NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 44 of 146

da iya aikin koina da yanda zasu iya fuskantar rayuwarsu idan sun tsayu a gaban duk Wanda yake jinin BOYEM. Rayuwar bayin BOYEM hatta inda zasu iya dagowa su kalla a qayyade yake hakama yanda zaka iya bude baki ko fidda Numfashi me sauti a gaban jinin BOYEM Akan kaida da doka yake hatta dukkanin gangar jikin bawa da abinda yake gangar jikinsa Akan kaida da tsari tareda amarni yake. Wasu irin kaidoji da dokoki tareda tsari masu tsauri da karfi aka fara dorasu dan kuwa ko tafiyarka a tsari take aka dorasu, Lokutansu na bacci da fitowa fara aiki tareda wata irin tsaftar gaske duka Akan tsari suke da yanda ma zaka dago kai Ka iya kallan inda kake sbd kaida ne koyaushe Kanka ya zama a qasa, Duk jin dadi da nutsuwar da suka samu a BOYEM din tsari da dokokin tini suka daga hankalinsu tareda shiga tsoro me tsanani sbd laifuka da kurakuran da zasu iya rabaka da ranka a masarautar yawa ne dasu sbd mafi yawan hukuncin kasar cire kai ne kawai kokuma ciyar da dabbobi namanka dan haka babu Wanda yake yadda komai tsananin tsautsayi yayi laifi dan tsira da rayuwa, Mataki mataki ne na bayin masarautar sai Wanda yakeda matakin saar karshe ta rayuwa yake samun damar yin aiki a inda asalin jinin BOYEMs din suke. ***Ayanah da Zuhrah harma da sakina basuda Sauran kowane zabi Bayan mayarda hankali suna daukan karatun da ake musu tareda samun qarin nutsuwa sbd a yanzu damuwa da kuncinsu a natse ma yake cinsu, Sun sauya sosai kawai dai quncin dake kwance a zuciyarsu ne yake hanasu yin jiki ko mulmulewa suna nan basu wani qara kiban komai ba kawai dai yunwa tabar jikinsu. Kullum da safe a kaida da doka zasuyi wanka su shirya a cikin uniform dinsu tsaf tsaf su isa gurin karban abinci abi Layi su karba abinci su ci kafin masu wucewa aiki su wuce su kuma su isa inda ake karantar dasu acan suke wuni sai yamma suke dawowa. Sakinah data Saba da bauta zuwa yanzu ta sake ta karbi sabuwar rayuwarta da babu matsi hannu bibbiyu tareda samun nutsuwa da gode wa Allah daya rayar da ita ta fito daga hannun kusra batareda rasa komai nata ba dan haka a yanzu batada doguwar damuwa saita Ayanah wadda koda minti daya quncin dayake zuciyarta bai taba fita ba zuciyarta a qulle take tamau da wani irin qunci da damuwan da har abada kila bazasu fita ba dan rayuwarta ta Riga tayi rushewan da bazata taba gyaruwa ba, Tana komai Akan lokaci tareda komai da ake Dorasu akai a natse babu hayaniya babu rawan jiki komai nata yayi sanyi ya koma zallan nutsuwa bata sake bude baki ta Ambaci Abaas ko Nurat ba komai ta tattara ta ajiye sa a cikin zuciyarta yana cin lafiyanta da kwakwalwanta a hankali ahankali batareda sanin kowannensu ba, Sakinah datafi su wayo da shekaru sosai ta fahimci Ayanah ta kafe komai a tsakiyar zuciyarta Wanda illar da hakan zai mata tasan mai yawa ce sbd ta riqe baqin cikin da quncin gam a cikin rai ta kasa fitarwa amma ganin bata nuna ba tana komai na rayuwarta a natse ya saka bata ce komaiba sai itama ta sake sbd tinanin insha Allah lokaci na tafiya quncin kila zai ringa wankewa yana ficewa daga ranta. Zuhrah da farko mamakin Ayanah ta ringa yi ta yanda ta Dena maganar su Abaas kwata kwata da iyayensu ta nutsu duk da tayi sanyi sosai kaman ba ita dinba ko dagowan magana bata iya yi yanzu Wani irin miskilanci da son kadaici ya aureta, Zuwa yanzu kusan sunsan koina a bangaren nasu na bayi da yawan bayin da suka taho tare sun sake sun karbi wannan rayuwar dari bisa Dari farin cikinsu sukeyi da walwala tareda jin dadi, Suna Sauran sati daya a kwashe su zuwa cikin asalin masarautar subar daular bayin hankalin Zuhrah ya tashi sbd tsananin tsoro da fargaban shiga BOYEM palace take dan abu daya ne akace a cikin biyun matiqar Kafarka ta shiga gate din masarautar aka rufe to tabbas gawarka ce kadai idan lokaci yayi zata fito bauta ce zakai har tsawon ranka sai kuma idan Ka zamo daya daga cikin bayin da zaa riqa kwanciya dasu Ka zama abar kwanciya kenan a duk lokacinda aka ga dama har tsufanka shima kokuma idan an gama jin buqatar kusantar taka zaka koma tamkar fankon da baida Sauran amfani a duniya shikenan. Wannan tinanin ne yake saka zuciyar Zuhrah shiga mafi girman tsoro da tashin hankali harma firgita takeyi a cikin baccinta duk tabi ta firgice ta rasa nutsuwarta ga yawan mafarkin Abaas da Nurat datake suna zuwar mata cikin yanayi na tsananin tausayi. Yanayin ya saka ta fara kasa maida hankali Akan karatun da ake musu ta fara zama yanayi na kaman tana Neman fita hayyacinta, Yau ma cikin damuwa me tsananin yawa take zaune ta kasa saka Kayanta daya fito wanka ta qurawa guri daya ido hannuwanta qanqame da uniform dinta kanta bai ma San tinanin dayake ba. Ayanah ce ta fito wankan daure da abin wankanta me tsayi da kauri fatar jikinta ta samu lafiya sosai haskensu kusan duka ya kusa dawowa, Cikin sanyinta da rashin hayaniya ta dauko uniform dinta zata saka Zuhrah daya zuba mata idanuwanta da sukai jajir zuciyarta na Wani irin zafi da quncin dayake lullabe dasu ta bude baki idanuwanta na cikowa da
🏠