NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 48 of 146

rin kuka Mara sauti zuciyarta na mutuwa a matakin karshe na shikenan. Ayanaah ma wani irin kuka takeyi mata sautin tana kasa dauke idanuwanta daga Zuhrah wadda itama ita take kalla sakinah ma hawayen takeyi tana sunkuyar da kanta qasa. Layi na zuwa kansu sunansu AYANAAH GHAZ da ZUHRAH GHAZ Ana tambayan alaqarsu Ayanah ta dago jajayen idanuwanta da suka rine gabaki daya ta zubawa Zuhrah wadda ta goge fuskanta tas ta bude baki tace ‘BABU ALAQAR JINI sunan ne iri daya’ Tana fadar haka take aka buga stamp a sunayensu tareda wata irin stamp ta daban wadda take bada tabbacin ko a toilet daya tsautsayi ya hadasu a kashe dayansu abar daya sbd kawar da zargi hakama duk ranar da dayansu ya kalli daya shima hukuncin daya ne. Miqa musu Id cards nasu akai tareda jansu zuwa ciki Wanda kowannensu babu abinda yake aiki a gangar jikinsu Bayan kafafunsu dake jansu kaman marasa lakka a jiki. Hawaye ne masu tsananin zafi suka gangarowa Ayanah tanajin kusan komai nata na Dena aiki tanason dagowa tayiwa Zuhrah kallan karshe amma damar ta qare hakama itama Zuhrah Ayanah takeson kallan ba damar ta qare sedai hawaye suka sauko mata ta rufe idanuwanta tana bin inda ake tafiya dasu hanya daban da wadda aka tura Ayanah da sakina. Duk Taku daya da Ayanah ke yi jin takeyi tana rabuwa da ruhinta sbd a yanzu kam takai matakin karshe na rasa komai nata batada Sauran hasken da idanuwanta zasu gani ko miskala zarratan, Rawa kafafunta keyi zuciyarta na kasa wa sbd bazata iya rabuwa da Zuhrah ba koda hakan zai rabata da rayuwanta ta yadda dan haka ta dakata ahankali daga tafiyan datake, Dagowa tayi ahankali zata juya ta kalli Zuhrah koda hakan zaiyi sanadin rayuwanta, Da sauri sakinah dake bayanta ta riqeta cikin nutsuwan da bazata bari a gane su ba ta hanata Juyawa sbd bazata iya barinta Juyawa ta rasa rayuwanta kokari da sadaukarwar Zuhrah ya tashi a banza, Wasu hawayen ne masu tsananin zafi suka cigaba da gangarowa Zuhrah wadda itama bata juyoba tana Jin ciwo da radadin halinda Ayanaah take a jikinta, Sakinah ce ta iya waiwayowa a hankali ta zubawa Bayan Zuhrah dake tafiya jikinta na bayyanarda gap take da samun bugawan zuciya, Tausayinta ne ya rufe zuciyar sakinar sbd ita zata rayu bateda duk Wanda rayuwarta ta taba sani ba dan gwara Ayanaah din ita tana tareda ita, Koma menene tasan wannan ma wata sabuwar jarabawar ce Allah zaici gaba da jarabtarsu da ita, Ahankali ahankali aka gama rabasu zuwa bangarori da dama Wanda sai da aka kuma daukansu cikin wasu motocin aka isa dasu can ciki inda duniyar boyem take, Tsari da yanayin gini da aljannar duniyar dake cikin Masarautar boyem ya wuce tinanin duk wani labarin daular duniya da ake bada labari da tarihin Masarautu, Tamkar suna tafiya baa cikin duniyar ba haka suke jin kansu sbd koina da ake giftawa dasu madubai ne suke ganin kansu a ciki suna daukan idanuwansu dan haka tsoro duka ya cika su suka sake saukar da kawunansu a qasa suna kama jikinsu dake rawa sbd tsoro suna tattaro nutsuwarsu sbd itace gaba a komai na aikinsu. Kai tsaye sabon bangaren bayin dake cikin masarautar aka kaisu aka basu daki shima kamar wancan da suka Baro daular bayi sedai wannan Mutum uku uku ne a daki. Duniyar da aka jefata daban data Zuhrah sbd tsakanin bangare da bangare akwai yar tazara da kuma tsaro sosai dan haka ita kai tsaye ita bangaren imebētiś aka kaita Wanda yake duniya ce guda mai zaman kanta wadda take dauke da part part sun kai hamsin duka na imebētiś ne maana mistresses na sarki, Duk macen da sarki ya kwana da ita indai ta samu ciki anan zaa bata flat dinta mai shegen kyau da wata irin daula a cikinsa tareda bayi sama da goma wainda sun zama nata zatai rainon cikinta anan ta haihu anan ta reni jini boyem cikin jin dadi da daular da hankali ma bazai daukaba kuma anan zataci gaba da rayuwanta da bayinta cikin jin dadi da yanci har sai jinin BOYEM data haifa ya girma ya kai shekaru goma sha biyar shikenan zaa ware masa nasa muhallin daya zarce tinani acan cikin asalin ginin da sultan yake a zuba masa bayin ya koma can sedai Yazo gaida mahaifiyarsa kokuma ita taje gurinsa. Duk macen da sarki ya kwana da ita kuma bata samu ciki ba bangarensu daban bautar suke komawa sedai Ana sauya musu guri a cire su cikin asalin bayi, To Ayanah a cikin bayin dake kulawa da sabuwar imebētin sultan aka kaita itada sakina ita kuma Zuhrah a can asalin bangaren uwargidan sultan aka kaita dan haka sukaiwa juna Nisan da babu ranar cike gurbin. Tinda suka iso dakinsu Neman somewa Ayanaah keyi sbd halinda tashiga na rabuwa da Zuhrah daqyar sakina ke kokarin bata taimakon daya hanata somewan sedai har tsakar dare tana fama da ita kafin Allah ya kawo mata dangana ta sakawa kanta karfin halin hakura. Washe gari tinda asubar fari suka shirya cikin uniform dinsu tsaf suka fito zuwa aikinsu, Kai tsaye bangaren sabuwar imebetin suka isa su shida ne dan haka suna isa suka bude suka shiga kai tsaye kowannensu ya fara hidimarta tin kafin ma ta tashi. Ay
🏠