gaske tana kokarin dawowa ya dago idanuwansa jajir yace
‘Ban Aminta ki tsaya ba bare dawowa gareni ki tafi Allah zai zama gatanku insha Allah,
Burina burin Ammanku shine ku tsira dan haka Ayanah ku tafi ku cika mana wannan burin ku rayu,
Duk rintsi ku hada kai karku rabu da juna’
Sake turata yayi sa karfi tana qara riqosa amma ina jini sosai yake fita a kirjinsa harma da bakin sa take kafafunsa suka kasa daukansa ya durqushe a gurin ta kira sunansa da karfi tana kokarin durqusawa Kaman daga sama taji bayanta an riqeta.
Cikin tsananin azaba ya dago idanuwansa ya kalli Asamah wadda bata hayyacinta sbd kukan baqin ciki da danasanin datake ciki tareda fatan tayi mummunan mutuwan data jawa rayukan dake ANJOM.
Daqyar ya bude baki jini na fita sosai yana kallan Asamah yace
‘Ki tseratar dasu,
Karki bari kowannesu ya tsaya bare dawowa ANJOM ‘
Janta Asamah tayi tana Hana su Zuhrah dawowa suka fara ihu ganin halinda Abaansu ya shiga ransa na kokarin barin kirjinsa sbd wani irin jinin dake fita bakinsa.
Kaman daga sama sai ganin Mutum biyu sukai akansa ba Imani a tare suka soka wuqa biyu a wuyansa idanuwansa na kan yayansa dake Ihun gaske suna Neman zarewa sbd mummunan tashin hankalin sheda mutuwan mahaifinsu akan idonsu.
Asamah cigaba da turasu tayi suka kutsa dajin suna tsananta gudu hannun Ayanah yana cikin na Abaas hakama Nurat da zuhrah suma hannuwansu na riqe dana juna.
Biyo su akai wannan Karan an Dena harbin da alama da rai ake sonsu.
Kuka sosai sukeyi suna tsananta gudunsu Banda Ayanah datake Jin zuciyarta na kokarin nema bugawa hakama idanuwanta basa ganin komai jefa kafa kawai takeyi.
Dukkaninsu sun kasa yadda a awannin da basu wuce uku ba sun rasa iyayensu duka cikin dare daya a Masifa da mummunan kaddara daya,
Neman sarewa sukeyi amma Sam Asamah ta kasa Bari saima hanya data sauya musu sbd an kusa kamosu dan haka cikin wani irin qazantaccen rami ta turasu suka shige suka boye tareda sakina wadda take riqe da Zuhrah a yanzu.
Suna shigewa Asamah ce ta saka hannuwanta ta toshe bakin Nurat da Abaas ita kuma sakina ta rufe na Zuhrah sbd yanda suke kuka suna wata irin jijjiga.
Ayanah ta kasa komai ta koma tamkar marasa hankali da kwakwalwa kwata kwata dan haka batace komai bare kukan Wanda ya kasa fitowa tsabar muni da girman tashin hankalin datake ciki.
Suna Ji kusrawan na wucewa da gudu da karfi suna ihu me ban tsoro amma basu motsa ba har saida suka Ji sun gama wuce kafin Asamah ta zare hannunta a Bakinsu Sai a lokacin Nurat ta fasa wani irin kukan daya saka Idon sakina fara zubar hawaye
Asamah kuwa kukan itama ta fasa me tsananin ciwo tana rungume Zuhrah dake jijjiga kaman me wani ciwo.
Rintse idanuwa Ayanah tayi tareda sunkuyar da kai tana fasa kuka mai tsima zuciya da girgiza kowa.
Babu Wanda yace komai a cikinsu dukkaninsu kuka ne sukeyi mara dadin Ji bame rarrashin wani sbd kaddarar tayi musu nauyin da zuciyarsu take kasa dauka,
Ayanah hannu ta Dora Akan kirjinta tana duka kukanta na sake tsananta sbd kirjinta ya toshe Jin takeyi kaman ta mutu tabi iyayenta.
Har asuba tayi gari ya fara haske suna cikin ramin idanuwansu sunyi wani irin kumbura da ja babu me iya dogon motsi sbd mutuwa da j