NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 22 of 146

r kamshin da babu kamarsa, Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba, PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu. 08103155915 ******** Idanuwan Ayanah da suka koma manya sbd gabaki daya naman fuskanta daya tafi babu shi sai qashi zalla Wanda Kana kallanta zaka dauke idonka akanta sbd gabaki dayansu haka suka koma babu Kyan gani sbd babban cin kamannninsu da wanda qwarangwal fata ne da dan abinda baa rasa ba sai Sauran rai dayake jikinsu, Kallan kannenta dake kwance gefenta dukansu kaman gawar dataqi rami takeson yi amma ganinta yayi Raunin da bata iya gane wa sosai dan haka bushashen hannunta ta motsa daqyar yakai kan fuskan Abaas wanda wasu haqoran wahala kawai ta iya Ji a fuskan tasa wainda sune kadai a tsaye sbd babu komai a fuskan tasa idanuwansa sunyi zurfin data kasa iya tantance ramin ido ne ko kuwa ramin bakinsa dan haka ta sauke wani wahalallen Numfashi daqyar tana taba Zuhrah wadda cikinta ya hade da bayanta ta koma halittar da zata iya firgita qananun yaran gata. Hawayen da babu su ne a jikinsu Ayanah ke kokarin hada wa amma babu yanda zasu taho sbd basu da Sauran ruwan komai a jikinsu sbd fitsarinsu ya dade da komawa baqi qirin sukeyinsa alaman babu Sauran ruwan komai a jikinsu. Nurat wadda kowane lokaci ranta zai iya fita jikinta ta sauke hannunta akanta tana Jin kanta ba komai sbd gashin kanta data ringa figewa a kwanakin sbd azaba da rashin cikakken hankali. Rufe idanuwanta tayi tana Rokan Allah ya kawo musu daukin da shine ya kamacesu. Sakina ta dan kalla daqyar bata gane kamanninta tana fatar ko a Aljannah Allah ya hada su guri daya da Sakina sbd ta zama jininsu koda basu hada jinin gaske ba. Zafi garin ya sake dauka sosai da tsananin azaba har rana ta fadi suna kwance har duhun dare yayi, Tsakiyar dare ruwan sama ya sauko wanda da ruwan saman ne daman suke samun sauki a wasu lokutan. Yanzunma ruwan saman ne dayake sauka kansu sosai ya dan saka wasu daga cikinsu motsawa amma ba wanda ya iya tashi har saida ruwan ya dauke da safe tukuna dukkaninsu suka bude idanuwansu amma babu me iya tashi. Zuhrah ce kunnuwanta suka fara jiyo mata takun mutane me dan karfi kadan kadan sai ta Lumshe ido tana fatar abinda take Jin da gaske ne dan kuwa suna buqatan koma masu kashe su ne a yanzu suzo su kashe su tinda a yanzu basuda ma karfin yi da kansu. Hanyar ta qurawa ido daga kwancen datake duk da bata gani sosai gabaki dayansu dishi dishi suke gani ganinsu ya samu matsala wanda kaman illar ganyan da suke ci ne kaman dabbobi. Ayanah ma ahankali ta fara jiyo takun amma bazata iya Juyawa ba bangaren ta kalla sedai Lumshe idanuwan datai na jiran tsammanin koma menene sbd su yanzu kusan tsoro ya cire daga rayukansu. Sauran ma dukansu suna jiyo takun da sautin sa ke amsawa a dajin ta nan bangaren da suke, Sakina ce tafara daga hannu Daqyar tana fatar a hangosu su samu koma wane irin dauki ne. Shiru shiru baa nufo ta bangaren da suke ba har yamma basu Dena jin hayaniya sama sama ba, Duhu ya fara harsun cire rai da tsammani ita Zuhrah da Nurat harma da Abaas duka sun some babu me Sauran numfashi a jikinsu. Sakina da Ayanah ne keda Sauran numfashi amma suma idanuwansu a rufe koma sun bude basa ganin komai se duhu ga kuma dare. Tsakiyar dare sosai Ayanah itama ta some gabaki daya bata numfashi sakina data rage sama sama taji magana akansu Ana cewa ‘Muna buqatan hada wa dasu tinda sunada Sauran rai idan anje can zasu farfado tinda kams yace duk wani dan Adam koma dabba ce idan har tanada rai a tattaro a kawo masa sbd yaune ranar mu tanada qarshe a wannan nahiyar Bayan tsawon shekaru idan muka tafi yau har abada munbar nan tinda a yanzu babu gari anan sedai a tarihi kuma., Daukansu sukai dukansu tsaf suka bar gurin dasu suna dorawa Akan dokuna masu karfi bakyan gani suma sbd abubuwan da duk suka Shafa musu da adon ban tsoro. Suna barin gurin itama sakinah ahankali numfashinta ya tsaya bata sake sanin inda take ba. Mutane sosai suka tattaro a dajin duk sun galabaita wasu kuma sun mutu harsun bushe wasu kuma suna gap da mutuwar wasu kuma macijai sun kashesu wasu kuma sun zare sbd gane ganen Masifa hadda jinnu. Fiyeda Rabin tarin yawan rayukan garin ANJOM sun kashesu dan haka wainda suka mutu sunfi wainda suka Kama sosai dan haka basu wani samu yanda suke so ba Shiyasa ya bada umarnin a sake shiga dajin da zagayensa a kamo wainda suka tsira sbd ya samu tarin bayin da zai siyar wannan Karan su haura daruruwa dan yanada wasu tarin bayin dasuka safaro daga nahiya daban daban a cikin jirginsa me kamar gari guda. Bayan gari ya waye har rana ta keto tukuna suka samu gama hada bayinsu a cikin bangarensu daban can qasan jirgin wanda kowace bawa kafafunsa a daure suke da kaca hannuwansu ne kadai a sake, Su Ayanah da ire irensu da suka gama lalacewa mutuwa kawai suke jira daban aka ware su Ana zuba musu ruwa duk bayan dan lokaci. Yamma sosai kusrawa suka daga daga nahiyar gabaki
🏠