o abinci sun dena iya ci sedai sakina ce take karbowa ta rarrafo ta zauna tsakiyar su ta ringa basu a baki Akan dole sbd karfinsu dayake sake yin qasa sosai Wanda Sai a yanzu sakina ke sake tabbatarda kasancensu su duka hudun a tare da gaske shine rayuwa,ruhi,kuzari da karfin zuciyarsu sbd a yanzu Ayanah da zuhran gasunan sun zama tamkar marasa cikakken hankali.
Idan dare yayi haka zata zauna tsakiyar su ta kwantar da kansu a jikinta tana Shafa bayansu da fuskar su sbd samar da nutsuwa ko yar qanqanuwa ce a zuciya da gangar jikinsu.
Idan gari ya waye haka zata jawosu inda ake fiddosu Ana zuba musu ruwa sbd su wanke kullum kafin isarsu inda zaa kaisu,
Haka zata janyo su kaman qananun yara Ana dukansu duk da yanzu an rage dukansu sosai sbd duk anason suyi dan yi Kyan kallo dan haka kullum Ana fiddosu a hade guri daya a ringa zuba musu ruwa masu tsananin yawa suna goge jikinsu Wanda baya goga jikinsa lokacin da ake zuba ruwan duka yake sha da Bulala dan haka sakinah ganin kullum sai an dake su amma tamkar jiran duka sukeyi sbd ya wahala ta kashesu subar daniya ya saka koyaushe idan Ana zuba ruwan itace me wanke jikinta ta wanke nasu su dukan.
Ana gama wankesu haka zaa sake shanyasu a rana sai sun bushe a gargadasu a maidasu inda suke a rufe,
***********sake nutsawa tafiyarsu tayi Wanda a yanzu suna samun abinci sosai hakama wankan kullum ake musu dan haka yunwarsu ta ragu sosai sedai shi wanka kam ya saka duk fatar su ta bushe qayau sun koma wata sabuwar halittar daban kowannensu cikin bayin ka kalla tamkar an birkidasa cikin farin gari an ciro sbd kullum ruwan kawai ake zuba musu sannan a shanyasu a rana.
Har lokacin babu abinda ya sauya a sabuwar kaddararriyar rayuwar data samu su Ayanah,
A yanzu basa iya ko magana daga ido se ido sai kallo dan haka ne ita kuma sakinah nauyinsu ya dawo kanta gabaki daya fatarta dai suna isa qasar da zasu din a siyesu koda kashesu zaayi gwara a siyesu acan din da azo baa siyesu ba kusrawa su dawo dasu.
**********Tafiyar sati bakwai sukai tukuna jirginsu ya fara shigowa qasar da kowane tarihin zamanin ke fadar iko,girma,mulki,arziki da tsananin da masarautar qasar take dashi sakamakon sarakunanta da suke aje tarihi me girman gaske kafin rasuwa subar karagarsu.
Tsananin tsaro da tsari tareda dokokin dake zagaye da qasar daban yake da duka Sauran qasashen duniyar Wanda ya saka zuwa qasar yake tamkar samun babban rabone da saa a duniyar da suke rayuwar,
Suna gap da isowa kusan iyakar bodar da zata shigo dasu farkon ruwan qasar saida aka sake tsafta ce kowane bawa kafin suma suka wanke kansu da dan gyara komai na tsarinsu dasu kansu din.
Boda biyar ce tin daga farkon shigowa nahiyar qasar kafin isa cikin bodar ruwa ta cikin qasar wadda ita kanta bakin bodar cikin kasar daga nan bakin zuwa cikin qasar tafiya ce tsananin tafiya.
A bodar farko saida suka share kwana daya a bakin wajen qasar batareda sun samu damar shiga ba saida aka gama binciken tabbacin kasuwan bayin sukeyi kafin aka barsu suka wuce.
Wuni guda suka sake share wa Bayan barinsu Checking point na bodar farko kafin suka iso ta biyu.
Anan ta biyu ba saida suka share kwana daya harda wuni kafin aka gama tareda basu damar wucewa.
Shima tsakanin boda ta biyun zuwa ta uku tafiyar wuni guda ce sukutum sai tsakar dare suka isa dan haka baa duba kowane jirgin ba duka jiragen da suka taho a wajen bodar suka kwana sai washe gari aka fara aiki akansu.
Tashin farko abinda suka fuskanta anan shine bazasu shiga da jirginsu can bodar karshe ta cikin asalin qasar ba dan haka duka yawansu anan bodar zasu tsaya da jirginsu sedai shugabansu da wasu daga cikin manyansu da bazasu wuce Mutum Ashirinba dan a qaida baa wuce hakan dan hakan komai yawan bayinsu koda bayinsu sunfi dubu daruruwa to su dai da zasuci kasuwarsu bazasu wuce Mutum ashirin ba kuma da jirgin bakin bodar zasu biya su dauka su isa can sai sun dawo su koma jirginsu su koma inda suka fito.
Wannan dalilin ya saka kowace boda dake qasar girman bodar kawai yana fin girman qasashe da dama sbd irin tarin manyan mahaukatan jiragen ruwan dake tsayawa ko zama a gurin ba qaramar qasa ke iya daukansu ba,
Kowace boda dake qasar tamkar wata qasar ce me zaman kanta sbd gari ne da mutane sosai sbd duk wani maaikacin bakin boda na qasar anan yake rayuwa da iyalansa da yan kasuwarsu harma da sauran manyan huldodon kasuwancin qasar da akeyi kuma anan ma Ana cin kasuwar bayi sedai acan babbar bodar ake cin asalin babbar kasuwar bayin datafi kowace a duniyarsu,
Hakanne ya saka kowace bodar qasar gari ce guda mai zaman Kansa hidima sosai da cin kasuwanni akeyi tareda dubban Jamaa.
A nan jirgin kusrawa ya tsaya suka gama karba da biyan komai na tsantsar dukiya me yawan gaske kafin suka fiddo bayinsu kaf aka Kirgasu tareda biyawa kowane bawa daya Lasisin shiga qasar.
Saida suka kwana biyu a wannan bodar Ana harkar lasisin shiga qasar kafin aka kammala komai suka zuba bayinsu a sabon jirgi da zai kaisu suka wuce tareda barin dukannin