NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 138 of 146

aka dagowa yayi idanuwansa jajir da wasu irin hawaye a cikinsu sbd bazai taba yadda ya sake shiga hannun kusrawaba koda zai rasa ransa gurin cetan Kansa da ayshahh da boukar sbd har abada bayason su dandana baqin cikin daya dandana shi da yan uwansa musamman ayshaahh datake mace, A baya rauni da rashin karfi ya sakasa zamowa nace yana kallo baida abin yi Bayan kuka aka tarwatsa rayuwar yan uwansa aka kashe masa Nurat dan haka wannan Karan a yanzu daya zama namiji ya zabi mutuwa Akan tafiya wannnan mummunan rayuwar. Takobi da adda boukar ya basa yana kallan Zafin dayake bayyana a cikin idanuwansa yace ‘Ka tabbatarda Ka bawa Kanka da Ayshaah kariya’ Wucewa gaba boukar yayi da dan gudunsa na fuskantar komai ai kuwa yana fita take fadan ya dawo Kansa amma dayake yanada nasa karfin sosai haka ya ringa fadan dasu. Shima Abaas baisan lokacinda ya fado cikin fadan ba idanuwansa a rufe komai na abinda ya faru dasu kawai yake gani dan haka kusrawa kawai yake gani a idanuwansa ya ringa fadan bayaji baya gani. Fin karfinsu fadan ya fara yi sbd kusan duk bayin biyar an kashesu hakama suma anfara musu rauni dan haka boukar da jini sosai yake fita jikinsa kallan Abaas yayi cikin tsananin galabaitar daya fara yace ‘Ka tafi Ka dauki ayshahh da jaka na nan gefen gadonta na ajiye ku bar nan kuje garin neruji ku tsallaka ruwa zuwa kiyoje ku jirani anan,Ka tafi da sauri…. Kasan Juyawa Abaas din yayi yana kallan boukar din tamkar yanda Abaa dinsu yayi musu hakan ce yake sake faruwa Ayau din dan haka zaiyi musu boukar damqi hannunsa da karfi yace ‘Idan ban taho ba zuwa gobe to bana duniya Ka dauki Ayshaah Ka tafi da ita inda zata samu rayuwa me kyau ita amana ce gareka duniya da lahira, Hakama idan ranar goben ta fadi ban bayyana gareku ba na ‘yantaka Nurat, Ka zama gatan ‘yata ka zama gatanta da dukiyarta’ Cikin tsananin baqin ciki da radadin zuciya a Karan farko Abaas ya bude bakinsa Bayan shekaru ya furta ‘ABAAS GHAZ’ Kallansa boukar yayi da Wani irin yanayin karyewan zuciya batareda yaddarsa akansa ta girgiza ba ya bude baki idanuwansa na yin jajir yace ‘Abaas ghaz ina fatar Ka zamo gatan ‘yata da bata kariya da rayuwarka har karshen rayuwarta ko taka’ Tura Abaas din yayi da karfi zuwa cikin gida shikuma yana sake bude kofar fita daga bangarensu zuwa bangaren da hatsin zuwa da kuma zuwa kofar ficewa da tini suka shigo. Da sauri Abaas ya juya yana jin zuciyarsa na yanka da Wani irin yanayin da yake sakasa jin kaman bazai iya tafiya yabar boukar ba amma kuma matiqar zasu bawa ayshahh kariya su tseratar da rayuwarta dole ya tafi. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 11:19 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 67 Kai tsaye dakinta ya isa da gudun gaske ya banka kofar bai tsaya komaiba ya dauki jakar da boukar yace ya miqa hannu ya damqi hannunta datake tsaye ta miqe cikin tsananin tsoro da fargaba. Janta yayi da karfi suka fito tsakar gidan Wanda yake hayaqi da ci da wuta take ta riqe hannunsa da karfi cikin tsananin tsoro da tashin hankali tace ‘Meya ke faruwa, Ina Abbu?? Baice mata komaiba ya jata da saurin suka bi ta kofar baya da babu Wanda ya sani sai iya su zasu fice ta qwace hannunta zata koma da gudu tana kwala kiran sunan mahaifinta. Riqota Abaas din yayi da karfin gaske yana kokarin sake tafiya da ita ta fara fizgewa tana Ihun daya sakasa rufe mata baki da karfi yana kallanta cikin duhun hanyar ya sanar da ita abinda yake faruwa da kuma abinda mahaifinta ya ce akan zuwansu su jirasa. Kasa iya barin mahaifinta tayi ta fara Wani irin kuka da rawar jiki tana kokarin kwacewa sbd tasan mahaifinta bazai tsiraba kashesa zasuyi batada kowa bazata iya rayuwa ba mahaifinta ba,bazata iya shiga duniyar da tasan bazata taba sake dawowa ba anan ko kabarin mahaifinta ta ziyarta ba dan haka gwara ta mutu a guri daya da mahaifinta. Rufe mata baki gabaki daya Abaas yayi zuciyarsa na jin abinda take ji sbd shima ya shiga irin wannan mummunan yanayin harma nasa ya zarce nata nesa ba kusa ba dan haka daukanta yayi cak yabar gurin da ita yana sake rufe mata baki da duka karfinsa. Gudu yakeyi da ita a cikin tsananin duhu da shukokin da sun kusa finsu tsayi dan haka cikinsu kawai yake jefa Kafafunsa da ko takarmi babu yanaji qayoyi manya da qananu suna sukarsa da abubuwa masu laifin da harma sun fasa kafafunsa jini suke fiddawa amma bai tsayaba gudun yakeyi sosai sbd yana jiyo hayaniyar biyosu da akai Wanda hakan ya tabbatar musu su duka biyun da boukar ya fadi. Kuka Ayshaah takeyi sosai dukkinanin jikinta na sakewa a jikinsa tanajin duniyarta ta gama kifewa da lalacewa kenan har abada dan haka bazata taba dawowa daidaiba. Shi Kansa jin yakeyi jikinsa na Neman mutuwa da wannan mummunan baqin cikin na rasa Wanda yakeda mahimmanci a rayuwarsa datake a rube Bayan rasa iyaye da yan uwansa amma ganin a yanzu shin
🏠