anah aikin gyara toilet tayi tareda wanke Kayan wankin da ime din tayi amfani dasu ta wanke su sosai da hannuwanta batareda ta saka washing machine ba duk da an koya musu komai da yanda zasuyi amfani da koman a gurin karatunsu,
Tana gamawa sake gyara toilet tayi ta hada mata ruwan wanka masu dumi sosai da Kayan qamshi masu dadi na wanka Wanda duka shima an koya musu dan kusan babu abinda baa koyar musu ba komai kankantarsa,
Tana gamawa ta koma bakin toilet din ta tsaya kanta a qasa tana jiran farkawanta,
Tsayuwan mintina talatin tayi kafin ta fito daga cikin makeken lafiyayyan gadonta mai rumfar dataji ado da dukiya.
Tana qarasowa ko amsa gaisuwan da Ayanah din tai mata bataiba ta zare rigar baccinta ta Sama ta Bari a gurin tareda shigewa toilet din daya gama tsaruwa,
Sunkuyawa qasa Ayanaah tayi a natse ta dauke rigar data zare din tana barin gurin ta kai rigar inda Kayan wanki suke ta dawo ta isa inda towels suke sama da guda ashirin ta dauko guda uku harda na goge kai suna wani qamshi me sanyi ta dawo bakin kofar ta tsaya da towels din.
Tsayi me tsanani tayi a gurin batareda ta motsa ba duk kuwa azabar datake ji ta tsayin hakan take a tsaye kanta a qasa har tsawon lokacin da batasan Yaushe ne ba tukuna ime din ta bude kofar toilet din Wanda Ayanaah tayi saurin miqa mata towel din farko ta amsa ta daura a jikinta kafin ta sake bata wani t rufo jikinta kafin na ukun ta Dora akai dan goge kanta.
Tana wucewa gaban mirror Ayanah ta fada toilet din ta sake gyaresa tsaf ta qamar da ruwan toilet din tsaf duk kaman ba yanzu aka fito wanka cikinsa ba.
Tana gamawa ta fito tana gyara dakin da gadon dakin sakina da wata baiwar daya suka shigo suna busar mata da gashinta tareda gyarasa tana zaune tana kallan kanta a madubi.
Tsawon lokaci suka dauka suna hidimarta kafin suk kammala ta fito cin abincin da Sauran su suka dafa mata sama da Kala daya ta zauna suka zagayeta kowannesu da abinda yake mata.
Har dare suna tsaye kan kafafunsu basu zauna ba Bayan sallah babu abinda sukeyi sai hidimarta wadda bata qarewa.
Sai tsakar dare sosai suka koma daki Bayan tayi bacci,
A tsananin gajiye suke dan haka komai babu Wanda suka iya yi bacci suka buge dashi mai karfin gaske,
Asubar fari aka buga qararrawa tashi yake suka fito sukai ayyukan bangarensu na bayi har lokacin sallahn asuba yayi sukai sallah sukai wanka tareda shirya wa suka fice ayyukansu na iyayen gidansu.
Kaman yanda sukai jiya yauma haka suka wuni suna aikin wahala da bauta babu sukuni abincin da sukeci ma a tsaye suke cinsa ba yancin zama.
****farkon wannan wahalar da suka samu kansu a cikinta na bautar da babu Hutu ko kadan dan Baka isa kayi bacci ba sai Wanda kake bauta wa yayi nisa sosai a nasa baccin,
Farko farko kafin su Saba sosai suke jin jiki amma ahankali ahankali suka saba da wahalar wadda ta zama jiki har basa jin komai,
Kaman computers haka suke da aiki ba mantawa ba kuskure a natse,
Watanni hudu kenan yanzu a zamansu cikakkun bayin boyem da suka Riga suka saba da tsantsan na masarautar da dokokinta ba kuskure ko daya,
Idan aka hada da watannin da sukai a daular bayi kusan wata bakwai kenan a BOYEM Wanda yayi daidai da shekara guda harda wata daya rabon su iyayensu,
Tsawon watannin nan babu ranar da Ayanaah bata baqin ciki da quncin rashin Zuhrah,
A kowane motsi da numfashinta babu abinda ya rage na rayuwar baqin ciki da quncin datai tareda rashin yan uwanta a tareda da ita,
Sakinah ce kadai zata iya shedar da qunci ne zallansa a daddabe da zuciyar Ayanah amma a bayyane ta rungumi kaddarar datake cikinta.
Ime dinsu da suke bautawa kwatsam Allah ya azurtata da samun cikin daya saka aka yayeta daga zuwa shimfidar sarki sai kuma idan ta haihu idan tanada rabon ya sake kwanciya da ita kenan.
Yayeta da akai ya saka dukkanin bayi shiga fargaba da tsoron sabbin imebētin da zaa zabar wa sarki Wanda a yanzu baya qasar kafin dawowansa zaa kuma zabar sabbin imebētin da zai huta dasu dakyau idan ya dawo.
#MAMUH
#ROYALTY
#AYANAH GHAZ
#NUAB BOYEM
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_
Mamuhgee
24
Duk damuwa da fargaba da duka kyawawan bayin dake BOYEM ke dan shiga da tsoron sabbin imebētin da zaa zaba Ayanah bata taba ma San da hakan ba sbd bama huriminsu ne na shiga ba dan kuwa tasan a cikin sama da mata bayi sama da dubu dake bauta a masarautar bama sa cikin wainda zaa iya gani bare sani tinda suna bangaren imebētis din sarki suna bauta basa can bangaren matansa biyu da bayansu bai taba qarawa ba.
Dan haka bautarta kawai takeyi babu tinani kowane iri a zuciya da rayuwarta Bayan na ‘yar uwarta datake azabtuwa da rashinta a kowane daqiqa,
Tinda ta rabu da Zuhrah bata taba jin sassauci na rashinta ba ko kadan a zuciyarta Wanda bama ita kadaiba kowace daqiqa tana wuce mata ne da tsananin ciwo da quncin rashin Nurat da Abaas