tan me BOYEM na isa qasar tareda Ayanah wadda jikin yake buqatar ganin likitocin nan da NUAB din ya tanadar mata tini amma basu taho ba dan haka doctors din su buqaci a kawota sbd ta farfado a kusa dasu dan su tabbatar sun bata treatment din dazai hanata rasa hankalinta.
Hakan ya saka NUAB shima kai tsaye tahowa da Abaas din nan dan ganin likitocin,
Manyan motocin ghaz dake qasar ne suka taho har airport suka daukesu shikuma Abaas ambulance ta asibitin ce ta taho dan haka kai tsaye asibiti suka dunguma gabaki dayansu.
Koda aka isa asibiti da Abaas ya farfado sedai zuwa lokacin gabaki dayansu jikinsu yafara mutuwa me tsananin gaske ta yanayinsa dan haka Koda suka iso abinda NUAB ya saka akai musu shine hade Abaas din da Ayanaah a daki daya.
Koda suka iso asibitin babu kowa sbd baa barin relatives shiga kai tsaye dan haka sultan Bayan an kammala komai na admitting Ayanah dashi da tenya tareda securities dinsa da fadawansa barin asibitin sukai zuwa masaukinsu sai kuma idan an nemesu dan haka Sam basuma San isowan su NUAB ba.
Duk wani taimakon gaggawa da doctors zasuyi wa Abaas dayake fidda jini a bakinsa a duk ya yunqura da tarin da bayama fitowa sbd rashin karfi ko kadan daya rage a jikinsa sunyi sunga ma sunbarwa Allah dan haka NUAB shigowa yayi dakin a sanyaye kafafunsa da Wani irin mugun nauyi ya tako ya iso inda yake.
Tsayawa yayi ahankali bakin gadonsa tareda miqa hannunsa a tsananin sanyaye ya Dora Akan na Abaas din Wanda ya fara bude nasa idanuwan da ganinsu ya fara ragewa ya saukesu Akan NUAB din.
Wani irin Numfashi me tattare da sanyin jiki NUAB ya sake tareda daga hannun Abaas din ahankali ya Dora Akan na Amminsa dake kwance har lokacin bata farfado ba ya hada hannuwansu guri daya ya matse musu su da nasa hannuwan biyu yana sunkuyar da Kansa qasa wasu hawaye masu tsananin Zafin gaske suna ciko idanuwansa ya kasa cewa komai….
Kokarin tsayawa Numfashi da bugawan zuciyar Abaas sukeyi sbd abinda ya dirar masa zuciya ya Lumshe idanuwansa ya bude ahankali da qurawa fuskar NUAB dake sunkuye ido batareda ya juyoba yaga fuskar hannun dayake hade da nasaba sbd bazai iyaba.
Aleey ne dayake Bayan NUAB din ya tako a sanyaye shima nasa idanuwan na cike da hawaye masu zafi ya Kama kan Abaas din cikin kulawa da ya juyo dashi setin fuskan Ayanaah dake gefensa Akan nata gadon daban idanuwanta a rufe fuskarta fayau asalin kamanninta babu abinda ya sauya sai manyanta datai….
Wasu hawaye ne masu tsananin dumi suka gangaro daga cikin idanuwan Abaas daya kasa kyaftawa daga kafe idanuwansa dayayi Akan fuskar Ayanah hawayensa na tsanananta gangarowa da Wani irin dumi,
Bude bakinsa yakeson yi ya Ambaci sunanta amma Allah bai basa damar hakan ba dan haka hannunsa ya dan iya motsawa ahankali ya Kama hannunta cikin nasa tareda sauke ajiyan zuciya me sanyi ya rufe idanuwansa ahankali wasu hawayen suka gangarowa ahankali idanuwan na rufe.
Shiru gurin ya sake dauka me tsananin gaske Wanda ya saka NUAB sauke ajiyan zuciyar daya sauka tareda wasu irin hawaye masu Zafin gaske daga idanuwansa da suka kasa riqe dukkanin jarumtarsa.
Aleey ma Juyawa yayi ahankali yana saka hannunsa daya ya rufe idanuwansa dake fidda hawaye sosai har hannuwansa rawa sukeyi kaman yanda na NUAB ke wata irin rawa sbd tabbatarda Ran ABAAS GHAZ ayau yabar jikinsa ya amsa kiran ubangiji.
Sakinah dake bakin kofa rawa jikinta itama ya dauka me tsananin gaske ta saka hannu da karfi ta rufe bakinta tana fasa wani irin kuka Mara sauti zuciyarta na tsananin ciwon me Zafi.
BAHAR da bata fahimci meya ke faruwa ba tana tsaye daga waje idanuwanta jajir ganin irin yanda sakinah ke Wani irin kuka jikinta na jijjiga ya sakata fara takowa ahankali ta sako kai cikin dakin kafafunta na rawa.
Gap da isowa ga mahaifinta data kafe da ido takeyi Aleey ya sake fasa wani irin kuka me sautin daya sakata fahimtar Abaa dinta ya bar duniya yabarta.
Duhu ne ya rufe zuciya da idanuwanta ahankali Wanda ya sakata kafafunta gazawa ta yanke jiki a gurin ta zube jikin NUAB Wanda ya tarota da hannu daya har lokacin Sauran hannunsa daya yana riqe da hannun Abaas da Ayanah.
Doctor shigowa sukai suka fara kashe naurorin dake manne da Abaas din bayan sun rubuta time of death nasa.
Daganan ficewa sukai sukabar fmly da jimamin rashin.
Kuka sosai sakinah takeyi kaman rayuwanta tazo karshe sbd wannan itace kaddarar karshe data qarasa yanke farin cikin dasuke sakaran yi a gaba,
Ayau Abaas ya tafi yabar duniya kaman yanda Nurat da Ayshaah suka tafi sun barsu da tabo da gurbin da bazai taba cikewaba har abada.
NUAB daukan Bahar yayi yakaita Dayan dakin da doctors zasu dubata kafin aleey ma da yasha kuka sosai ya fara shirin komawansu da gawar da bazaa rufeta a nan ba dole zasu koma dashi ghaz acan zaa rufesa.
Zaman qunci da damuwa tareda zullumi me tsanani sukai kafin cikin saa suka samu jirgin dawowa da gawar wadda Washe gari tinda safe suka Juya kuma har lokacin Bahar bata farfado ba haka suka dawo da ita.
Haka suka kuma doguwar t