NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 52 of 146

a baqin cikin ne a zuciyar faree wadda laulayi takeyi sosai ga qarin baqin cikinta shikenan ta zama macen da har abada bazata sake samun Wanda zai aureta ko kwanciya da ita har sai ranar da sultan YASAR baya duniya dan babu Wanda ya isa yana raye ya kusanci Matar da shi ya kausanta indai ta haifar masa ‘yaya kenan. Baqin cikin dake cin zuciyarta da damuwan hakan ya saka laulayinta yake tsananta bata kaunar kowa ko komai Bayan hantara da kyara da rashin daraja ko kadan babu abinda take yiwa bayin dake mata hidima kaman zasu bata rayuwarsu. Ayanah ma kusan so biyu tana qonewa a hannu da ruwan zafi sbd hidimarta da fadanta, Duk wahalar da Ayanaah Tasha sosai ta rayuwar da suka fito ta qangin bautar kusrah ta wanke sosai lafiyar fatarta ta dawo haskenta ya dawo sosai amma ba duka ba sbd ba lallai ta koma asalin fararta qal ba har abada kila, Tsayin gashinsu ya dawo sosai duk da akai akai ana yanke musu tsayinsa sbd tsafta baa wani son tsayin gasu sosai a gurin bayi dan haka duk Bayan watanni kadan ake yanke musu tsayinsa bawai aski ba kawai dai zaa yankesa baa son ya wuce iya wuyansu ya sauka kafada zuwa bayansu. Gashinta ya dawo sosai da tsayinsa gashi lokacin yanke musu baiyiba dan haka take dunqulesa sosai a cikin hularta ta uniform, Faree dukkanin bayin dake mata hidima kyawawa ne sosai bama kaman ita Ayanah din wadda sanyinta da nutsuwanta ke qara mata kyau da burgewa, Faree jin tayi duk ta tsanesu bata ko kaunar ganinsu dan idan kaddararsu me kyau ce ko a cikinsu zaa iya zabar imebēti koma dukansu zaa iya zabarsu, A duk lokacin data gansu tafasa da ciwon rai zuciyarta keyi dan haka ta dauki hanyar illatasu a cikin dabarar da bazaa taba zabarsu ba, Hakanne ya saka so biyu tana kokarin koma Ayanaah da ruwan zafi sedai Allah bai saka ta taba samunta a Fuska ba sedai hannuwa kuma har so biyun babu inda fatar Ayanah tayi tabo sbd matiqar kanada tabon daya wuce numbernk ta Shedan bauta dake jikinka to Ka haramta ga zama imebēti. Ayau ma umarnin su hada mata ruwan wanke kafa tayi su dukan haka suka hada ruwan mai dumi daidai yanda zai mata daidai a fata suka kawo suna ajiye a gurin hutawanta dake dan madaidaicin American garden dinta dake nan cikin bangarenta, Tamkar wadda zatai wata gagarumar hidima haka aka tsara mata gurin suka shirya mata komai daidai yanda zata Ji dadin hutawan da wankin kafar da zaayi mata, Ayanah da sakina ne biye da ita kansu a qasa a lokacinda take fitowa tana isowa gurin Ayanah na dauke da wani lallausan showel din lullubawa mai tsananin taushi Wanda idan iskan gurin yayi mata yawa zaa rufa mata, Sakinah kuwa wasu towels din da zaa goge kafafun ne idan an gama a hannunta suma masu Laushi suka qaraso, Zaunawa tayi dukansu suka koma bayanta suka tsaya Sauran masu wankin kafar kuwa suna durqushe gabanta suna jiranta, Farawa sukai ta jingina bayanta jikin lallausan kujeran tana Lumshe idanuwanta, Tray din tea mai Zafin gaske aka kawo mata da snacks din da yanzu ne akai mata su da Zafin su aka kawo aka ajiye gabanta, Zuba mata tea din akai yana wani irin siracin daya sakata zubawa hannun wadda ke zuba mata din idanuwa tana kallan yanda zara zara yatsun hannunta farare tas ke daukan ido take taji wani irin abu ya taso ya danne zuciyarta batasan lokacinda ta dauko ruwan tea din gabaki daya ta watsa musu su hudu dake gabanta ba duka a Fuska tareda wurgi da Kayan gaban nata tana jin Wani irin Zafin zuciya kaman zai kasheta. Cikin tsananin azabar data ratsasu har cikin qwaqwalwa suka sauke kansu qasa batareda sun zabura ba ko magana bare nuna halinda suke ciki sedai idanuwansu sukai jajir suna sake sauke kansu qasa tareda bata hakuri akan abinda ya bata ranta. Ayanah ma qasa suka sake yi da kansu cikeda wani irin sanyin jiki batareda sun motsa ba, Cikin zafi da faree ta bude baki tace ‘Ina buqatar wani shayin ganye’ Miqewa sukai a natse suka bar gurin dan hado mata wani. Suna barin gurin sakinah ce ta zagayo gabanta ta durqusa itada Ayanah suka fara wanke mata kafafun cikin nutsuwa da tattali kaman kafar zinari. Suna cikin yi aka sake kawo mata sha yin ba Imani ta sake zubawa su Ayanah dake gabanta Wanda sakinah dake gefen Ayanah tafi samun ruwan sosai sbd dan karewa Ayanaah datai batareda lurar faree din ba dan haka suma take idanuwansu sukai jajir Wanda ya tabbatarwa da faree wannan Karan kam ta gama da bayin bangarenta babu wadda zaa iya zaba a cikinsu sbd duka konuwarsu a Fuska ne indai ta tashi to tabbas sun haramta har abada. Hakan data ga ta samu ya sakata samun sassauci da sakewa hankalinta ya dan kwanta ta koma yar walwalarta. Su kuwa gabaki dayansu su Ayanah kusan ruwan sun kona fatarsu sosai musamman sakinah wadda har wuyanta saida konuwar ta dan tashi dan haka kwana Ayanah tayi bawa sakinah kulawa sbd ita iya ruwan da suka sameta basu wani Konata ba ja kawai gurin yayi kuma koda gari ya waye jan ya rage kuma a kirjinta ne dan haka baa gani. Haka suka shirya suka taho aikinsu kowa gefen Fuska da
🏠