NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 37 of 146

kai zuwa masaukin da suka Kama dan hutawa a qasar BOYEM su kafar da tarihin hakan sbd hutawan gaske zasuyi da jin dadin da akace ana dashi a qasar. Tinda aka Jere su Ayanah da sauran bayin duka a rumfar babu Wanda ya iya dagowa kan kowannesu a qasa yake suna kallan qasa sbd basuda ikon dagowa su kalli koina sai Angama cin kasuwansu. Ayanah da batada sauran kuzari ko tinanin kanta bare iya kallan koina idanuwanta a rufe suke ta soka kanta a tsakiyar kafafunta zuciyarta na Wani irin yanka da radadi me zafi, Ta rasa wasu gurbi masu girma a rayuwarta da bazata taba cikesu ba har karshen rayuwarta, Rayuwarsu ta sauya ne a dare daya,kaddararsu tazo ne a daya dare,tashin hankali da baqin cikinsu duka Yazo ne a dare ya sauya rayuwarsu gabaki Dayan tamkar kyaftawar idanuwa. Basuda sauran rayuwar da zasu kira rayuwarsu kuma, Basuda komai da zasu kira nasu sbd gangar jikinsu da rayuwarsu gabaki daya ba tasu bace sbd basu da ikonta, Daga yanzu a inda suke daga lokacinda wani zai saka kudi ya siyesu ta tabbas sun qarasa rasa kansu har abada har sai ranar da Wanda ya siyesu ya iya yantasu idan ma ya mutu batareda yanta su ba suna cikin gadon iyalinsa kamar wasu kadara. Numfashi ta sauke me dumi tana sake rungume jikinta sbd sanyi dayake rata fatarta yana keta wa har cikin qashinta da yunwa ta gama rage masa kwari. Zuhrah idanuwanta a bude suke ita sedai kanta na qasa ta qurawa qasa ido tana kallan qasar dake gabanta zuciyarta na Wani irin mutuwa da sanyin dayake na tsagwaron baqin cikin da qunci, Motsa yatsun kafarta tayi ahankali suna shiga cikin qasa ta Lumshe ido ahankali wasu hawaye masu dumi suka gangaro mata a karo na farko Bayan rabuwansu da Abaas da zuciyarsu ta kafe ta kangare, Wannan itace qasar da a yanzu zasuyi rayuwa a cikinta babu ranar fita ko tafiya harsai rayuwarsu ta qare kenan, Sun rasa uwa da ubansu da gidansu da garinsu da rayuwarsu da yanci su da qasarsu duka sbd kaddarar zuwa nan, Anan Allah ya kaddaro zasu qarasa rayuwa Shiyasa duka wannan kaddarorin suka hau kansu, Numfashi me dumi ta sauke ahankali mara sauti tana gode wa Allah Akan wannan jarabawar me nauyi da munin daya kaddaro musu tareda fatan su cika fa Imani su samu Hutu Bayan mutuwarsu sbd a yanzu da dukkaninsu kowa ya rasa babban bangare na rayuwarsa babu komai da yayi saura kuma a kaddararriyar rayuwarsu Bayan jiran lokacin mutuwa kuma dan haka duk abinda zasu gani na azaba ko baqin ciki basajin zuciyarsu ma zata girgiza ko kasa dauka sbd rayuwarsu bata shigo qasar d sauran kowane irin taushi ba a zuciya ta gama bushewa. Sakinah dake kallan qasa itama lashe lips dinta da suka bushe tayi ahankali tana Hadiye wani busashen yawun daya wuce maqoshinta daqyar Tana jin itama wannan Karan takai karshen zamowa baiwa sbd acan baya datake baiwa a gidan GHAZ Ashe ba bauta takeyi ba cikin gata take Sai yanzu ne zatai asalin bauta Bayan zuciya da rayuwar gabaki daya ta bushe musu. Dukkanin sauran bayin kowa da tinani da quncin tareda radadin da zuciyarsa take ciki kansu a qasa gabaki daya basa ma iyawa ko ikon dagowa su kalli mutane masu yanci kokuma wainda zasu iya siyensu. A haka suka kwana gurin gari ya waye suka sake wuni a gurin sedai a basu ruwa so daya da dan abinci su ci kansu a qasa babu Wanda har lokacin ya dago bare yasan kalan duniyar da suka taho. Haka suka wuni suka sake kwana babu kowane irin alamar zaa fara siyar dasu sai ranar cin kasuwar zaa bude tasu hajar a kasar dasu. ****kwana hudu sukai a gurin a Shanye sunsha rana sun bugu da rana da sanyi da iska da sauro harma da qwari Kala Kala kafin ranar cin kasuwar ta iso. Tamkar ranar sallah ta duniya haka ake ta hada hadar kasuwar da zata ci sbd manyan mutane da wakilan Masarautu da suke zuwa cin kasuwar, Daga qasashe daban daban na nesa da kusa ake zuwa cin kasuwar wasu daga qasashen nesa wasu daga qasashen kusa wasuma daga wata duniyar daban da baa San inda suka fito ba, Dan haka wasu irin mutane ne tako ina ke cika koina wainda mutane da dama basu taba ganin yawan mutane irin hakan ba ciki kuwa harda kusan duka bayin da zaaci kasuwarsu basu taba ganin tari da taron mutane masu yawa irin hakan ba dan haka kusan harda tsoron tarin girma da yawan mutanen dake cike ne sha cika su. Khams da Yaransa tin da sauran duhun safiyar ranar suka Baro gurin hutawar da suka Kama suna holewa da mata suka iso rumfar su aka sake tsara komai tareda fara tantance bayinsu daya bayan daya. Kamar kwason dankali haka aka kasa su masu karfi da cikakkiyar lafiya daban, Masu yar dama dama daban hakama maza daban mata daban hakama yan yaran da basu qarasa zama mata ba ko maza suma daban. Yanda aka rabasu din a guri daya aka hade su Ayanah da Zuhrah da sakina basu samu an rabasu ba dan haka babu motsin ko wata kuzarin yin komai da su keda suna Zaune da sarqa a kafafunsu duka babu me iya ko doguwar motsi. Rana tsaka kasuwar take kokarin fara ci amma a al’adar cinta ko a kaidar cinta bata fara ci sai wakilin Sarkin bayin qasar ya iso ya
🏠