NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 31 of 146

Ayanah zubewa tayi jikin sakinah gabaki daya jikinta na saki idanuwanta na kasa Juyawa ta koma kamar wadda aka zarewa komai aka Barta da rai kawai. Jin hakan sakinah ta sake rungumeta jikinta kukanta na tsananta Tana Jin inama a ranar da suka so kashe kansu ta barsu sun mutu sun bar duniyar da sun huta da ganin wannan balain da daace iyayensu na raye mutuwa zasu yi idan suka Ji wannan mummunan ranar. Tsit babu Wanda ya iya ko dogon motsi a dakin kwata kwata kaman yanda babu Wanda ya sake Jin ko kukan su Ayanah ne dukansu sun mutu a inda suke babu abinda ke motsi a jikinsu Bayan zuciya dake bugawa. Gap da asuba aka bude dakin Wanda ya saka su Ayanah daga Kai ahankali suna kallo aka turo Nurat wadda Kayan jikinta gabaki daya suke a yage harma kusan Rabin jikinta duka a bayyane. Abaas ne ya Tara hannuwansu biyu ya tareda ta fado jikinsa ya rungume ahankali yana rufe jikinsa ta inda jikinta yake bayyane yana sake rungumeta tsamtsam. Wasu hawaye ne masu dumi suka gangaro daga idanuwanta Wanda ya sauka tafin hannuwan Zuhrah data motsa zata tabata, Saukar hawayen nata ta saka Zuhrah kallan fuskanta cikin duhun bakinta na budewa da tsananin sanyi tace ‘Nurat,Yene(my/tawa) Nurat,Yene fikir(love/masoyiya) Nurat Rabin Raina.’ Wasu sabbin hawayen ne suka gangarowa Nurat din Tana son Dora hannunta Akan na zuhrah din ta kasa dan haka ta rufe idanuwanta bakinta daqyar ya iya budewa tace ‘Ammah’ Kalmar yanka zuciyar Ayanah da dukkaninsu tayi Ayanah ta rufe idanuwa hawaye masu tsananin zafi suka gangaro mata ta motsa hannuwanta dake rawa ta Kai fuskar Nurat din taji wani abu yana gangarowa ta hancinta Wanda ta tabbatarda jini ne yake fitowa ta fasa wani irin wahalallen kuka Mara sauti tareda Kai fuskanta ta hade data Nurat din tayi sumbaci goshinta ta sumbaci hancinta tareda sarqe hannunta da nata Tana kasa furta komai sai sumbatar hannunta taje yi tana wahalallen kuka Mara sauti jikinta a mace gabaki daya ba karfi ko daya. Zuhrah hannuwanta ta kasa janye wa daga hawayen Nurat din dake zuba suna zuba a hannunta itama kukan takeyi sosai kaman ranta zai fita mara sauti, Nurat data dawo hayyacinta Tana jinsu amma babu inda take iya motsawa a jikinta sbd jininta dayake qarewa yana qarasa zubewa sbd tin acan take zubar da jini sosai haryanzu sosai yake fita a jikinta batareda yan uwanta sun saniba duk da ko sun sani basuda abinda zasu yi sedai zubawa sarautar Allah ido. A haka suke Zaune kowannensu kuka ne na fitar hankali sukeyi mara sauti har lokacin Abaas yana rungume da ita cikin jikinsa hakama Ayanah na riqe da hannunta tana sumbata Tana kukan da shi Kansa kukan ya gaji sai Zuhrah dake tare hawayenta da hannuwanta duka biyu kowace diga yanka zuciyarta yakeyi,sakinah ma Tana Bayan Ayanah kuka takeyi kawai tana kusan abinda dukansu suke Ji, Gari ne yi yi haske sbd safiyar datai dan haka duhun dakin ya ragu sosai suna iya kallan fuskanta kuma har lokacin babu Wanda yayi hayaniya ko doguwar motsi a dakin sbd duk da suna qangin bauta suna sheda tsananin kauna da son da yan uwan kewa juna kaman rai, Ahankali Nurat din ta sake bude ido ta zubawa Abaas Wanda ya kasa kuka sedai jinin dake fitowa daga bakinsa idanuwansa sunyi jan da gap suke da fara fidda jini, Hannunta ta daga daqyar yana rawa sosai ta share masa jinin bakinsa Tana kallan cikin qwayar idanuwansa hawaye suka sake gangaro mata ta kasa iya cewa komai kafin ta dauke idanuwanta a galabaice tanason kallan Zuhrah da Ayanah amma Allah bai bata ikoba jikinta ya sake ahankali ranta na fita. Dukansu babu Wanda ya motsa sbd tashin hankalin daya wuce Kai tsaye cikin kansu ya sanqarar da komai nasu, Sakinah ma mutuwar Zaune tayi dukansu suka dauki mintina a hakan kafin Ahankali Ayanah ta motsa tana tallafo fuskan Nurat din datai haske sosai tareda duka jikinta sbd jininta daya gama tsiyayewa tas ta hade fuskanta da tata muryanta na rawa tace ‘Nurat rayuwata, Nurat hasken rayuwata,yene Nurat,Nurat kece kuzarina, Nurat kune haske da kuzarin rayuwata da ruhina da bazan iya rayuwa babu ku ba, Nurat kune karfin daya saka zuciyata take bugawa haryanxu batareda ta tsaya ba, Nurat ke suka keta amma mu rayuwar ce aka keta sbd kece rayuwarmu, Nurat ki bude idanuwanki ki kalli halinda muke ciki Bazamu taba dawowa daidai ba har abada idan babu ke koda kuwa mun samu sauyin rayuwa, Nurat,Nurat…….wani irin kuka me tsananin jijjiga duk me saurare da ratsa zuciyar kowane dan Adam dazai jisa ta sake Tana sumbatar tsakiyar kan Nurat din da goshinta kafin ta rungume kanta a kirjinta tana rufe idonta kukanta naci gaba da fita. Zuhrah ma hannunta Nurat din ta riqe ta sumbata Tana rungumewa kukanta na fita da tsananin kashe jiki, Abaas a kirjin Nurat din shima ya kife Kansa a Karan farko da sautinsa ya fita Bayan tsawon watanni yana fasa wani irin kuka mai tsananin taba zuciya da narkarwa. Basu taba tunanin samun kansu a cikin wannnan mummunar halin ba da zasu rungume gawar daya daga cikinsu ba a Hali mafi muni i
🏠