawowa saiyayi sati kullum yana Bare sabuwar mace.
Kai tsaye idanuwanta ta sauke akan fuskokinsu zuwa daya bayan daya tana binsu da kallan nutsuwan da kyau ne zalla take gani a tattare dasu sedai kowacensu babban tabo ne a Fuska,wuya da hannuwansu,
Batace komaiba ta zubawa faree ido tana karantar yanayinta kafin ta maida idanuwanta akan tabonsu dayake nuna wuta ce a jikin kowannensu,
Kyansu ta sake kalla da kyau take ta fahimci komai ta tabbatarda meya faru dan haka kai tsaye akan Ayanah ta tsayar da idanuwanta wadda kanta ke qasa.
Cikin bayinta ta kalli daya kai tsaye wadda ta fahimci me take nufi take ta matso gurin Ayanah ta saka hannu ta zare Hular kanta gashinta dayake dunqule take ya zubo ahankali yana sauka a bayanta.
Faree da kanta ke qasa har lokacin wani mummunan yawu ta Hadiye zuciyarta na harbawa da karfe sedai kafin su dake jan Numfashi su fitar take ten’ya ta kalli Ayanah ta bude baki tace
‘Tashi ki bisu’
Ayanaah da bata gane me hakan ke nufi ba miqewa tayi ahankali tareda bin Bayan bayi biyu da akace ta bi tana adduar kada hukuncin da zaa yiwa su sakina daya saka akace ta tafi yayi tsauri.
Tafi me dan tsayi kadan sukai suka isa wani babban guri nai shegen kyau da tsari Wanda a cikinsa zaa yiwa duk macen da aka zaba gyaran fitar hankali na ciki da waje na wata daya.
Tana saka kafarta cikin gurin taga mata a jere tsaye gabanta yayi mummunan faduwa ta tsaya cak tana kallan gurin da idanuwanta Wanda ke fahimtar da ita menene yake shirin faruwa a gurin.
Kasa daga kafarta tayi sbd toshewan da kanta ke Neman yi ta juyo ahankali ta kalli wainda suka kawota zatai magana numfashinta ya dauke cak bakinta ma kafewa yayi komai nata ya Dena aiki ya tsaya cak sbd idanuwanta da suka sauka akan Zuhrah da aka shigo da ita itama……
#MAMUH
#BEST ROYALTY STORY
#BEST LOVE
#LOVE/ROMANCE
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
26
*_UMMU ASLAM COLLECTION_*
08035014107
-Ina mata yan kwalisa masu son burgewa?
-Shin Kayan kitchen na zamani masu sauki da rahusa na kitchen din yan gayu dama na gargajiya kike so?
-shin abayas na yayi da daukan ido da burgewa kike nema?
-kokuwa original misk dahara kuke buqata dan asali?
-kokuwa Kayan GHT na Neman lafiya da gyara kike so?
-ke harma laces da atampopi na alfarma masu sauki kikeso?
To duka kinzo gidansu indai sune abinda kike buqata ba bata lokaci kinzo kin gama samu kawai tintibi UMMU ASLAM COLLECTION 08035014107 duk inda kike zata aika miki.
***********
Dauke wuta kafafunta suma sukai maqoshinta na wata irin bushewa qayau yawun bakinta suma suka dauke,
Wani yaji yaji taji yana cike idanuwanta sbd tashin hankalin da baida ‘dan uwa a gareta,
Zuciyarta kuwa harbawa take a kirjinta da mugun karfi da wani irin rauni dayake gauraye gangar jikinta na ganin Zuhrah Ayau cikin idanuwanta a Karan farko Bayan rabuwarsu kusan shekara guda,
Ayau idanuwanta sun samu haske da rahamar da