NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 46 of 146

da dagowa ta kalli Ayanah din zata bude baki tayi magana Ayanah ta girgiza mata kai tana cewa ‘Ba komai ya wuce kije ki shirya din’ Miqewa Zuhrah tayi ta fada toilet duk ta zama kalar tausayi. Tana fitowa sakinah ma ta shiga suka gama shiryawa tsaf suka fito su ukun suka wuce zuwa hall din karatun. Wannan sabanin da suka samu ya sake ruguza Ayanah ta qarasa rasa walwala da kuzarinta sbd damuwan datai mata yawan gaske a cikin rai dan haka ta sake zama tamkar qanqara sbd sanyi da rashin magana sosai, Komai Zuhrah takeso shi kawai take mata bata iya hayaniya ko magana koyaushe indai suna daki Zuhrah na jikinta kwance zata rungumeta tana mata addua da shafata dan bata nutsuwa sbd tsoro da firgici na Neman taba kwakwalwan Zuhrah din tsoro mai tsanani kawai take samun kanta sbd ganin kaman suna shiga palace din sun rasa kansu kenan har abada kila ma harda junansu, Tsananin tsoron rabuwa da Ayanah take ji fiyeda komai ma daya faru a baya, Idan har zata rasa Ayanah so take Allah ya dauki ranta ta mutu, Koba komai mutuwar ma take tsananin so sbd rashin nutsuwan datake ji a zuciyarta. Ana gobe ne ranar tafiyarsu zuwa cikin palace a zaune suka kwana rungume da juna Sai a Daren Ayanah ta bude baki tayi doguwar magana da Zuhrah din tareda tinatar da ita babu abinda zasu iya yi a duniya yanzu su samu damar haduwa da Abaas wata rana irin su jajirce su rayu har zuwa lokacinda Allah zai sake kawo musu wani sauyin rayuwar, Babu abinda zasu sakawa kowane dan GHAZ dashi Bayan su rayu su kai labari dan haka matiqar tanason Allah ya kawo mata ranar haduwa da Abaas ko jin labarinsa to tabbas zata jajirce ta rayu zuwa lokacinda Allah zai dauki ranta. Zuhrah da Sai a lokacin ta fahimci karfin halin da Ayanah takeyi jin tayi jikinta ya sake mutuwa dan kuwa kaman ita bazata iya ba takeji amma ko bazata iya ba zatai kokarin bawa Ayanah karfin gwiwan rayuwa sbd itace kadai a raye wadda take saka zuciyar Ayanah bugawa daidai, Ita dai kam bazata iyaba da gasken gaske duniyar take son Allah ya dauketa daga cikinta ta tafi ta huta amma kuma idan babu ta Ayanah zata zama mara amfani a duniya sbd bazata taba moruwa ba. Koda asuba tayi suna tsaye sbd tin kafin asuba aka tadasu aka tarasu a babban guri, Anan aka sake rarraba musu uniform da abubuwan amfani a jaka aka bawa kowa nasa, Sallar asuba kawai suka koma daki sukai aka sake buga qararrawa kira suka ringa fitowa kowa dauke da jakarsa fes dasu, Jikin Ayanah dana Zuhrah a sanyaye sbd Sai yanzu ne Ayanah take sake fahimtar tsoron Zuhrah na zaa iya rabasu a gurin aiki ko gurin kwana dan haka itama jikinta ya tsananta sanyi. Motoci ne masu tsayi bus bus aka zuba su a ciki aka fice dasu zuwa cikin palace din. A mota ma hannuwansu na riqe dana juna qamqam sakina na gefensu, Ficewa akai dasu daga babbar gate din daular bayi aka miqa zuwa mahaukacin gate din shiga BOYEM palace wadda securities dinta suka mugun baci sbd tsananin tsaro, Shi Karan Kansa gate din shiga Masarauta kashe idanuwansu sukaga kaman yana yi sbd kyansa dayake tamkar na zinari, Scannin komai nasu dasu kansu akai daya bayan wuni guda Ana abu daya kafin Ana gap da kammala wa aka zo kan wasu su biyu wainda sunan mahaifinsu Yazo irin daya komai da komai. Dakatar dasu akai tareda zagaye su da wasu irin securities da suka sakasu saurin durqusawa kasa kansu a qasa jikinsu na wata irin rawa cikeda tsoron dake Neman rabasu da bugawan zuciyarsu. Chief security ne Yazo gurin da Kansa ya kallesu dakyau kafin ya kalli sunayen nasu Akan wadda tafi girma ya tsaida idanuwansa ya bude baki yace ‘Meye alaqarku da sunanku Yazo daya?? Wani yawu babbar ta Hadiye kafin cikin sanyi kanta na qasa tace ‘Alaqar jini ce…… Ko rufe baki bata gama yi ba akai sama da ita tamkar ba Mutum ba aka jefa cikin wata motar da batai Kama da mota ba sbd tsarinta dayafi Kama da motar yaqi. Wani ihu taje yi tana kokarin riqo qanwarta a lokacinda ake janta tana jin kaman ranta zai fita amma ko imanin kallanta babu take aka buga kanta da karfen motar ta zube a cikin motar jini na fitowa gefen fuskanta kadan. Qanwar tata ma Wani irin kuka me karfin gaske takeyi tana ambatar sunan yar uwarta kaman ranta zai bar jikinta take aka sumar da ita da wata shocker a gurin akace a dauketa a maidata daular bayi. Ganin hakan ya saka wainda ke bayinsu suma su uku fara rawar jiki sbd suma yan uwane uwa daya uba daya. Suma Ana duba sunayen su take aka rarrabu su ukun aka soke lasisin biyu aka bar daya Sauran zaa rabasu zuwa dauloli daban daban ga Wanda yayi rashin saa kuma ciyar da dabbobi namansu kawai akeyi sbd tin farkon shigowa qasar baa karban bayin da suke da alaqa da juna, Doka ce da kaida me tsananin karfin gaske baa barin masu alaqa a masarautar matsayin bayi duk lokacinda aka Kama masu alaqa kai tsaye hukuncinsu a kashe daya abar daya tin asalin asali wannan dollar take sbd a shekarun baya sosai da suka gabata akwai bayi uku da suke uwa daya uba daya da suka kulla shirin guduw
🏠