NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 40 of 146

tin kakanni da kakannin shekaru daruruwa ya saka sune suke juya qasar da duka kasashen zagayenta Wanda sune suka kirkira tareda kafa qasar gabaki dayanta Shiyasa kasar take da sunansu kuma haryanzu generation Bayan generation sune suke juya qasar kuma har gobe babu me irin tarin arzikinsu a qasar sbd koyaushe gaba suke sake yi ba baya ba dan hakanne ma kasancewanka jinin BOYEM a duniyar tasu ba qaramar sallama mutanen duniyar suke ganin Allah ya maka ba a zaman rayuwar duniyar dai sbd koda duk wani asalin jinin BOYEM koda zai fado duniya cikin zanin goyansa yanada arziki da dukiyar da harya bar duniya bazai gama cinyewaba, Yanada power me karfin gaske sbd ko dan shekara biyu jinin BOYEM zai iya yanke maka hukuncin da zai iya rabaka da duniya kuma Ka tafi kenan matiqar kayi laifin daya sa yace bayason sake ganinka, Hakama yanada gata da suna sbd duniya zata sansa koina kuma Ayi shakkarsa. Abu daya ne yake qaranci a zuriar BOYEM tin asali Wanda suke ganin shine kadai abinda zai iya kawo rauni a wani bangaren duk da hakan sun tsaya cak akan hakan shima kuma Allah na dafa musu waton shine yawan ‘yaya maza Wanda tin daga kakannin kakanninsu ne, Kowane zamani kowane generation yanada wuya duk namijin dake zuriyar BOYEM ya wuce samun yaya maza biyu ko uku, Mutum hudu ne kaf suka taba haihuwan yaya maza biyar da shida sai me takawas a tarin zuriyar tasu datafi hada zuriar sama da dubban dububuwan da har abada baa iya kirqe zuriarsu sedai wainda sukai mulkinsu kuma suma Mutum hudun tin a farkon karnin dasuka dade da gabata ne dan duka zuriar kowa yayi mulkinsa ya gama yabar duniyar yayansu ma sun hau sunyi sun tafi hakama jikokinsu duka sunyi sun tafi harma da tattaba kunne haka haka sarautar take tafiya, Masarautar BOYEM sune suka kafata da karfinsu da jininsu da zufansu da dukiyarsu harta kafu ta zama masarautar da kowa ke shakka yake tsoro ba masu kudi ba,ba talakawa ba hakama ba Sauran masu mulki ba kowa yana shakkarta da tsoronta sbd tsaurin hukuncin da rashin shamakinta a komai kuma hakan ya saka babu Wanda ya taba mulkar BOYEM Wanda ba asalin jininta ba kuma har abada bazasu taba barin Wanda ba jininta ba ya hau mulkinta matiqar ba Allah ya kaddaro hakan ba dan hakanne duk wani Sarkin da yayi mulkin BOYEM yana ‘yaya masu tsananin yawa sbd sunada IMEBĒTI wainda suke kiransu ARKI wato kuyangin da ake kai musu suke kwana dasu suna hayayyafar musu zuriar da suke alfaharin sunada ita fiyeda kowane ahali. *******tin daga babban lafiyayyan titin dayake tsakiyar gari da zai dauki hanyar zuwa masarautar checking points masu tsananin karfi da tsaro na wasu irin kakin askarawa da bindigogin da kowace kalar babu da wasu irin sharp wuqaqe dake soke jikin kowane jami’i,weapons dai gasunan Kala Kala marasa Kyan gani Wanda kasan Ana Dora daya akan jikinka to sai maqabarta direct kabari. Bayan tsaro Wani irin tsari ne da kowane Taku daya yake nuni da ba qaramin guri ne Ka zo ba, Gine gine ne masu tsananin tsayi da kyau da daukan ido da gigitarwa kaman zasu fado a Kanka sbd har wani jiri suke sakawa suna haske ido kaman zinariyar ce da gaske a jikinsu kaman yanda tarihi yake fada akan masarautar. Duka duka checking points uku suka wuce suka isa daular bayin dake kafin isa asalin makekiyar kofar datake kaman gida guda ta shiga masarautar. Daular bayi ake kiran babbar bangaren da aka Gina me girman gaske na horar da bayi sama da dubban miliyoyi Wanda kuma a cikin daular bayin bangare guda lafiyayyan gidan Sarkin bayi ne Wanda masarauta ta tanadar masa estate guda a daular bayin inda gidansa a cikin estate din yafi kowanne girma da tsari da tarin dukiya kafin Sauran na dukanin Sauran ma’ikatan dasuka shafi kula da dukkanin harkar bayi kowa da iyalansa da yayansa da iyalan yayansa dan haka daular bayin duniya ce guda mai zaman kanta datake cike da tsaro da tsari tareda daula tamkar wani babban shugaban wata qasar ne a nan, Acan nesa da estate na gidajen babban bangaren kula da bayin yake Wanda shima a tsare yake a tsaftace tamkar wata lafiyayyan jamiar karatu sbd komai nasu a tsare yake, Uniform ne dasu masu kyau da qarko coffee brown Wanda kowane bawan a tashin farko Kala biyar biyar ake bawa kowa kafin kuma lokaci lokaci Ana sauya musu sabbi sbd tsantsar tsaftar da BOYEM take dashi Akan mulkinta. Akwai bangare daban kuma daga nesa Wanda yake da girman dayafi koina sbd tarin manyan dabbobin daji masu mahaukacin girma da koshi sbd zakunan su da da misos jinsu naman jikinsu har wata irin rawa yakeyi sbd qoshi tareda samun cikakkiyar kulawa, Mahaukatan wild animals ba kadan suke dasu ba wainda suka samu mahaukacin training da zama savage Wanda suma kansu sarautar suke bugawa sbd hatta dabbar masarautar BOYEM din Taku ne dasu sbd training, Tsananin tsaro da tsarin yanda aka killace su wani abu ne me girma na daban dan kusan kilometers ne a tsakaninsu da inda Sauran bangarotan suke. A dayan bangaren dayake kusa da dabbobin bangaren hora bayi ne masu laifi da basu azaba dan haka daul
🏠