NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 30 of 146

akin suka kalla da wani irin mafi girman firgici sbd jin baa cikin dakin take ba dakin dake samansu ne na shugaba khams… #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 09033181070 15 *JEWELRY JUNCTION* 08039440312 Ina macen datasan Yar kwalisa ce ko kuma wadda ke son zama cikakkiyar Yar kwalisa da zata kece Reni a cikin yan uwanta mata harma da maza ma, Ina macen dakeson ta shiga mutane a kalli wuyanta da hannuwanta a sake kalla batareda an tantance asalin gwal da diamond ne a jikinta ba ko kuwa me Kama dashi ne?? To tazo ga inda dukkanin wani burinta zai cika gameda son hakan, Mata Da Ado da Kwalliya Akasanku JEWELRY JUNCTION shago ne Na kayan Kawa Na Mata Manya DA Qanana, ✅duk wani nau'in design Na Sarka, 'Yankunne, Awarwaro, Zobe, Agoggo DA sauransu akwai su kala daban, daban. Sayen daya Ko sari👌 ✅Munda ready to wear Na Adire dana materials daga kan boubou gowns zuwa palazzo DA tops dinki Na zamani👌 ✅Idan ke ma'abociya son Kamshi ce munada turaruka kala daban daban masu Kamshi da rike jiki👌 ✅Gefen inner wears din Yara ma ba'a barmu a bayaba, bra tops, half vest,vest, boxers DA pants Duk akwai masu kyau da inganci😍 🛒Shagonmu na nan a kan tanki road, guiwa low-cost a cikin garin Sokoto. Muna tura kaya ko wace jiha cikin Aminci DA Amana In Sha Allah. WhatsApp 08039440312 Tiktok :@sokoto jewelry seller Instagram: jewelryjunction23 ************ Miqewa tsaye dukkaninsu sukai kafafunsu na kasa daukansu sosai sbd zaman dayake cinye lafiyar kafafun, Jijjiga da fizga jikin Ayanah yakeyi bama rawa ba ta bude Baki da karfin gaske Tana kwala kiran Nurat wadda take Ihun itama sosai. Abaas harshensa yake cizo yana wani irin gurnanin kiran Yar uwarsa a zuciya jini na fitowa bakinsa sbd mummunan tashin hankali da yanda yake cizan harshensa. Zuhrah Neman zarewa takeyi itama kaman Nurat Tana qwala kiran Nurat qafafunta na kasa daukanta. Sakinah ma kuka takeyi sosai zuciyarta na bugawa kaman zata fado, Miqewa tsaye Ayanah tayi cikin tsananin duhun tana kokarin taka mutane ta isa kofar ta kife sbd sarkar kafarta amma bata tsaya komaiba jikinta na tsananta rawa ta sake miqewa kwala kiran Nurat da karfin daye amsa dakin dukansa har sama inda Nurat din take Tana sake faduwa taba sake tashi tana taka mutane hankalinta gabaki daya ya gushe daga jikinta Ihun kiran Nurat takeyi Tana jin kaman mutuwa zatai a lokacin, Ihun Nurat dinne yafara ratsosu itama cikin tsantsar azaba tana kiran Ayanah da sunan Ammah muryanta ba dadin sauraro. Isowa setin kofa Ayanah tayi tafara bugawa da hannuwanta tana wani matsanancin kukan da ihu, Yanda take bugawa hannuwanta duga biyun da karfi batareda damuwa da yankewan da hannun keyi ba ga qusa dake jikin gurin Tana fasa hannuwanta jini na fita jin kawai takeyi tamkar ranta ne zai fita idan rayuwan Nurat dinta ta lalace. Kukan datake yi Sam bata hayyacinta sbd da a gabansu ne ake kokarin hakan da yau duka zasu bar duniya sbd bazasu tsaya kallo ba zasu qwaceta koda hakan na nufin rabasu da ransu. Jini sosai taje fiddawa a hannuwanta amma ta kasa denawa sbd bata ma Jin Zafin komai kukanta na qaruwa sosai har maqoshinta na kasa fidda sauti. Abaas da Zuhrah harma da sakina da suma kowa ke cikin mummunan Hali suka rarrafo basa gani zuwa inda sautin muryan Ayanah din yake fita Zuhrah ce tayi saurin riqeta Tana rungumeta sbd jinin dataji hannuwanta nayi data lalabo ta tareda fasa sabon kuka itama jikinta na fizga, Abaas ma Kansa yake bugawa a kofar yana wani irin kuka zuciyarsa na yagewa tako ina da radadi me yawa ga bakinsa bazai budu ba dai harshensa yake taunawa yana jini yana cigaba da buga Kansa a kofar, A daidai lokacin da Nurat ta qwalla wata mummunan qara wadda take tabbatarda azaba ce ta keta ta da akai da wasu irin surutai da khams ke sakewa a cikin kunnuwansu suna ratsa zuciya da kwakwalwansu take kowannensu ya silale qasa suna yin tsit sedai sakinah ce ta saki wani irin kuka a lokacin Tana riqe hannuwansu su duka ukun a cikin nata duka biyu sbd yanda suke jijjiga batareda sun iya sake kowane irin yunquri ba alaman zuciyarsu bugawa zatai ko ta dauke wuta, A cikin kunnuwansu sautin duk abinda khams keyi yake sauka tareda kukan Nurat dake fita har tayi tsit babu kowane irin sautinta sai nasa Wanda duk abinda yayi da ita kunnuwansu sunji musu Wanda kuma sauti ne da zai zauna a kunnuwansu da zuciyoyinsu har abada har ranar da jinsu zai dauke Bayan rai ya fita a jikinsu, Zuhrah juyewa kanta yake yi itama sbd dukan da zuciyarta ta samu mummunan dayake Neman buga zuciyarta. Sakinah rungumesu tayi da hannuwanta Tana qanqamesu kukanta na tsananta sbd yanda dakin yayi tsit kowane bawan dake jirgin ranar duk da halin da suke ciki kukansu Ayanah din ya sanyaya jikinsu tareda hawayen tausayin qaddadarsu su duka da basusan ya zata qare ba.
🏠