a bata iya dauka Wanda hakan ya saka bayi da yawa shiga mummunan Hali daga lokacinda aka Zabesu zuwa shimfidar sultan sun San kwanansu ya qare ne a duniya,
Abinda ya kawo sauki da sassaucin kishinta akan hakan shine fara samun ciki da sukai suna haihuwan yaya mata kuma babban me mata duba ya sanar da ita itace zata haifawa sultan YASAR ALMAZ BOYEM namiji.
Wannan bayanin ya saka ta sassautowa ta kyalesu ta duqufa rokon Allah samun ‘da namiji koma yaya yake ko wane iri ne tanaso hakama tana hada wa da aikin bokayen malamanta masu tsananin karfin gaske.
‘yayanta uku mata wainda sune manyan yayan sultan YASAR wato ASLAM,NEESAT da MERYAM,
Sun girma sun zama yan matan da sukafi kowace mace daraja a qasar BOYEM sbd sune arzikin sultan da BOYEM a yanzu tinda sune jinin sultan YASAR ALMAZ na farko a duniya,
MARAKI itace Matar sultan YASAR ALMAZ BOYEM ta biyu wadda itama kyauta kusan daya dana HAILE sedai anfi zuzuta na HAILE cin sbd itace uwargida kuma wadda kaman sultan din yafi Ji da ita duk da bawai ya fada ko nunawa bane kawai macen da sarki yafi kwanciya da itace wadda yafi so kenan a cikin matansa ko imebētis dinsa dan hakan na nufin samun cikakkiyar gamsuwa yake da ita,
MARAKI batai shekarun HAILE ba duk ba wani shekaru ta bata ba hakama ita MARAKI bata taba samun haihuwa ba kwata kwata Shiyasa batada wani power kaman HAILE amma itama kam duniya ce gida take Juyawa a bangarenta wanda yake dauke da bayin hidima sama da ashirin sbd girmansa da daular datake ciki,
A cikin matan sultan da duk wata mace wadda take jinin BOYEM babu wani adon dayake jikinta Wanda ba asalin zinari bane yake motsi a jikinta,
Sarkan wuyansu,
‘yan kunnen dake kunnuwansu Wanda a qalla zaa samu huji sama da uku a kowanne kunnen,
da zoben hujin dogayen hancinsu na gadon asalin BOYEM,
Zobunan hannuwansu da chains na hannu da bangles,
Chains na kafafunsu da zobunan yatsar kafarsu da sarkar adon dogayen gashin kansu gabaki dayansu na zinari ne kawai suke amfani dashi sbd basusan kowane irin abin ado ba Bayan na zinari Wanda kaf idan ba a jini da masarautar BOYEM ba babu irin wannan dukiyar,hatta abinda suke rufe fuskan su me kyau adonsa akwai zinari a cikinsa dan hakanne ake zuba asalin mulki da sarauta a BOYEM.
A cikin imebētin da suka haifawa sultan YASAR yaya basu fi goma ba dan kusan su kansu imebētin Wanda tenya taji bai mata ba a gurin haifawa sultan yaya tsarin hanasu daukan ciki takeyi,
Rashin samun ‘da namiji a masarautar yanzu shine babban qalubale da tashin hankalin da ake ciki Wanda shi kansa sultan rashin samun LEUL BOYEM ne kadai abinda ya taba taba zuciyarsa dake tsaye babu sanyi ko kadan a cikinta,
LEUL BOYEM shine kowane sultan daya mulki BOYEM baya da nutsuwa sai ya Haifa sbd shine ze qarasa kafa tarihin mulkinka,
Rashin haihuwan LEUL BOYEM na nufin sarautar BOYEM Bayan kai zata koma wani dakin Wanda kai Baka cike tarihinka ba kenan,
Babu qasar da bata tsoron yaqi ko tinkarar masarautar BOYEM,
Babu sarki ko sultan din da baya shakkar sultan YASAR BOYEM,
Babu bawa ko wani Mutum da baisan ransa baa bakin komai yake ba a masarautar BOYEM idan yayi kuskure ko laifi,
Babu me mulki ko muqamin wasu qasashen da baya shakka da tsananin tsoron Masarautar BOYEM da sultan dinta YASAR ALMAZ,
Babu matarsa ko imebētinsa da basa sunkuyar da kansu a qasa idan yana kusa
Amma duka wannan babu babban Buri me tsananin gaske ga sultan YASAR irin samun LEUL,
Ya batar da dukiyar da bata lissafuwa ko a gurin masu lissafi gurin sadaka da Malamai gurin adduar Neman haihuwan LEUL Wanda babu abinda bazai iyaba akan ya samu haihuwan Namijin.
jamaar qasar BOYEM da masoyanta a tsaye suke gurin addua da biyan malamai wasu harma da Neman manyan bokayen qasashe duk akan Allah ya bawa sultan YASAR magajinsa wato LEUL BOYEM,
Duk Wanda yasan BOYEM da Wanda yake cikinta koda bawa ne kuwa yasan da wannan tsantsan burin me girma da karfi na sultan YASAR ALMAZ BOYEM,
Wannan shine babban dalilin daya saka ake zabar masa imebēti daban daban yana kwanciya dasu babu kakkautawa sbd Neman haihuwan LEUL BOYEM wato magaji zakin BOYEM.
#MAMUH
#BOYEM
#BEST LOVE
#BEST ROYALTY
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee
25
Ayanah tana cikin masu kulawa da yanayi na laulayin faree wato imebētin sultan wadda kwata kwata batai farin ciki da samun cikinba sbd yanda taso taci gaba da samun damar datafi mata komai duniya ta zuwa shimfidar namijin dayafi kowane namiji daraja a qasar BOYEM dama zagayenta,
A ranta tariga tasan kila itama macen zata Haifa tinda shine baya haihuwan namiji dan haka Sam bata wani doki da cikin gashi matiqar mace na laulayi baa kara kaita tirakarsa sbd baya iya mu’amalantar mace me laulayi sosai dan haka faree sai an yayeta sedai ta jira haihuwa idan tanada rabo zai sake buqatan kwanciya da ita,
Wannan quncin d