zuciyarta ta mutu gangar jikinta ne kawai ranta rage,
Zuhrah ma dawowa tayi gefen Ayanah din ta zauna ahankali tana kwantar da kanta a gefen kafadar Ayanah din tareda saka hannunta cikin nata suka sarkafe ahankali bata ce komaiba ta rufe ido hawaye masu dumi suka gangaro mata suna sauka a kan hannuwansu dake sarqe.
Bude idanuwa Ayanah tayi ahankali ta kalli hawayen yanda suke gangara a fatar Bayan hannunta ta Lumshe ido ta bude tareda Dora hannunta daya Akan fuskan zuhrah ta Shafa ahankali tareda juyowa kadan tayi sumbaci tsakiyar kanta da babu dankwali sun zama tamkar mahaukata ta sauke ajiyan zuciya tareda bude baki ahankali tace
‘Zuhrah hįyįwetēni bemulu,ye’īne aleem zuhrah(Zuhrah my whole life, zuhrah my world)
Allah ya hanani dandana rabuwa dake,
Ina rokon Allah ya dauki rayuwata kafin kaddarar da zata rabani dake tazo..’
Tsananta gudu hawayen Zuhrah sukai ta sake shigewa jikin Ayanah din tana fidda kuka Mara sauti tareda girgiza kai tana cewa
‘Ayanah idan babu ke wlh zan kashe kaina na biku duka bazan iya rayuwa a duniya ni kadai babu ku dukanku ba,
Na Roki Allah kaman yanda yabarmu muka rayu a tare zuwa yanzu ya raya mu a tare mu mutu tare mubar duniyar tare.’
Girgiza Kai Ayanah tayi idanuwanta na qara yin jajir tace
‘Abaas…’ sai ta kasa cigaba da magana ta rufe idanuwanta tareda sauke Numfashi me zafi.
Sun jima a hakan tsawon lokaci kafin sakinah da itama tana rabe a gefe ta taimaka musu suka miqe kafin suyi wani motsi aka fara buga wata qararrawa me karfi ta kiran kowa da anfada musu maanarta tin kafin a basu daki dan haka a sanyaye babu me iya miqewa tsaye daidai suka fito.
Kusan su Dari harda qari ne bayi mata sababbi da aka kawo yau din dan haka iya su dinne a bangaren yanzu sbd tsofin bayin basa nan duka suna gurin aiki dan haka suna fitowa a wani babban guri me fadin gaske dayake shafe da tiles fari qal da hanyar wucewan ruwa da famfuna babu adadi da hanyar wucewan ruwa Wanda yake nuna alama da gurin wanki ne,
A ciki gabaki daya aka turasu daya bayan daya aka saka kowace su ta tube Kayan jikinta aka sakar musu ruwa daga samansu batareda sunsan ta inda ruwan ke fitowa ba,
Ruwa sosai ne yake sauka akansu inda wata irin dauda take jiqa a jikinsu me yawan gaske tana gangara qasa take tiles din gurin ya sauya Kala haka ganin farinsa ko kadan ruwan daudar jikinsu ne kawai ke kwarara a qasa,
Wani irin qarni da tsami tareda wari ne sosai ya gauraye gurin take Wanda ya saka maaikatan mata sake ja baya suna nesa dasu dan duk bawan da aka kawo BOYEM sai an tsaftace sa sosai tin asali dan haka kowane bawa dake BOYEM ya samu Kansa a irin yanayin,
Umarni daga cikin lasifikar dake hannun jakadiyar ne ya shiga kunnuwansu cewan kowa ya Shafa abinda aka basa su wanke jikinsu sosai sosai.
Maaikatan da zasu tsaftace su ne suka fara shigowa daya bayan daya dauke da trays masu girma suna Jeruwa har suka gama shigowa kusan su goma sha biyar kafin jakadiyar ta shigo daga karshe.
Layi aka fara jansu daya bayan daya,
Ta farkon da aka fara da ita shaving cream aka shafe musu jikinsu dasu inda yake da gashi kafin aka dauki lafiyayyan almakashi aka Kama gashinta kai tsaye aka yankesa sosai aka bar Wanda tsayinsa bai wuce tsayin rabin biro ba.
Haka aka fara yi musu daya bayan daya Ana fesa Musu wani abu a cikin gashin Wanda take yake kashe dukkanin qwari ko qwarqwata idan akwai a ciki.
Haka aka ringa musu daya bayan har aka zo kansu Ayanah wainda idanuwansu suke a rufe zuciyar kowannensu na qarasa macewa tana barin gangar jikinsu.
Kama gashin Ayanah akai me tsananin tsayi take aka yankesa duk da akwai wainda suka fita tsayin gashin da yawa tinda su kusan a qasashensu babu mara gashin daman suna rage tsayin gashi yayan sarautarsu ne kadai basa rage gashi sosai sbd cikon al’ada ne ga dukkanin jinin sarauta,
Na Zuhrah ma dayake da tsayin dayafi na Ayanah haka aka yankesa Wanda ya sakata sauke ajiyan zuciya sbd shi Kansa gashin a yanzu tamkar azaba ce a garesu.
Mintina qalilan aka sake sakar musu ruwa masu yawa sosai aka sake wankesu sosai a karo na biyu kafin aka sako musu ruwan sabulu me kumfa sosai shima anan wankan sosai aka sakasu sukai tareda wanke kansu Wanda wasu hadda jini yake fitarwa tsabar qwarin dake cikin gashin suna Shan jininsu a maqale,
Sosai aka sake wankesu da ruwa me kyau kafin aka sake zuba musu kumfa sai da sukai wanka kusan so goma kafin aka sallamesu ana basu saqi na zanin Daurawa me kauri daya bayan daya suna wucewa.
Koda suka koma daki kusan da yawansu zazzabi ya gama rufe su na wankan duk sun shaqa ruwa wasu kuma sanyin ya shigesu sosai dan haka magani aka sake rabawa kowa koda haka zazzabin ance kowa ya sha.
Uniforms suka saka wainda bazasu iyaba kuwa zazzabi me karfi ya kwantar dasu Wanda ya saka da yawansu basu iya fitowa karban abinci ba harda su Ayanah wainda suke kwance sosai har jijjiga sukeyi.
Sakinah ce ta iya fita tabi Layi ta karbo musu abinci ta dawo dakin ta taimakawa Ayanah taci kafin ta ta