NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 39 of 146

oto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah. WhatsApp 08039440312 Tiktok :@sokoto jewelry seller Instagram: jewelryjunction23 ************** Ahankali hannunsa ya fito daga akwatin Wanda yake dauke da lambar data saka Wani irin Ihun murnan daya saka rumfar gabaki daya girgiza sbd Ihun samudawan Kusra dayake tashi yana ratsa kunnuwan bayinsu dake sake shiga Hali na Godiyan Allah suma daya rabasu da kusra daga karshe dai sunga karshen wata kaddarar tasu mara dadi zasu su tarar da wadda basusan yaya zata kaya ba. Sai a lokacin Ayanah ta bude idanuwanta ahankali tana zubawa qasar gabanta idanuwanta da sukai jajir tana ji a zuciyarta kaddararta bata qare ba dan kuwa sai ranar da ranta yabar jikinta kaddarar rayuwarta kila zata qare. Lumshe idanuwanta tayi tana sake jin Ihun kusrawa na ratsa kunnuwanta zuwa zuciyarta dake Wani irin quntatar da batada mafita ko samun sauki. Take aka fara Jere dunqulallen zinariyar da sai an auna nauyin kowace kafin a Jereta Ana Kirga bayin tareda auna nauyin kowane sbd nauyinsu ne yake zabar musu farashinsu, Daya bayan daya aka fara aunasu tareda rubutu wa a lasisin kowannensu farashin da aka siyesa da nauyinsa kafin a dangwala hannunsa a matsayin to a zama cikakken bawan BOYEM har qarshen rayuwarka. Ana zuwa kan Ayanah hakanan kowa ya tsayar da idanuwansa akanta Ana jin Wani irin yanayi na tausayi da Jin nauyi har aka gama da kanta ta daga hannunta a hankali ta dangwali ruwan saka shedar ta Dora akan lasisinta ta daga kafarta ta tsallaka zuwa inda rayuwarta ta koma a yanzu kwata kwata tana fita daga hannun kusra. Zuhrah Ana zuwa kanta tana dangwala hannunta kasa sakawa tayi a lasisin da zai tabbatarda fitar ta daga hannun kusrawa Hawaye masu tsananin zafi suna gangarowa daga a idanuwanta sbd daga yau shikenan sun yadda da kaddarar data rabasu da rayuwarsu ta baya da yan uwansu, Daga yau sun rabu da dukkanin abinda zai iya sake hadasu da Abaas ko wata ran, Daga yau sun zama abinda aka saka kudi aka siya sannan daga yau ne zasu fara amsa asalin sunan zama bayi sbd a baya da Allah zai kubutar dasu daga hannun kusrawa zasu iya gudu wa su Gina sabuwar rayuwa amma daga yanxu da aka biya kudin su sun zama cikakkun bayin da har abada shikenan. Rawa hannunta keyi sosai a lokacinda ta daga hannun ta saka a lasisin dayake dauke da sunanta a matsayin baiwa ta lambar dake hannunta wadda akai musu da wuta harta warke ta zama kamar Zanen tattoo. Wucewa tayi ahankali ta isa inda Ayanah take tsaye hawayen ita sun qare mata basa iya fitowa sedai Idon yayi jajir. Sakinah ma gurinsu din ta tsaya a gefe Bayan an tantance ta a hakan har aka kammala komai aka biya dukiya me tarin yawa gurin siyansu cinikayya ta gama tabbatuwa aka zuba su a motar da basusan mecece ba amma kuma basuji tsoro ba sbd babu Sauran tsoron komai ya fice musu. Sai tsakar dare sosai aka gama cin kasuwar wadda iya ta bayin aka gama ci daga nan ne Sauran kasuwancin yaci gaba da gudana Wanda zaaita ci har safe har a wuni sbd sai kasuwar tayi kwana biyar tana ci, Motocin masarautar BOYEM dai a Daren suka daga zuwa cikin qasar wadda tafiya ce me tsayi ta kwana biyu kafin ma an isa cikin qasar kafin isa babban birnin kasar inda asalin masarautar take. Motocin na daga wa aka fara bukukuwan cin kasuwa da kide kiden al’adarsu dana taya wainda suka ci kasuwar bayi Murna. Tinda suka fara tafiya hannun Zuhrah yana cikin na Ayanah sun riqe juna shiru babu me iya ko dogon motsi sbd rayuwar kowa data gama mutuwa. Sakina ma tana Dayan gefen Ayanah wadda Ayanah ta miqa wa hannunta daya itama ta Kama suka riqe hannuwan juna su ukun suna jin dumin tafukan hannun juna. Tafiya me tsayin gaske akai kafin aka tsaya aka fiddo bayin gaba daya sukabi kayi aka rarraba musu abinci da ruwa kafin kafin masu lalura suka sauke suka huta tukuna aka sake daukan hanya. Tafiya me tsayi gaske sukai kusan kwana uku suna shiga garuruwa masu girma da Kyan gaske da abinda basuma San duniya na da shi ba kafin suka fara shigowa asalin babban birnin daular BOYEM Wanda a garesu ganinsa tamkar Aljannar duniya ce da ko a labarai basu taba Jin akwai irin wannan duniyar ba, Dukkanin abinda idanuwansu ke gani kansu ya kasa dauka sbd tsoro ma suka ji ya fara kamasu mai tsananin gaske take suka Ji duniya ma suke son Bari gabaki daya dan bazasu iya rayuwa a cikin irin wannan daular ba. Kai tsaye suna shigowa babban birnin qasar Wanda yake da wani irin tsari da tsaro tareda wata irin rayuwar da ni’imar iskar ma da kake shaqa jinsa zaka yi daban, Koina a birnin Ihun tsantsar dukiya da arziki yakeyi sbd kusan duka garin yana cike da masu sarauta da mulkin kasar, Manyan daular qasar gabaki dayanta suna cikin birnin, Duk inda Ka daga kai Ka kalla tambarin masarautar BOYEM ne Wanda hakan yake nuni da karfin mulkin masarautar tafi na gwamnatin qasar da zagayenta gabaki daya, Tsananin karfin iko da tsananin dukiya da arziki tareda rashin tsoro da asalin jarumta da ahalin BOYEM suke dashi
🏠