rsa dan haka mutuwar Ayshaah ta karya duk wani karfin hali da jarumtar dayake da ita ya fadi ciwon da bai taba samun waraka daga garesa ba,
A haka ya rungumi ‘yarsa da sabuwar kaddararsa a cikin qunci da ciwo,
Ya zama uwa kuma uba ga yarsa
Ya zamo aboki da dangin uwa da dangin uba ga yarsa wadda ta taso itama a rayuwarta batasan kowaba Bayan mahaifin nata sai tarin sunayen da kunnuwanta da zuciyarta sun riqesu,
Duhu ne a rayuwarsu da babu ranar shigowan haske a cikinsa,
Qunci ne a rayuwarsu da babu ranar saukar sa sbd duk wani daci da qunci da baqin ciki tareda duhun rayuwar mahaifinta ta dabaibaye tata rayuwar ta shigo ciki tayi zaman da bata taba sanin menene farin ciki ba bare dandanon yanda yake,
Bata taba sanin haske a rayuwa ba bare sanin yaya yake a ruhi,
Bata taba sanin walwala ba bare sanin ya murmushi yake ba a zuci da Fuska dan haka a haka ta taso tin mahaifinta nada karfi da kuzarin kulawa da ita har karfinsa ya qare shima ciwo ya kaisa qasa yana jiyo qamshin mutuwarsa datake gap da iskoshi dan haka tinda ya kwanta ciwo ya sadaukar da Sauran numfashinsa gurin rokon Allah a kowace daqiqa Akan Allah ya kawo masa Ayanah kafin ransa yabar jikinsa sbd yarsa Ayanaah,
Ya roki Allah a kowane Hali Ayanaah take Allah a kawota garesa kafi mutuwarsa sbd goben yarsa ta inganta,
Ya roki Allah ya tsaya Akan rayuwa da duk wani lamarin BAHAR,
BAHAR itace rayuwa da sanyin idaniyarsa da ayanzu yake rokon Allah ya zama gatanta ya tsaya a lamarinta ya bata kariya da tsari daga kowace irin sharri na rayuwa da zata fuskanta.
Tinanin rayuwarsa na sake zuwa gangara babu haske ko daya a rayuwar dazai bar BAHAR dinsa ya saka ya roki Allah dauki ransa tareda ‘yarsa subar duniyar tare sbd zuciyarsa ta kasa riqe tsananin daci da radadin dayake ji na tinanin barinta a duniyar da babu komai a cikinta Bayan zalinci da son zuciya ita kadai ba uwa ba uba ba dangi ko daya sai tarin duhu da qunci.’’
****Wani wahalallen Numfashi ya sauke ahankali daqyar numfashin yana sarqe wa ya dago jajayen idanuwansa Akan NUAB ya sauke yanason bude baki yayi magana amma karfinsa yayi qasa sosai baya iya jan Numfashi da kyau hannuwansa na dan rawa yanason dagawa ya sake Kama hannun NUAB din amma karfin ya qare,
Da sauri Aleey ya da idanuwansa ke zubda ruwa ya qaraso ya mayar masa da oxygen sbd NUAB ganinsa ya dauke tsaf sbd yanayin mummunan Jan tashin hankali da jijjigar zuciya daya shiga hannuwansa rawa sukeyi yana riqe da hannun Abaas din daya gam,
BAHAR da tinda mahaifinta ya fara bada labarin suka iso amma bata shigoba itada sakinah suna tsaye kofar sakinah na Wani irin kuka mara sauti jikinta da kafafunta na rawa,
Ita kuwa jikin bangon gurin ta jingina tana rintse idanuwanta dake Wani irin silili da yajin azabar radadin dayake cikin zuciya da jininta da suka zama rayuwarta datake tamkar fanko,
Shigowa tayi kafafunta na wata irin rawa hawaye masu tsananin zafi da radadin dayake Neman fasa zuciyarta ta iso gurinsa tana zubewa qasa kan kafafunta ta Kama hannunsa daya da hannuwanta biyu dake wata irin rawa ta Dora kanta Akan tafin hannunsa ta fasa wani irin kukan da bata taba fasawa ba a rayuwarta me tsananin tsima zuciya da tafa tsigar jiki tana kasa cewa komai Bayan sake hannunta da nasa datai kanta na kai batasan me takeji ba a yanzu Bayan gajiya da rayuwa,
Bata taba shaawa ko so daya taci gaba da rayuwa ba idan mahaifinta yabar duniya sbd babu abinda zata tsaya ta samu a duniyar,
Mahaifinta shine kadai hasken dayake rayuwarta idan ya tafi rayuwar batada Sauran amfani sbd duhun dake cikinta kasheta zaiyi dan haka bata taba sauya adduarta daga Allah ya dauki ran mahaifinta tareda ita ba.
Ahankali ya bude idanuwansa dake rufewa ya Ambaci sunanta daga Wani irin sautin daya saka kukanta tsananta tana dukan kirjinta dake tsananin ciwon da tinda ta tashi itama dashi ta tashi sbd baqin ciki da qunci kawai.
Aleey ne daya fita ya dawo ciki da sauri tareda isa gefen NUAB cikin nutsuwa da qasa qasa ya sanar dashi komai na tafiya da Abaas din ya zama ready.
Gyada kai NUAB din yayi a hankali yana kallan Abaas da idanuwansa dake cikeda tsananin kaunarsa yana sake riqe hannunsa daya a cikin nasa yace a kira doctors.
Babu bata lokaci doctors suka taho tare akai masa wata allura a cikin drip tareda Sauran abubuwan da suka kamata aka bada umarnin kowa a fice.
BAHAR da NUAB ne kadai basu fice ba hakama babu Wanda ya iya sakin hannunsa a cikinsu saima Wani irin kukanta sanyayyan sauti dake tashi tana sake cusa fuskarta cikin tafin hannunsa daya sake baya motsi ko kadan.
Fitowa akai dashi aka saka ambulance suka fada motoci suma kai tsaye aka wuce airport dashi inda komai yake a shirye.
Private jet suka shiga Bayan dan dogon shirye shiryen dabai dauki lokaci ba Wanda akaiwa kowa tinda suka iso da Abaas din dan haka kai tsaye jirginsu ya daga gabaki dayansu.
#MAMUH
09033181070
[09/12, 11:22 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
69
Bayan doguwar tafiya Greece suka isa inda suna sauka jirgin sul