Sauran kusrawa a garin bodar su samu shaqatawa da hutawa suma kafin su dawo Wanda a kalla basu San kwanakin da zasu shafe ba kafin dawowan tasu.
Bodar gaba baa tsaya komaiba lasisin bayinsu aka bi daya bayan daya Ana duba wa tareda tabbacin sa tukuna aka barsu suka wuce.
Suna wucewa khams ya sauke wata sanyayar ajiyar zuciyar samun nutsuwa da jin qamshin cikar Buri,
Qamshi da iskar da kake shaqa a kasar kusan daban yake sbd nutsuwa da tarin arziki kawai kake Ji da gani tako ina,
Su Karan kansu bayin nutsuwan ruhi da zuciya suka Ji suna samu ahankali cikin sanyi sbd koba komai sunsan yanzu kam sun iso qasar da zaa siyar dasu su fita hannu kusrawa,
Dukkanin bayin a lokacin aka fara fitowa dasu daga jirgin kusra a wancan bodar da suka fito duk Wanda ya saka tafin kafarsa ya taka qasar da allah ya shimfida a duniya sai hawaye sun gangaro masa na godia ga Allah daya sauko jirgin ya fito batareda ya rasa rayuwarsa ba ko mutuncinsa kokuma dai Allah ya masa arzikin fitowa daga balai da masifar datafi komai a rayuwa wato jirgin kusra.
Ita kanta Ayanah a lokacinda jirginsu ya isa asalin bodar cikin qasar dago idanuwanta tayi ahankali ta kalli ruwan qasar da suke shar iskar su na ratso musu sbd a wannan jirgin inda ake ajiye bayi ba a rufe yake ba cikin duhu a bude yake suna iya ganin koina sbd harda winduna wani sanyi na ratsa fuskarta zuwa gangar jikinta daya sakata rufe idanuwanta ahankali tana dan qanqame jikinta hawaye masu dumi na gangaro mata tinanin Nurat da Abaas na danne kirjinta da dayanzu dasu zasu shaqa wannan iskar da suka manta rabon da su shaqa sedai wari da zarni tareda tsami da karnin dakin bayin dasu ciki na jirgin kusrawa.
A bakin bodar su khams suka fara tabbatarda sun iso qasar datafi kowace a duniyar da suka sani sbd wasu Hasken wutattakin Turawa dake haske gurare daban daban hakama maaikatan mahukunta qasar gasunan koina,
Tsananin girma da fadin gari da kasuwannin bodar baa iya ganin iyakarsu sbd girman garin ya baci sbd akwai kasuwanni da gidajen da suka hau dubu Dari kuma a hakan ba baa shiga asalin cikin garuruwan dake qasar ba bare akai ga isa asalin babban birnin qasar da acan Masarautarsu take ba Wanda akwai ma tafiya me tsananin gaske.
Sake tabbatarda lasisin su na shigowa kasar cin kasuwar bayi akai tareda tantance lasisin bayin daya bayan daya tukuna suka samu saukowa suna taka qasar masarautar BOYEM Wadda take sanyaya zukatan kusrawan da bayin sbd Allah ya yanke musu azabar kusra.
#MAMUH
#BOYEM
#BOYEM
#BOYEM
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
18
*JEWELRY JUNCTION*
08039440312
Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma,
Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne??
To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan,
Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana,
✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌
✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌
✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌
✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍
🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah.
WhatsApp 08039440312
Tiktok :@sokoto jewelry seller
Instagram: jewelryjunction23
*********
Sabuwar duniyar da kamar ba wadda suke rayuwaba suka samu kansu cikeda farin ciki da mamakin abubuwan rayuwan da suke gani da dama Wanda suke tinanin idan nan bakin bodar ruwan qasar ne yake da daukan hankali da mamakin duniya haka to yaya cikin qasar zata kasance musamman masarautar da a tarihi da labari suke jin tsaruwarta wasuma cewa suke da kalar asalin zinari akai adonta koina nata zinariya ce ke haskata.
Duk bawan da zai samu shiga masarautar BOYEM da sunan bauta ma a cikin tarihi sune masu saa da rabo ma dan haka ne da dama suke siyar da kansu a matsayin bayin BOYEM idan sunxo cin kasuwar sedai danginsu su dauka ya mutu sbd shikenan basa sake ganinsa.
Gidan ma sauki suka kama a cikin babbar kasuwar da zata fara ci ta bayin nan da kwana biyu dan haka rumfar da zasu ci kasuwa suka fara kamawa me girman gaske suka biya komai kafin suka zube bayinsu a rumfar tareda maida musu sarkar kafafunsu da duka aka cire sai aka Jere su tareda barin masu tsaresu Bayan sun saka tambarinsu babba Akan rumfar su dake nuni da kasuwancinsu.
Wucewa su