rin wannan,
Koda iyayensu suka bar duniyar sun mutu a hanyar Neman tsira da sauran mutuncinsu,
Amma ayau Nurat ta rasu tabar duniyar da ciwon baqin cikin abinda ya faru da ita,
Bata rasu ba saida tashin hankalin data fuskanta ya dawo da hankalinta jikinta dan hakanne baqin cikin abinda y sameta dashi ta rasu a ranta dole.
Kaman yanda Baqin cikin rashinta bazai taba barinsu ba hakama harsu mutu sautin kukanta a lokacinda ake keta haddinta bazai taba fita daga kunnuwansu da zuciyarsu ba shikenan ya musu rauni a zuci.
Har rana ta keto suna rungume da gawar Nurat sun kasa sakewa saida aka bude su dan basu abinci,
Jeho abinci akeyi masu karba na wawason karba amma babu Wanda ya motsa a cikinsu suna rungume da ita har lokacin babu Wanda idanuwansu ke Dubuwa sbd kumburi da ja.
Saida aka gama Rabon abincin a daidai lokacin suka iso qasar hidua jirginsu ya tsaya a bodar qasar zaayi abinda aka Saba tukuna aka shigo dan diban bayi Sai a lokacin akasan da akwai gawa a cikin gurin.
Zabar bayinsu suka fara yi wainda zasu siyar suka fitar dasu kafin suka dawo suka dauki gawar wadda aka cire daqyar a hannunsu Ayanah da suka riqeta gamgam dukkaninsu ganin bazasu sake ba aka dauko Bulala aka fara dukansu da karfi jikinsu na fashewa amma har lokacin kasa sake gawar sukai.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
16
*JEWELRY JUNCTION*
08039440312
Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma,
Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne??
To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan,
Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana,
✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌
✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌
✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌
✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍
🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah.
WhatsApp 08039440312
Tiktok :@sokoto jewelry seller
Instagram: jewelryjunction23
***************
Wani irin mummunan dukan Bulala aka ringa saukarwa hannuwansu Ayanah Wanda ya saka hannuwan nasu fara fashewa harma dukan yana sauka kan gawar Nurat wadda tayi haske sosai fuskanta tayi Wani irin fayau idanuwanta dake rufe sun boye mummunan ramar dasuke ciki kafin rasuwarta,
Ayanah Akan gawar ta zuba ido tana kallan dukan dake sauka akanta Wanda zuciyarta ta sake gabaki daya taji tana hakura da dangana tinda Nurat ta rasu hakan shine saukin data samu da hutawa daga wannan duniyar da babu komai cikinta sai qunci da azaba hakama babu abinda gawar Nurat ke buqata Bayan Hutu koda kuwa ba binneta zaayi ba taba buqatar abarta ta fita hannun kusra dan haka ahankali ta sake hannuwanta suna saki idanuwanta na tsananta ja jikinta gabaki daya na sanyi hawaye takeson yi amma sun kafe Idon ya gaji da kuka.
Zuhrah ma azabar dukan dayake fasa hannunta y saka hannuwanta saki tana sunkuyar da kanta kasa hawaye na diga babu sautin kuka sbd karfinta daya qare tas.
Abaas ne ya kasa sakin Nurat din dan haka suka taru akansa suna masa wani dukan dayake fasa fatar jikinsa har jini na fita ya kasa Sakinta kuma y kasa kuka dan haka suka tsananta dukan har saida Ayanah da bata hayyacinta sakinah ta girgizata da karfi ta tana cewa
‘Abaas zai rasa ransa’
Dagowa Ayanah din tayi tana kallan dukan da ake masa jikinsa duka yana jini da dan sauran karfin datake dashi ta fada Kansa ta rungumesa tareda Kama hannuwansa tana banbarewa daga Nurat jikinta na wata irin rawa sbd itama Jin takeyi kaman bazata iya barin a tafi da Nurat din ba.
Girgiza Kai Abaas keyi da karfi yana kasa Sakinta yana kallan Ayanah wadda ta kasa dagowa sbd yanda jikinta ke rawa ta zare hannuwansa tareda rungumesa tana basa kariya daga dukan da ake masa har lokacin aka hada su tare akai musu mummunan dukan daya saka Zuhrah bata kariya itama dukan na sauka kanta.
Saida suka gaji dan kansu sukabar dukansu suka dauki gawar Nurat suka fice da ita.
Babban arzikin da Nurat ta samu Bayan rasuwarta shine suna bakin bodar wata qasar dan haka ba damar yar da gawa sbd cikin mutane ne dan haka rami akai kaman kowace gawa aka rufeta a qasar.
Kwanansu biyar a qasar suka barta aka wuce sedai tamkar zuciyoyinsu Ayanah ne aka Bari a qasar haka suke Ji sbd tamkar sun