iga da ita masarautar a matsayin baiwa tinda babu Wanda yasan ita wace ce hakama babu damar fadar ita din waye Wanda sakinah batada zabin daya wuce ta tafi da ita a baiwa matiqar tanason kasancewa da ita batareda Ayanah tasan komai Akanta ba bare mutuwar Abaas.
Tausayin Bahar din ya sake cike zuciyarta sbd batasan tayaya zata fara fuskantar rayuwar da zasu tarar din a BOYEM ba musamman da suke ba kowa ba basuda kowane karfin kansu,
Hannun Bahar din na hagu dayake ajiye Akan kafafunta ta zubawa ido Akan lambar 99 dake zane a hannunta Baro Baro tayi baqi sosai Akan farin hannunta daya keda fari sosai sbd zamanta bata Baro komai na mahaifiyarta ba,
Wasu hawaye masu tsananin zafi ne suka gangaro daga idanuwan sakinah dake Haba kukanta zuwa sbd da wuta aka rubuta lambar 99 din wadda take lambar Abaas ta Shedan zama cikakken bawa da kusrawa sukai musu,
Lambar mahaifinta Abaas ce a jikinta zeti da inda akai masa tasa shima a gefen hannu daga sama gurin gwiwan hannun,
Rufe baki da hannunta daya sakinah tayi tana kukanta bayyana sbd Bahar dake shiru a jikinta,
Nata hannun ta kalla inda tata lambar take Baro Baro a jiki 96,
Zuhrah ce 97 sai Nurat 98 tukuna Abaas dinne 99 Ayanaah 100 Wanda haka akai musu su a Jere babu Wanda a cikinsu haryanzu wannan lambar bata jikinsa Wanda da ita zasu mutu,
NUAAB tin da ya tashi yaga mahaifiyarsa da wannan lambar a jikinta da hannunsa ya zanawa Kansa lambar a jikinsa da wuta sbd itace lambar dazai tabbatarwa Abaas shi din ‘dan Ayanah ne dan haka da lambar mahaifiyarsa ya tashi a jikinsa bata taba dauka Abaas shima yayiwa tasa yar lambar sa ba sbd koda baya raye da lambar sa zasu yadda da Bahar ‘yarsa ce.
Kuka sosai Maa sakinah din tafasa tana kasa riqe kanta sbd har abada sunyi rashin da bazasu taba manta radadin sa ba,
Sunyi rashin da shine mafi ciwon rashin da sukai a baya Bayan nan.
BAHAR dake kwance shiru zuciyarta bata iya komai Bayan bugawa ahankali sbd komai ya tsaya mata cak tana jin sautin kukan Maa sakinah yana shiga kunnuwanta a hankali yana ratsata sbd tasan kukan rashin Abaa dinta ne akeyi.
Bude idanuwanta tayi wasu hawaye masu zafi suka gangaro daga cikinsu a sanyaye tana sake Numfashi me sanyi Mara sauti batareda ta motsa daga kwancen datake a jikin matar da bata taba saniba a zahiri Sai a tarihi amma ayanzu da ita kadai zatai rayuwa.
Tafiyar kusan wuni guda sukai kafin jirginsu ya sauka a qasar BOYEM suka fito tareda securities din NUAB din duka da aka hado su dasu shikuma daga shi sai aleey suka koma.
Motocin alfarmar GHAZ ne suka daukesu daga airport zuwa Masarautar BOYEM me tarin abubuwa da tarihi dama Wani tarihin da zaa kafa.
Ko a cikin mota hannun BAHAR din yana cikin na Maa ta riqe cikin nata tana bata dumin dazai Haba gangar jikinta qarasa rasa kanta.
Duk duniya da Aljannar duniyar dake tin daga babbar gate din farko ta masarautar bai shiga idanuwan Bahar ba bare zuciyarta sbd komai na rayuwarta a yanzu rufe yake gap babu kowane irin Sauran shaawa ko burgewa a rayuwa da zai shigeta dan haka idanuwanta a kafe suke kawai a waje tana kallan wajen amma kwata kwata tinaninta baya jikinta ko daya tayi nisa a tinanin rayuwar datai a baya da mahaifinta Wanda a yanzu yana kwance cikin qasa,
Tafiya sukai suka sake wuce gate na biyu har zuwa gate na uku suka shige akai parking motocin bakin hanyar da zata kaisu bangaren cikin gida kai tsaye aka bude musu motocin dukansu su biyun a lokaci daya.
Maa ce ta fara fitowa a natse cikin sanyin jiki ta sauke ajiyan zuciya da Numfashi kafin ta zagayo ta miqa hannu cikin motar ta Kama hannun BAHAR wadda bata motsaba tinda aka bude mata motar ta janyota a hankali cikin kulawa ta fito motar,
batareda ta saki hannunta ba ta jata a natse zuwa ciki suna tafiya babu me karfin jiki.
Duk Taku daya da Bahar ke yi Wani siririn sautin sarkar kafarta ta mahaifiyarta data gada ne yake tashi tareda Wani irin sakar da nutsuwa da saka son juyowa ga duk Wanda sautin ya shiga kunnensa dan hakane duk tayi Taku daya bayin dake jere a hanyar sai sun sauke kansu qasa cikeda girmamawa ga Maa sakinah wadda kowa yasan matsayinta na shaqiqiyar Wishmah kuma jakadiyar bangaren wishmah ta biyu.
Kai tsaye hanyar bangarensu Maa ta nufa da BAHAR wadda har lokacin duk inda Maa ta jata saka kafa kawai takeyi ba Wani kuzari a jikinta.
Isowarsu gap da hanyar data raba bangaren Queen HAILE da bangaren Wishmah Ayanah a daidai wannan lokacin Li’uli ASIM ALMAZZ ya fito bangaren mahaifiyarsa cikin shigar sky blue cashmere mai fitinanniyar tsada qamshinsa yana sauya niimar gurin take dukkanin bayin dake hanyar suka sauke kansu qasa suna tsayawa cak inda suke har saiya wuce.
Maa sakinah dake gap da shigewa da Bahar bata juyowa tayi a natse dan basa girmamawa itama a natse Banda Bahar da batasan me takeyiba daga kafarta tayi tana cigaba da Takawa ba karfi a gangar jikinta ko kadan.
Sautin takunta ne da sarkar kafarta ke fiddawa a natse a gurin daya dauki tsit tamkar babu rai ko daya a gurin sbd bada gi