NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 23 of 146

dayanta har abada sbd basa maimaicin zuwa gari komai nasarar da suka samu akansa, Sun dauki shekaru a nahiyar ANJOM din wanda daga karshe sun samu abinda suke samu dan haka kai tsaye daga nan nasararsu da cikar burinsu zai cika sbd wainnan bayin na kaiwa MASARAUTAR BOYEM ne, Masarautar da duk suka samu ta karbi bayinsu to tabbas burinsu ya gama cika na duniya. Masarautar da babu kamarta a iko da tarin mulki da arzikin dayafi na kowace Masarauta tarihi, Idan har BOYEM ta karbi bayinsu to tabbas zasu shiga cikin littafin tarihi da ko Bayan shudewansu zaa San kusra. Jirginsu ahakali ya daga daga nan yana keta wa tareda Kama hanyar ruwan da zasu tsallake sama da nahiya hamsin kafin su isa nahiyar BOYEM. ********* tafiya me nisa akai ta kwana da wuni baa gama fita nahiyar dajin ANJOM ba wadda a qalla sai sunyi kusan sati kafin su fita dajin. A wannan kwana da wunin babu wanda ya farfado a cikinsu Ayanah saida aka kuka wuni tukuna suka fara farfadowa shima sbd ruwan da aketa zuba musu ne masu tsananin sanyi. Suna bude idanuwansu cikin Ayanah ce ta fara bude ido taga inda take cikin wani irin rikitaccen karfin da baifi ma jaririn rago ba ta yunkura tana tashi amma bata iyawa sosai, Sunan Abaas tafara ambata cikin dan karfin datake dashi tana dudduba gefenta dataga mutane barkatai sama da Dari duk wasu a kwance. ‘Zuhrahhh,Abaas,Nurat,Sakinah…….. Haka ta ringa jerosu tana kiransu jikinta na Wani irin mummunan rawar tashin hankali. Zuhrah ce ta fara jiyo Ayanah din da sauri itama t bude idanuwanta tana kwala sunan Ayanah din da dan karfi hankalinta a tashe ko gani batayi ta miqe tana kokarin takawa ta kife sbd kacar dake kafarta. Bude ido tayi a inda ta fadi sai idanuwanta suka sauka Akan Abaas cikin sauri ta cakumosa tana kwala kiran Ayanah. Ayanah gurin ta rarrafo ta iso suka rungume juna da karfin gaske suna jin sassauci. Nurat suka fara kira itama tareda sakina sai kuwa gasu sun gani a guri daya take suka rungume juma kaman Ana partyn ‘yayan aljanu sbd yanda suke hada qasusuwan jikinsu suna rungumewa. Can Kurya suka rakube inda baida haske sbd basason Abaas na bayyana sosai kada tsautsayi yasa a gane duk da bazaka taba kallansa kai tsaye kace ga ba macen bane suka maqale juna a zazzaune kowannesu da kaca a kafansa. Tsoro ne zuciya da gangar jikinsu sbd sun gama tabbatarda sun Riga sun zama bayi, Sun zama bayinda har abada basu yancin rayuwarsu sai yanda akai dasu, Sun rasa sunansu,sun rasa asalinsu rayuwa kuma yanzu sedai wadda aka zaba ko hukuntar musu. Bude kofar qaton dakin da suke akai daga sama kofar take. Kallo wanda ya bude kofar yayi musu tsaf kafin ya fara Jeho musu daurin gayar tuwon alkama da akai da nono. Masu dan karfin cikinsu take suka fara ruguwan Abinci suna tura Bakinsu cikin tsananin yunwa da ficewa hayyaci. Sakinah ma cikin karfin Hali ta yunqura tana wawaso abincin tana jefo musu take jikinsu na rawa suka fara sararsa suna Turawa Bakinsu hannuwansu na rawa. Zuhrah dataji kaman bazata iya tsayawaba yake itama ta rarrafa ta fada cikin wawason tana Turawa bakinta a haukace. Abaas ma fadawa yayi hakama Ayanah da Nurat Take suka zama kaman mahaukata kowa wawa yakeyi yana Turawa bakinsa a haukace. #MAMUH #BEST STORY #BEST LOVE #ROMANCE #ROYALTY HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 12 A cikin Hali na wawason suka ringa Turawa Bakinsu ko taunawa basa yi hadewa kawai sukeyi yana wucewa maqoshinsu da wani irin karfin gaske, Wani irin kuka hanjinsu keyi na samun abinda suka dade basu samuba wato abinci, Danne juna ake yi sosai Ana yiwa juna rauni da hakan suka samu suka cika cikinsu sedai kusan dukkaninsu sun samu rauni dan haka suka rarrafa gefe suka rabe suna dunqulewa sbd tsananin ciwon ciki daya taso musu. A kwance suka wuni ba lafiya sosai sbd ciwon ciki da lafiyarsu da daman babuta yanzu, Tsakiyar dare haka aka sake zuwa aka kawo abincin Ana jeho musu suna wawaso sedai wannan karan ba kowane ya iya tasowa ga abincin ba sbd kusan duka dakin basa da lafiya dan kuwa duka kusan ciwon su daya ne ciwon ciki sbd dade wa me tsayi ba abinci, Zubewa suke son yi kwance su jujjuya ko azabar ciwon cikin zai rage amma dakin babu gurin da kowa zai samu ya kwanta sedai suyi rayuwar zama a cikinsa ko bacci sedai kayi daga Zaune. Dan haka su Ayanah babu Wanda ya iya zuwa cin abincin tsakar Daren se Nurat data fada cikin masu wawan tayita ci da hauka itama sbd rashin cikakken hankali ne kuma duk anji mata ciwo sosai hada bakinta aka fasa yana jini suna kallo babu me iya motsawa saida ta koshi dan kanta ta dawo cikinsu. Kwantar da kansu sukai a kafadun juna suna sake lafewa jikin juna da babu wani sauran taushi na tsoka sai qashi amma su a gurinsu hakan shine mafi nutsuwa da kwanciyan hankali Jinsu a jikin juna, Amai wasunsu suka fara wand
🏠