da Zuhrah din,
Suna tsananin so da kaunar iyayensu amma yanda suke tsananin son junansu da irin gwagwarmayan da suka shiga ya saka suke jin mummunan ciwon rashin junansu fiyeda Zafin rashin iyayensu,
A nata zuciyarma gabaki dayansu a cikin jininta yake jinsu tamkar itace ta haifesu din da gaske sbd uwar data zama garesu musamman Nurat datake ambatarta da AMMAH kafin rasuwarta,
Ciwon rashin ‘yan uwanta da sune rayuwanta bazai taba barin zuciya da ruhinta ba har abada,da wannan ciwon zata mutu idan ma ba ciwon rashinsu bane zai zama ajalinta sbd a yanda takeji babu wahala ko azabar da bazata iya dauka ba amma ciwon rashinsu abu ne da zuciya da gangar jikinta bazai taba dauka ba musamman irin rasuwar da Nurat tayi.
Rayuwanta a Masarautar BOYEM bata taba sakewa ko sabawa da kowa ba Bayan sakinah wadda take tsananin kulawa da ita idan suna daki sbd tsoron bugawan zuciyarta datake riqe da abubuwa da dama ta kasa saki ta kuma kasa fada Bare nunawa,
Cin zuciyarta damuwa da quncin sukeyi Wanda suke bawa zuciyarta illa ahankali batareda saninta ba dan haka sakinah batada damuwa itama a nata rayuwar yanzu Bayan ta Ayanah din,
Itama sakinah ko a mafarki ma bata taba saka kanta a lissafin da wasu bayin keyi na shakka ko tsoro sbd ko zasuyi shekaru dari a BOYEM babu ranar ma da ko bawa irin su zai iya cewa yana shaawansu bare me qasar da kansa duk da bai taba zaben macen dazai kwanta da ita ba da kansa duka wannan aikin shugabar jakadan qasar BOYEM ce gabaki dayanta wadda take Zaune cikin masarautar itama da nata bayin sbd babu me matsayi dake Masarautar BOYEM fa baya cikin nasa jin dadin da daula me girma tareda tarin dukiya.
Meleketen’ya wadda ake kira da Ten’ya wato jakadiya da yarensu itama matsayi ne da ake gadonsa sbd tin kakanni da shekarun da suka gabata jini daya ne suma suke riqe wannan matsayin dan haka shima matsayi ne me girma da iko dan kuwa duka bayin dake cikin asalin masarautar BOYEM a karkashin iko da umarninta suke yawo da aiki,
Hakama tenya din itace me kulawa da dukkanin abinda ya shafi sirri da babbar buqatun matan sultan da ‘yayansa wainda suke jininsa,
SULTAN YASAR ALMAZ BOYEM shine Sarkin Boyem da ikonsa yake zagaye da kusan fiyeda Rabin daulolin dake duniyarsu,
SULTAN YASAR sarki ne da mulkinsa yakeda tsananin zafi da karfi tareda tsananin doka da ikon daya saka ko dabbar masarautar shakkar laifi takeyi sbd hukuncin dayane fa Mutum ga dabba wato cire kai kawai dan haka a cikin tarihi yana cikin sarakuna masu Zafin gaske da akai a BOYEM,
Sultan YASAR yana daya daga cikin sarakunan jinin BOYEM da su keda abubuwa da dama da suka Zarrah na kowa a tarihi dan hakanne shima yayi Wani irin sunan da sunan BOYEM yake sake gauraye duniya,
Sultan YASAR yana tarin dukiyar data qara Habbaka dukiyar Masarauta duk da asalin BOYEM sunada da wasu irin arziki wadda basa talauci Allah ya gama bude musu kofofin arzikinsa tin asalinsu babu talaka ko daya hakama su kansu basa sanin tarin arzikinsu sbd yawansa da yaduwarsa,
Sultan YASAR yana daya daga cikin sarakunan BOYEM da sukai karatun ilimin boko sosai da Larabci sbd asalinsu balarabiya ce Matar farko ta BOYEM dan haka suke tamkar ruwa biyu amma sunfi maida hankali akan karatu da samun ilimi da yarensu na Amharic da arziv dan haka qalilan ne a cikinsu suke karatun ilimin boko da larabci sosai dan haka sultan YASAR yana daya daga cikin masu bokon hakama yana cikin masu zafi,
Bayan duka wainnan sultan YASAR ya sakance cikin wainda Allah bai azurta da samun namiji ko daya ba a tarihin wainda suka mulki kujeran BOYEM,
‘Yayansa duka mata ne suma kusan duka imebētinsa ne suke haifar masa su,
Matansa biyu rak suma aure ne da kaman Alkawari da ake wa kowane Sarkin daya hau mulkin dan kuwa su biyun jinin BOYEM ne suma auren gida ne duk da bama qasa daya suke Zaune ba sai da akai auren aka kawo masa su a rana daya a lokaci daya,
Uwargidan itace HAILE wadda duniya take fadar kyauta da kaf BOYEM ba kamarta,
Jinin BOYEM ne yake yawo a jikinta itama,
A qasar Morocco take rayuwa itada iyayenta a cikin wata irin daula da ikon da mulkin da suke zubawa kafin auren daya kafa tarihi ya dawo da ita cikin BOYEM qasar da kowa ke kwadayi da maitar son zuwa yayi rayuwa a ciki dan haka ita a duniyar babu me saa irin tata samun kanta a matsayin Matar sultan YASAR ALMAZ BOYEM kuma uwargida dan hakanne duniya ke kiranta da HAILE(me power) kenan hakama kaf duniya Bayan bayinta babu Wanda yake da saa ko matsayi ko ikon ganin asalin fuskanta da ake cewa tafi kowace mace kyau sai shi sultan din da kansa Wanda take tsananin so fiyeda komai na duniya da ita kanta,
Kishinsa take kaman zata kashe kanta sbd son da take masa yayi yawan daya fita hankali dan hakanne ta ringa haihuwa bata jira sbd son ta haifar masa namiji amma Allah bai bata ba tana Ji tana gani aka ringa wanke masa imebēti masu kyau da daukan hankali Ana kai masa yana kwana dasu,
Da farko duk imebētin daya kwana da ita bada umarnin a kawar dasu takeyi sbd zuciyart