tabawa sbd yanason ya Nemi inda zai ajiyeta dan bata rayuwar kwanciyan hankali da nutsuwa amma abin ya gagara.
Ahankali suka fara Gagarin rayuwa a qasashe gurin Neman su Ayanah Wanda zuwa yanzu rayuwarsa ta qarasa macewa gabaki daya sbd ciwon wahala da azabar rayuwa da qunci da suka taru suka rufar masa dan haka ya samu qasa me dan nutsuwa yace zai siya mata gida y ajiyeta tayi rayuwarta ta huta da binsa gararin duniya kada ta qare rayuwarta kamar tasa ta mutu a banza.
Kasa yadda da hakan Ayshaah tayi sbd bazata taba iya rayuwa ita kadai babu sa ba sbd a yanzu shine t Rabin jikinta rayuwarta,
Shine kadai hasken dayake rayuwarta shi kadaine Wanda rayuwarta take dashi dan haka ta shirya mutuwa a gurin Gagarin duniya tareda shi,
Ta shirya rayuwa da mutuwa tareda shi ko an inane ko awa ce qasane zata iya zama dashi.
Da wannan suka fada qasar BOYEM Wanda Sam babu ta yanda zaa barsu su shigeta kusan watan su uku anan babu damar shiga qasar dan haka suka juya suka bar qasar.
A border ta farko da baa shiga qasar BOYEM aka daura musu aure sbd hanasu gurin zama da akai koina garin sbd basada aure dan haka suka daura aure Wanda har cikin zuciya da ransu suna tsananin son junansu hakama sun shirya rayuwa da mutuwa a tare,
Aurensu ne ya kawo wata yar nutsuwar rayuwa a rayuwarsu data cikin tsananin duhu da qunci tareda kadaici,
Kusanci da sabuwar shaquwa da kauna tareda so me tsananin gaske sukewa juna suna sake Jin karfin gwiwan fuskantar rayuwa.
Bayan wata uku suka bar BOYEM sakamakon cikin daya bayyana a jikin Ayshaah,
Cikin ya taho mata da rashin lafiya sosai dan haka tafara wata irin rama taba kofewa alaman jininta yana yin qasa dan haka Abaas ya sadaukar da rayuwarsa da kudirin sa dan bata nutsuwan rayuwan daya kamata kodan abinda zasu haifa kafa suyita yawon duniya dashi dan haka suka juya inda suka fito,
Shima kirgen garuruwan da suka Baro a baya tsawon shekaru lokacin da aka dauko su daga garinsu ya fara yi dan komawa qasar sa garinsa gidansu da iyalinsa sbd matiqar Ayanah tana raye to tabbas yasan zata je nemansa a cikin duniya kokuma anan gidan mafarinsu dan haka zai jirata daga yanzu har ranar da Allah zai dauki rayuwarsa.
*****tafiyar watanni sukai nai cikeda wahala da ukuba da tsinkewan zuciya ga yanayin ayshahh kafin Allah ya iso dasu dajin garinsu daya sha matiqar wuyar gaske kafin ya gane hakama dukiyarsu tayi qasa dan haka Koda suka iso ANJOM GHAZ cikin Ayshaah ya tsufa yakai wata takwas.
A garin ANJOM babu mutane sosai sbd garin ya Riga ya mutu dan haka babu wata daula da tatttalin arziki kaman baya amma akwai kwanciyan hankali dan haka babu wahala ko tashin hankali aka karbesu tinda ansan waye shi hakama duk da shekaru sunja kamanninsa basu sauyaba.
Babu kowa a fadar mahaifinsa dan haka Sauran dukiyar daya taho da ita ya bayar aka dan yi gyaran dazai yiyu suka shiga batareda tsoro ba suka zauna tareda kokarin daga ANJOM.
Kokarin dayazo dashi da qwazo ya saka jamaar garin samun kuzari da qwazonsu suma ya dawo take garin ya fara komawa ANJOM dinsa na baya a bisa mulkin ABAAS GHAZ din.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 11:19 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
68
ANJOM GHAZ ta dawo ANJOM dinta duk bazata taba komawa ANJOM din baya ba amma Abaas yayi iya kokarinsa ya sake kafata da dukiyarsa da karfinsa da lafiyarsa datake qasa sosai amma ya tsayu ya kasa barin ciwon kirji da zuciyar dake damunsa yakai sa qasa,
Ayshaah ma ta samu rayuwar kwanciyan hankali da nutsuwar da Abaas ke fatan ya bata sedai yanayinta itama sai ahankali lafiyarta tayi qasa sosai musamman da cikinta harya wuce watannin haihuwa bata haihuba dan haka aka ringa kawo mata addua da maganin al’adarsu tana sha,
Kauna da soyayya me girma tareda wata irin tsafta da nutsuwa take tsakanin Ayshahh da Abaas Wanda kusan duk ANJOM ansan irin son dayake mata da irin yanda ita kuma ya kere mata komai da duniyarta harma da rayuwarta dan haka yanayin jikinta ya saka duk Wanda yake garin mutuwar jikin halinda Abaas yake ciki Akan rashin lafiyarta.
Cikinta na cika wata goma sha daya cif ta Wanda yayi daidai da wata su uku cikin na hudu da dawowa ANJOM da samun rayuwa me nutsuwa Bayan shekarun gararin duniya da gwagwarmaya a qasashe cikin rashin gata hakama shekaru biyar cif da rasuwarta mahaifinta ta haifi ‘yarta,yar Abaas,jinin ghaz,hasken idaniyar mahaifinta a duniya wadda tana haihuwarta a idanuwanta kadai ta kalleta ko a hannunta Allah bai bata ikon daukanta ba tabar duniyar ta tafiyarta tabi mahaifinta Wanda bata taba Dena kewa da radadin rashinsa ba a rayuwarta tabar masoyinta da ‘yarta a duniyar da basuda kowa sai junansu a yanzu.
ABAAS GHAZ wannan shine farkon bude dukkanin kofofin karfin ciwon dayake cin tasa zuciyar wadda ta kasa dauka da jure rashin matarsa wadda itace take riqe da zuciyarsa dake a zube tin acan baya ta rashin yan uwansa a rayuwa