NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 143 of 146

afiya kafin suka sauka kai tsaye suka sake daukan manyan motocin da suka kaisu har cikin ANJOM ghaz da gawar Abaas GHAZ Wanda a lokacinda Bahar ta farfado rungume gawar tayi ta kasa cewa komai hatta kukan ya kasa zuwar mata idanuwanta ne kadai sukai Wani irin ja. A haka babu bata lokaci akai janaizarsa aka rufesa a cikin masarautar gefen kabarin mahaifinsa da mahaifiyarsa da Ayshaah da akai a cikin masarautar duka dan haka Ana gama janaizarsa suka tattaro suka juyowa tareda Bahar wadda gabaki daya baa San ma Wani halin rayuwarta take ciki ba sbd ko kyaftawa kaman batayi komai nata ya tsaya cak tana rungume a jikin sakinah wadda take jinta har cikin jinin jikinta. Suna isa qasar inda zasubi jirgi anan NUAB ya bada umarnin Maa sakinah da Bahar a wuce BOYEM dasu shikuma zai koma ga Amminsa. Zasu wuce Bayan kowa ya fice kallan Maa sakinah NUAB yayi da manyan idanuwansa da sukai tsananin Laushi ya tattaro dukkanin nutsuwansa ya bude baki yace ‘Maa ina Neman wata alfarma da nakeson kimun alkawarinta a yanzu, Inason kimun alkawarin idan Ammi ta farfado bazaki taba fadawa mata Abaas yabar duniyaba sbd bazata iya dauka ba a yanzu da muke kokarin Neman lafiyanta, Kimun Alkwarin bazata taba sani ba Bazata zan komai ba har sai ranar dana fada mata hakan da kaina, Zuwanmu ghaz da duka abinda ya faru Inason ya zama sirrin da bazai taba fita ba sbd lafiyarta da bazata iya dauka ba, Ki riqe ‘yarsa Amanace ya bar miki amma kada Amminah tasan wace ce ita sbd sanin ita waye din zai saka dole tasan anga Abaas ankuma rasashi dan haka ita din batada kowa sai ke sbd auren da aka daura ba aure ne dazaa tinaba bare qararwa, Maa Inason kiyimin wannan alkawarin’ Numfashi mai tsananin dumi sakinah ta sauke tareda dagowa ta kalli NUAB tukuna ta Gyada kanta alaman tayi wannan Alkwarin har karshen rayuwarta matiqar ba shine ya tado zancenba ta rufesa kenan har ranta ya fita. Numfashi me nutsuwa ya sauke kafin yayi sallama da ita aka wuce dasu airport ba bata lokaci jirginsu ya daga zuwa BOYEM. Suna wucewa da awa hudu suka nasu jirgin yayi daga zuwa ga Amminsa wadda bazai taba dawowa da ita ba matiqar lafiyarta bata daidaitaba. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laoualir *_HAYATEEM_* Mamuhgee 70 A jirgi kwance jikin Maa sakinah Bahar ke kwance idanuwanta da sukai ciki ciki jajir da galabaitar rayuwa da zuciya tareda sarewa da fidda rahama ga rayuwa gabaki daya, Rungumeta cikeda wata irin kulawa da kauna me tsananin gaske da Jinta har jininta Maa sakinah tayi sbd BAHAR itace Abaas da suka rasa har abada sai kuma Aljannah idan Allah yayi sunada rabon haduwa, BAHAR itace jini daya tak ta Abaas dinsu a duniya da idan basu jita har cikin jininsu ba me zasuyi? BAHAR itace jinin Abaas da duniya Ayanah batada kamarsa, Ayanah Allah baiyi tanada rabon sake Dora idanuwanta Akan ‘dan uwanta ba rabin jikinta ba sedai tanada rabon rayuwa da ‘yarsa a matsayin matar ‘danta da bazata saniba sbd ita kanta koda NUAB bai sakata alkawarin kada ta fada mata Abaas ya tafi yabar duniya ya barta ba itama kanta bazata taba iya fada mata mutuwar Abaas ba Wanda Ayanah bazata iya dauka ba dan haka wannan Alkawari ne ta daukanwa kanta itama bazata iya fada matan ba sedai shi NUAB din duk ranar dayaga ya kamatan, BAHAR Amanarta ce a yanzu da zata riqe da rai da rayuwarta tareda bata kariya da dukkanin kauna da kulawan tareda tattalin data rasa tin tasowanta, Insha Allah indai kulawa da nuna kauna da soyayya me tsanani sune suke kawo haske a rayuwar datake cikin duhun kadaici to tabbas zata cikewa Bahar duhun rayuwarta da haske koda kuwa zasu qare a cikin wannan sirrin su mutu matiqar hakan na nufin kariya da samun tsaronta. Numfashi ta sauke ahankali me sanyi da mutuwar jiki tana tina rayuwarsu ta baya da yanda suka Baro ANJOM GHAZ da kuruciyarsu dukkaninsu amma ayau gasu sun manyanta wasu sun rasu sun bar duniya wasu kuma basa tareda su ita kuma gatanan ayau da ‘yar Abaas a hannunta batareda dukansu sunsan hakan kaddara ta tanadar musu ba. Wasu hawaye ne suka ciko idanuwanta tana kallan tata rayuwar da babu komai a cikinta face kaunar jinin GHAZ da bauta musu har qarshen tata rayuwar da batasan Yaushe ne ba amma koma Yaushe ne tana fatar Allah ya dauki rayuwarta itama a cikin aminci da kauna. Shafa fuskar BAHAR data rufe jajayen idanuwanta a hankali tayi tanajin kaunar Bahar din na sake ratsata sbd rayuwarsu a wannan matakin da suke kai yanzu iri daya ce, kaddararsu iri daya ce, Basuda uwa basuda uba basuda Wanda kai tsaye zasu kira nasu Bayan Ayanah dake kwance basu San yaya tata kaddarar zata kasance ba sai NUAB Wanda ayau idan ya rasa Amminsa kila shikenan yabar BOYEM da duk Wanda yake cikinta har abada su kuwa kila duniyar zasu bi sbd rashin Ayanah a BOYEM zamansu a BOYEM din ya qare sbd ita sakinah ba baiwa bace a yanzu hakama Bahar din duk da a yanzu basuda zabin daya wuce a sh
🏠