NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 29 of 146

ya fito zigidir yana sauke Numfashi da shakar iska me dadi yana jin Kansa wasai hakama ya samu gamsuwa sosai da ita duk da bata tsaya ba. Yaransa biyu dake gadin kofar dakinsa ne suka fada dakin suka daukota tareda fitowa da ita suka fice zuwa maida ita. Wasu bayin ne guda biyu suka fada dakin suka gyara masa tareda hada masa ruwan zafi a qaton bahon dayake shiga ya kwanta ciki yayi wanka suka fice. Komawa dakin khams yayi yana jin bacci sosai a idanuwansa ya fada ruwan ya wanke jikinsa kawai ya fito ya fada gadon ba komai a jikinsa ya bige da bacci. A kofar dakin kafin a maidata suka ajiyeta aka kawo ruwa masu sanyi aka zuba mata a jikinta jinin dake fitowa gabanta yafara bin ruwa yana wankewa batareda ta San meya ke faruwa a rayuwarta ba suka bude kofar tareda jefata suka rufe suna barin gurin. Kasa motsawa kowa yayi bare dogon numfashi a dakin hakama babu Wanda ya iya ko Juyawa ya kalleta duk da duhu ne bare tabata ko bata taimako. Ayanah data rintse idanuwanta da karfi Tana dauke Numfashi sbd tsoro da bugawan zuciyar gabansu data fado har hannunta na sauka kan kafafun ayanar batareda ta farfado ba. Tsawon Daren a wannan mummunan halin suke haka aka ringa dawo dasu Dayan bayan daya sedai Mutum biyar kadai suka dawo sauran biyun an kashe an jefar. Asuba tayi har gari ya waye sosai su Ayanah sunyi tsit baccin wahala da ake yi daga Zaune a dan sauke su Ayanah taji an Kama kafarta a razane jikin na daukan rawa ta bude ido Tana firgita sedai kafin tayi baya yarinyar ta sake riqe kafarta tana son bude baki tayi magana amma bazata iyaba sai hawaye masu radadin dake bin fuskanta. A sanyaye Ayanah ta Dora hannunta akai nata din Tana kasa cewa komai. Daqyar cikin azabar yarinyar tafara kokarin miqewa amma take jini ya balle mata Wanda ya sakata Lumshe ido Tana sake qanqame hannun Ayanah ranta na fita take. Ayanah batasan ta rasu ba ta sake riqe hannunta dan bata sassauci sbd duhu ne. Baa basu abincin safe ba haka suka wuni a rufe har saida Ayanah taji jikin yarinyar yayi sanyi sosai ya sanqare ta gane mutuwa tayi dan haka ahankali ta zare hannunta daga nata tana kuka mara sauti jikinta na qarasa mutuwa sosai. Sai dare aka zo basu abinci akaga gawar yarinyar aka dauketa tareda fiddata daga cikinsu aka jefar a ruwa. Abincin da aka basu ranar cikin damuwa da sanyin jiki suka cisa sbd zuwa lokacin dai sun sake tabbatarda rayuwar ba sauki a tsakanin wahalar ko mutuwar. ******** Nisa rayuwarsu da tafiyar keyi a cikin kusrawa dan zuwa lokacin sunkai watanni biyar a cikinsu batareda sunkai inda Allah zai yanke tasu wahalar ba, Qasashe sosai daban daban ake tsayawa anata rage bayi Ana kuma tsayawa wasu garuruwan Ana qara wasu. Tsawon wannan rayuwar da sukai ko so daya Nurat bata taba dawowa hayyacinta ba, Abaas bai taba bude bakinsa ba maganarsa ta jima da qarewa, Zuhrah bata taba fita tsoro da firgici ba, Ayanah bata taba Dena kuka na fili dana boye ba,.zuciyarta bata taba samun Hutu da sassaucin baqin ciki da qunci ba koma daqiqa ne, Sakinah kuwa bata taba Dena adduarta akansu ba da zubda hawayen tausayin su da kanta ba, Dan hakanne rayuwar take tsananta tsanani a garesu, Nurat yanayinta a kwanakin rikice wa yakeyi Wanda hakan ya karya dukkanin kuzari da juriyarsu, Wata irin rama takeyi Tana yin fayau dan haka suka Dena cin abincinsu suna tattarawa suna bata saisu ci na Mutum biyu su kuma su taru suci sauran. Babu wani sauyi dan haka jikinsu ke sake yin sanyi da shiga sabuwan damuwa, Daren da zasu isa qasar Gaku baccin wahala da damuwa ya dauke su daqyar sai aka bude kofar wannan Karan ba hasken farin watan dan haka cikin duhun kawai aka fara damkosu kawai Ana jeho wa waje saida aka dauki mace tara tukuna aka rifesu. Ana rufe su gurin yayi tsit Zuhrah dake maqe da jikinta Tana rawar jiki sosai sbd yau duk har gurinsu aka taho saura dakan a damqota Allah ya kubutar da ita dan haka jikinta ke rawa sosai tana kakkarwa. Motsawa tayi Tana fidda hannunta daya dan sake kamo Nurat datake riqe da ita tashin hankalin ya raba hannuwansu sai taji babu Nurat din a gefenta. Zuro hannuwanta tayi duka biyun taba lalubar gefenta da sauri hannuwanta na tsananta rawa taji babu Nurat da karfi ta Ambaci sunanta saida gurin ya amsa gabaki daya da hakan. Ayanah da zuciyarta ta tsaya cak da bugawa hannuwanta na muguwar rawa ta miqa tana lalubar Zuhrah Tana cewa ‘Meya faru? Ina Nurat din?? Girgiza Kai Zuhrah tayi Tana Neman zarewa tace ‘Nurat banjitaba,bata nan,banji ta ba’ Abaas ma cak kirjinsa ya Dena bugawa ya Kama hannun Ayanah da karfin gaske yana son magana amma ba dama sbd alkawarin dayake kansu dan haka cizon harshensa yafara yana jijjiga Ayanah da karfin gaske. Ayanah da karfi itama ta kwala kiran Nurat din wadda kaman daga sama suka Ji saukan muryanta a tsakiyar kunnuwansu Ta kwalla qara me karfi tareda kiran sunan AMMA saida kunnuwansu suka amsa Amo zuwa kirjinsu musamman Ayanah datasan ita Nurat din take kira da Ammah. Saman d
🏠