NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 33 of 146

rasa barin rayuwarsu a qasar da bazasu taba mantawa ba tinda Nurat dinsu na qasar. Rayuwarsu ta raunana daga lokacin dan haka ko abinci sun wani Dena ci sai sakinah ce take wawusowa ta kawo musu ta takura musu tareda roqo ta samu su ci amma gabaki daya rayuwar ta qarasa fita kansu barin duniyar shine kawai fatansu a yanzu, Quncin da suke ciki ne ya saka duk wahalar da suke ciki yanzu basa jinta dan kuwa a yanzu kusan babu abinda bazasu iya jurewaba a rayuwa illa rabuwa da juna. ******Tafiyar sati biyu sukai a ruwa suka isa qasar Nuggi wadda qasa biyu ce a gabanta kafin isa BOYEM, Tinda suka tinkaro qasar jikin dukkaninsu yayi sanyi duk da basusan suna tinkarar kowace qasaba a taqaice ma basusan ina suke ba kokuma ina suke dosa, Da asuba ne suka iso bakin bodar qasar dan haka baa bude su ba saida gari ya fara haske tukuna aka basu abinci. Yau Ayanah da kanta ta shiga karban abincin ta rarrafo gefensu ta zauna ta kallesu kowannensu ya zama wani halittar daban yunwa na yawo koina a jikinsu da wahala. Zaunawa tayi tsakiyar Zuhrah da Abaas din ta sauke ajiyan zuciya me sanyi da mutuwar jiki kafin ta dago ta kalli Abaas ta saka hannuwanta biyu ta Kamo fuskarsa ta sumbaci goshinsa ta sumbaci gefen fuskansa da tsananin sanyi murya tace ‘Bazan iya rayuwa babu Kai ba hasken idaniyata ka riqe hakan kada ka yadda ka sake laifin da zasu illatamun kai kaji???? Dago idanuwansa da sukai ja yayi take ya sauke Akan fuskanta da idanuwanta suka ciko da hawayen rauni da tsananin kaunarsa dake bayyane a fuskanta. Gangarowa hawayenta sukai tace ‘Kamun Alkawarin bazaka taba sake abinda zai saka rayuwanka a hadari ba koda bana raye tareda ku? Saurin kallanta yayi yana son rufe bakinta da hannunsa ta riqe hannun tana girgiza masa kai hawayenta na gangarowa da gudu tace ‘Kamun alkawarin hakan Abaas, Kamun alkawarin zaka kula tareda kiyayewa sbd mutuwa zanyi idan wani abu ya samu daya daga cikin ku biyun,dan Allah Kamun Alkwari…..’ Qarasa fada tayi muryanta na karyewa sosai tana sunkuyar dakai sbd gajiyayyan kukan dake taso mata. Kama hannuwanta yayi yana hawaye masu dumi shima ya sumbaci hannunta kafin ya kamo kanta ya sumbaci goshinta yana rungumeta cikin jikinsa yana share mata hawayenta. Tashi tayi ahankali daga jikinsa ta juyo ta kalli Zuhrah tareda zuba mata ido tana kallanta cikeda tausayi da kauna me karfi, Hannu takai ta shafi fuskanta ahankali kafin ta sumbaci gefen fuskarta tareda rungumeta ahankali ta bude baki tace ‘Zan tabbatarda na kashe kaina kafin wani ya lalamin rayuwarki sbd ke zuciyata ce,ke Rabin jikina ce,ke jinin jikina ce keda Abaas…’ Sake sumbatar goshinta tayi tana hada su itada Abaas ta rungume sukai shiru tsawon lokaci a hakan kafin ta janye su tana fara basu dambun alkamar da akai zalla babu komai a cikinsa tafara basu a baki da hannunta tana kallansu kaman zata cinyesu. Basu takeyi a baki suma suna diba suna bata hakama Abaas na bata yaba Zuhrah hakama Zuhrah tabawa Ayanah din ta bawa Abaas a haka suka ciyar da junansu babu Wanda baya hawayen qunci da radadi a cikinsu. Suna gamawa suka kwanta jikin juna sakinah na gefensu tana hawayen tausayinsu dana kanta da batada kowa a duniyar Bayan su. A haka suka wuni shiru jigum babu motsin komai sbd se dare kuma zaa sake basu abinci dan haka ko motsi babu keyi dakin tsit yake. Har dare suna jikin juna saida Daren yayi tukuna zaa fara cin kasuwar bayi ta garin dan haka aka zo aka bude kofar su dan diban bayi. Ana budewa take suka fara diban suna turasu waje, Bayi arbain zasu siyar dan haka Ana kirqa Talatin da Tara Wanda yake diban ya finciko Abaas kai tsaye ya jefa kofa yana cikewa arbain dashi, A tsananin haukace Ayanah ta miqe tana riqe hannun Abaas din da tsananin karfin gaske har tana kife wa qasa sbd sarkar kafarta amma bata sake hannun Abaas ba Wanda shima ya riqeta da tsananin karfin gaske duka jikinsa na daukan mummunan rawa, Zuhrah ma fadowa tayi kan Abaas din tana riqe sa da karfin gaske tana kiran sunansa da karfin gaske duka jikinta jijjiga tsabar rawa. Ayanah miqewa tayi tana fadawa jikinsa ta qanqamesa da karfin gaske tana cewa a siyar dasu tare dan Allah idan ba haka ba mutuwa zatai. Zuhrah ma hakan ta riqe sa tana kukan da ko maganarta bata fita. Ganin hakan y saka kai tsaye aka dauko buloli masu tsananin tsayi aka fara dukansu da ita amma Sam daga Ayanah har Zuhrah da Abaas din sun kasa sakin juna Neman zarewa sukeyi da tsananin tashin hankalin daya saka sakina ma fasa kuka tana fadawa kansu tana rufe su sbd tsananin dukan da ake musu jini na fita jikinsu. Azabar dukan da ake musu sun kasa sakin juna jininsu na fita ya saka gangar Zuhrah kasa dauka ta fara zame wa qasa idanuwanta na Neman rufewa zuciyarta na tsananin gajiya wa da komai ta zube a gurin a some. Ayanah data kasa sakinsa duk da komai nata musamman zuciyar sun gama gajiya da rayuwar gabaki daya sun gaza hannuwanta jini sukeyi amma ta kasa sakinsa daukanta ake cigaba da yi
🏠