NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 45 of 146

hawaye tace, ‘Ayanah kin samu sabuwar rayuwar data mantar dake abaas na can wata duniyar yana gararin da zai iya rasa rayuwarsa koma ya rasa din? Ayanah kin manta komai ne kin zubar da komai? Sakinah data fito wanka ne ta iso gurin Zuhrah din da sauri tana riqe hannunta cikin tausasawa tace ‘Kar kice haka Zuhrah’ Fizge hannu Zuhrah tayi tana Miqewa tsaye idanuwanta na gangaro da hawaye tace iso gaban Ayanah din wadda bata iya juyowa ba ta kalleta cikin wani irin radadin zuciya tace ‘Maye a cikin wannan sabuwar rayuwar daya mantar dake yan uwanki da halinda muka shiga? Daman damuwarki Akan yan uwanki na dan lokaci ne? Daman akwai jin dadin da zai taho miki ki manta dan uwanki dake can duniya cikin garari da qunci?…. Riqota da karfi sakina tayi tana cewa ‘Ya isa haka Zuhrah,kinfi kowa sanin Ayanah ba haka take ba karki Bari Batan tinani yakaiki ga aikin dana sani’ Sake fizge wa tayi tana kallan Ayanah wadda ta dago ta zubawa Zuhrah idanuwanta da sukai wani irin jajir tsananin qunci da radadi me ciwon gaske yana cikesu amma bazata iya cewa komaiba Bayan kallan zuhran dake fada mata maganganu masu ciwo da radadin gaske. Zuhran ma cikin tsananin jin ciwo da radadin ganin idanuwan Ayanah din taci gaba da fada mata maganganun da itama suke sosa zuciyarta tace ‘Ayanah su Amma sai sunyi Allah wadai dake da zasu dawo duniya su ga yanda kika zabi jin dadin duniya kika manta amanar da suka bar miki a lokaci dan qanqani, Abaas zaiyi baqin cikin zabar sonki fiyeda Sauran yan uwansu idan yaga yanda kika zabi wata rayuwar akan tinaninsa, Ayanah inama ace Nurat ce aka bar mana dan ita bazata taba manta yan uwanta ba koda bata cikin hankalinta…..’ Wasu irin hawaye ne masu tsananin dumi suka gangaro daga cikin idanuwan Ayanah a karo na farko Bayan tsawon lokaci mai nisa, Silalewa qasa take kokarin yi sakina tayi saurin riqeta tana fasa kukan kalaman Zuhrah itama sbd tsananin tausayin Ayanah wadda har lokacin ta kasa furta komai sbd rabata da ranta ne kawai kalaman Zuhrah basuyi ba amma sun gama ratsa zuciyarta sun yayyankata, Kalaman sun qarasa karya duk wani kuzarin daya rage mata na rayuwa, Kalaman sun yanka mata sabon Raunin da shima har abada bazai warke ba……. Wasu irin hawayene ke gudu sosai a fuskanta ta kasa iya tsayuwa duk riqon da sakina tayi mata silalewa qasa tayi tana Dora tafin hannuwanta biyu a fuskanta ta rufe wani irin kuka mai qaramin sautin daya saka Zuhrah yin tsit yana zuwar mata jikinta na wata irin rawa sosai wadda ta saka sakina zubewa qasa tana rungumeta da sauri, Zuhrah ma sautin kukan ya ringa sosa zuciyarta ta durqushe itama a gurin tana fasa kuka sosai zuciyarta na dana sanin saka Ayanah kuka irin haka. Shiru dakin ya dauka babu sautin dayake tashi saina kukansu mara sauti sosai amma babu dadin Ji ko kadan. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 22 *JEWELRY JUNCTION* 08039440312 Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma, Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne?? To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan, Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana, ✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌 ✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌 ✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌 ✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍 🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah. WhatsApp 08039440312 Tiktok :@sokoto jewelry seller Instagram: jewelryjunction23 ********* Sun jima a wannan yanayin kafin Ayanah ta taqaita kukanta data jima bata samu yi ba sai yau ta miqe tareda sake komawa toilet. Acan ma wani irin sabon kuka ta durqushe tana yi Wanda dukkaninsu suna jiyota daga bandakin sai data jima tayi ta gama ta wanke fuskanta da ruwa ta fito ta goge fuskanta ta shirya cikin uniform dinta tana jin kirjinta da zuciyarta na Wani irin ciwo amma batada abin yi musu kawai qarasa shirinta tayi ta koma gefe ta zauna tareda kallan Zuhrah dake kuka har lokacin ta taso ta rankwafo kawai ta sumbaci tsakiyar kanta da gefen fuskanta ta bude baki da tsananin sanyin murya ta bude baki tace ‘Ya isa haka ki wanke Fuska ki shirya mu fice’ Ajiyan zuciya Zuhrah ta sake tare
🏠