NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 24 of 146

a ya hargitsa numfashin dasuke shaqa a gurin, Amai sosai kowa yakeyi haddasu Ayanah din saida dukansu suka galabaita amma a hakan baa bude su ba saida safe gari ya waye sosai aka bude su haka aka ringa zubo musu ruwa masu yawan gaske daga sama Ana wankesu kaman dabbobi, Bakinsu suke budewa ruwan na shiga har sukasha sosai kafin ruka zauna ruwan na dukansu da ake zubowa har jikinsu ya wanke tas. Kowa saida jikinsa ya wanke kafin aka fara Fiddosu daya bayan daya daga dakin ana Jere su a fili. Babu me iya miqewa tsaye sosai sbd yunwa da wahalar data gama cinyesu, Hasken sararin samaniya suke kalla yana kashe musu idanuwa sbd duhun da suka fito cikinsa, Kirgasu aka fara yi Ana daya bayan daya Ana raba maza daban mata daban Wanda anan hankalinsu ya tashi tsoro da fargaba suka shigesu Ayanah ta miqa hannu cikin na Abaas da dukkanin jikinsa yake rawa sbd fargaban kada a ganesa, Su duka rawa jikinsu keyi dan Ana gane Abaas mutuwa ce tahau kansa, Qanqame hannunsa Ayanah tayi shima qanqame nata tayi Zuhrah kuwa mannewa tayi a jikinsa itama tana riqe sa suna kokarin hana bayyanar tsoronsu da fargabansu. Shi Kansa Abaas zuciyarsa cikin wani mummunan Hali take na halin da zasu shiga idan asirin hakan ya tonu. Duk Wanda aka Kirga sai an masa sheda a gefen hannunsa da wani karfen wuta. Ana zuwa kansu Nurat aka fara fizgo wa aka kirqa baa tsaya komaiba aka manna mata karfen wuta a gefen hannu Wanda ya sakata qwalla wata gigitacciyar qara tana zubewa a gurin. Cikin firgita Ayanah tayi kanta zata tarota tayi mummunan kife wa kanta na buguwa da katon drum din ruwan dake gurin Wanda ake watsawa duk Wanda ya sume gurin ruwa sbd azaba. Wani Juyawa kanta ya ringa yi sbd bugawan da yayi bata dawo hayyacinta ba taji saukar azababbiyar azaba Akan gefen hannunta Wanda ya sakata somewa a gurin itama. Motsawa Abaas yayi da sauri yana yin kanta itama shima ya kife sbd sarkan dake kafarsa hakama Zuhrah. Anan aka mannawa kowa tasa Shedan cikin azaba suka dunqule suna fidda Wani irin zufa Zuhrah saida ta yanka Wani irin Ihun azabar da bata taba jiba, Abaas duk tsananin azabar dayaji rana ratsa jini,tsokar jiki,qashi da kwakwalwansa kasa ihu yayi sbd Alkwarin da sukaiwa juna na har abada idan basu fita wannan ukubarba bazai taba magana aji sautinsa ba na namiji dan haka daga lokacinda ya aka saiya jinsa zuwa na mace ya koma kurman da baya magana sedai nuni. Wasu irin hawaye masu Zafin radadi a ido da zuci ne suka gangaro masa na tsananin azabar dake ratsashi gashi shi ya kasa somewan. Bulala aka daga me kaurin gaske ta fatar dabba aka zabga masa yayi daurin rintse ido numfashinsa na sarkewa akace ya tashi. Da rarrafe ya koma gefen wainda akaiwa Shedan numfashinsa har lokacin na kokarin yankewa hakama yanason fasa kukan azabar dake ratsashi amma fitan sautin kukansa zai bayyana sautin muryansa datake da dan kauri ta maza dan haka haka yaci gaba da danne azabar yana hadiyewa jikinsa na wata irin muguwan rawa. Zuhrah ma dake Ihun gigitacciyar azaba har lokacin bulala me Zafin datakai azabar wutar aka sakar mata wadda ta sakata sakin qara me rikitarwa Tana rarrafawa gurin Abaas nenam dauki. Ruwa aka watasawa su Ayanah da Sauran bayin da suka some Ana dukansu da Bulala a haukace suke rarrafawa gefe suka fadawa kan yan uwansu. Sakinah ma bata some ba amma tashiga kidima da fitar hayyaci azaba, Nurat duk rashin hankalinta kuka takeyi sosai na azaba Tana nunawa Ayanah hannunta dake tsananin radadi. Hawaye Ayanah ke fitarwa Tana rungumesu cikin azaba da wahala me tsanani suna dauriya da karban wannan sabuwar masifar da suka samu kansu kuma a ciki. Ana gama kirgasu aka fara raba musu Abinci suna karba Ana wucewa dasu dayan dakin da Sauran bayin duka suka ciki sama da daruruwa masu shegen yawa. A yunwace suna jin azaba suka hau cin abincinsu Bayan sun Nemi guri sun rakube a cikin dakin, Ana gama shigo da kowa aka rufe kofofin dakin dake sama take dakin yayi duhu nan take kuma aka fara ihu da kuruwa tareda hayaniyar kokuwan masu karfi da marasa karfi gurin qwacen abinci. Cikin tsananin sabon tsoro su Ayanah suka qanqame juna suna hadewa guri daya take sakinah ta tura Abincinta duka a baki tana hadiyewa tace suka Suyi hakan. Tura abincin sukai gabaki daya a baki suna hadewa cikin azaba da wahala yana yankar maqoshi amma haka suka Hadiye. Kafin kace me gurin anji wa sama da Mutum Hamsin rauni wasu ma a qonuwarsu aka raunatasu. Su kansu Ayanah sunsha duka da shuri na mutane kafin dakin yayi tsit Angama kokawar. Wani Daren ne ya tsala sosai koina yayi tsit duk da basa gane dare bare rana sbd duhun inda suke dan amma shirun ya tabbatar da Daren yayi. Babu Wanda ya samu bacci a cikinsu shiru sukai zuru a jikin juna har lokacin suna maqale, Zafin zazzabi me karfi ne ya fara saukarwa Nurat har tana dan fizga Hakan yasa Ayanah rungumeta a jikinta Tana Shafa bayanta Ahankali, Itama zazzabin take fama dashi sosai amma bata kwantaba sedai jikinta da yayi Wan
🏠