NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 21 of 146

as ne shima yayi kanta da gudu hakama sakinah Ayanah Sakinah kuwa Nurat ta riqe sbd kada itama ta juye ta bisu ta fada ruwan. Har Zuhrah ta fada ruwan Abaas ya Riga Ayanah isa gareta ya riqota tana fizge wa tana kuka me karfi tana rokonsu su tafi. Rungumeta Abaas tayi sosai jikinsa yana bude baki cikin karfin Halin dake zuciyarsa data fara bushewa yace ‘Zuhrah zamu jure,zamu jajirce,zamu tsira,zamu rayu insha Allah zaku ma mu sake amsa sunanmu GHAZ wata ran…. Girgiza kai takeyi tana cewa ‘Aa Aa Abaas bazamu sake amsa sunanmu ba har abada gwara mu tafi dan Allah’ Girgiza mata kai yakeyi shima yana sake daurewa kukan dayake zuwar masa Ayanah ma rungumesu tayi dukansu tana maimaita abinda Abaas ya fada Akan sun rungumi hukuncin ubangiji duk tsananin tsanani zasu jure zasu jajirce zasu rayu a cikin kowane Hali dadi ko wuya. Kuka Zuhrah keyi sosai tana girgiza kai a hakan haka har suka fito ruwan suna samun guri suka zauna suna yin shiru tsawon lokaci kafin suka kalli juna suka sake daukanwa kansu alkwarin jurewa da rungumar kaddara tareda kasancewa da juna sbd duk masifa da munin rayuwan da zasu fuskanta idan suna tare da juna zasu jure dan rabu wa da junansu shine mafi muni da girman kaddarar da suke tinanin zai samesu Wanda gwara musu mutuwa Akan hakan. Fitowa rana ya saka suka miqe suna sake cika cikinsu da ruwan sosai suka bar gurin Bayan sun jiqa kayansu sosai da ruwa har suna tsiyaya ta yanda zasu yi tafiya me tsayi basu azabtu da tsananin Zafin rana da kishirwa ba. Komawa sukai cikin dajin suna kallan hanyar gabas suka miqa suna riqe hannun juna Nurat kuma tana hannun Abaas ya riqe hannunta gam cikin nasa. Wuni sukai suna tafiya har rana ta fadi duhu yayi suka nema guri suka zauna babu me iya numfashin arziki sbd wahalar yunwa da kishirwa. Dukkaninsu sunyi galabaitar da baa magana dan haka tinda suka zube a gurin babu Wanda ya sake motsi kaman matacci har gari ya kuma wayewa yayi haske. Numfashinsu fara Neman gagararsu yakeyi amma a hakan suka tashi suka sake bin hanya suna kasa ko riqe juna wannan Karan, Wuni suka sake yi suna yawo a dajin batareda ma sun San inda suke jefa kafafunsu ba gashi kaman dajin dayake da wani sirri dan baka iya gane gurin fita.. Kwanaki suka dauka suna ragaita a mummunan dajin Wanda zuwa lokacin tini suka fara cin ganyen duk icen da suka samu Wanda yafara maidasu kaman wasu dabbobi, Kamanninsu sun sauya daga mutane zuwa wasu kalar, Fatar su ta koma kaman busashiyar dabinon daya fito cikin qasar sahara, Bakinsu ya bushe ya far fashe jinin dayake fitarwa shi Kansa ya bushe, Wata irin dauda da qasa tareda qazanta ce kala kala a jikinsu Wanda bushewan da sukai qayau yake rage warin dake tashi a jikinsu, Zuwa lokacin dukkaninsu sun gama cire rai daga rayuwa harda Sakina kanta me basu kwarin gwiwa wannan Karan mutuwar take fata da son ta dauke su sbd rayuwa dai ta qare musu a inda ko gawarsu basuda me kalla yayi musu fatan rahama sedai tsutsa su cinye namansu iska ya busar da saura sbd ko dabbar da zata cinye namansu a dajin babu. #MAMUH #BEST STORY #ROYALTY #SLAVERY #BEST LOVE #BOYEM HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 11 *_PRIME SCENT_* 08103155915 Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa? Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents? Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites? Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa? Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT Duniya
🏠