NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 136 of 146

a sukuma suka siyarwa wasu marasa imani shi da niyar zasu je dashi su huta a tinaninsu mace ce gashi yaqi cewa komai dan Alkawari ne bazaiyi magana ba da yayiwa Ayanah harsai rayuwarsa ta kubuta dan haka bazai taba karya wannan Alkwarin ba. Akan kudi ba masu yawa ba aka siyar dashi take wainda suka siyesa suka tafi dashi zuwa gurin hutawarsu, Koda suka tafi dashi mummunan abinda suka fara aikata masa shine dukansa suka ringa yi har saida ya Dena motsi yayi mummunan illatar da baida Sauran amfani a duniya tukuna suka yaga Kayan jikinsa gabaki daya Akan zasu masa fyade sai suka tarar dashi namiji ne dan haka baqin cikinsu ya tsananta take suka qarasa kashesa da dukan tsiya suka tattara shi suka Kai bakin ruwan suka yar suka Tafiyarsu. A wannan Daren gap da asuba wasu suka tsincesa suma maimakon su taimaka masa sai suka duba suka ga yanada Sauran rai dan haka suka wankesa tas suka sake saka masa Kayan mata sbd ganinsa da yan kunne a kunne harma da abin hanci, Gari na fara wayewa kafin rana ta fito suka kallaba suka siyarwa Wani matafiyi shi a matsayin baiwa mace sbd anfison bayi mata a Kasuwan yanzu Shiyasa suka fi tsada. Matafiyin raya siya bawan asalin balaraben shemali ne Wanda yayiwa ‘yarsa kwalli daya alkawarin siya mata baiwa mace da zata zama tamkar kawarta sbd debe mata kewan rashin uwa da kawayen datake fama dashi dan haka har zai tafi ya samu baiwar duk da taji jiki tana cikin wani mummunan Hali sosai amma hakanan bai damu ba ya siye sbd jirgin ruwa zaibi zuwa komawa qasar sa bazai jira gari ya waye a fara cin kasuwan bayi ba. Hakanan ya karbi Abaas ya wuce dashi Bayan ya biya kudin jirginsa na ruwa ya biya kudin kayansa da bawansa Wanda zaa saka guri daya da Kayan sbd haka akeyi bayi da kaya guri daya ake sakasa kaman wasu dabbobi dan haka babu komawa jirginsu yabar qasar. Tafiyar wuni da kwana daya sukai suka isa qasar wadda take cikeda nata kalar arzikin, Boukar shine sunansa hakama shi din mai arziki ne sosai a gurin yan uwansa dama garin nasu Wanda yake na qasar larabawan shemali ne, ‘Yarsa tak daya a duniya wadda mahaifiyarta bata jima da rasuwa ba tabarta da kadai cin daya saka ya siyo mata baiwa sbd ta fita daga kewan datake cikinta, Baya tareda yan uwansa sosai sbd akwai Hassada da qyashi sosai a tsakaninsu dashi, Duniyarsa ta tsone musu ido sosai, Tsananin hanyar da zasu rabasa da dukiyar suke nema dan haka basa rabarsa ko kadan sbd rayuwarsa suke dako dan hakanne ma yake tsananin kiyayewa Akan yarsa da ita kadai garesa bai hadata da komai, AYSHAHH ne sunan yar tasa wadda take balarabiya gabanta da bayanta sbd uwa da ubanta duka yan asalin shemali dinne dan haka da kyau da gata da nutsuwa ta taso tareda gatan da kusan a garin babu Wanda ya keda irinsa. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 66 Koda boukar ya kawowa yarsa ayshahh baiwa tayi farin ciki sosai sbd tana tsananin buqatar Abokiyar debe kewa dan haka tayi kaunaci kyautar baiwar musamman ganin kusan kansu daya kila ma ba Wani sosai baiwar ta girmeta ba dan haka taimaka mata sukai sosai da magani da ruwa da Sauran abubuwan da abinci ta samu a cikin kwana biyu ta dawo daidai hayyacinta ya dawo Wanda a hakan bata tana magana ba dan haka ran boukar ya baci ganin Ashe Murna aka siyar masa dan haka yayi alkawarin sake siyo mata wata idan yayi tafiyar kasuwancinsa. Sosai Abaas yayi jinya tukuna ya dawo tsaye a kafafunsa ya fara aikin bautar da aka siyosa yayi batareda har lokacin ya fara magana ba, Bauta yakeyi a gidan da rayuwar masu gidan dan kuwa kaf hidima da wahalar aikin gidan shine yakeyi Bayan hutawa babu abinda sukeyi se idan boukar ya fita ke yake Zaunawa da Ayshaah dan debe mata kewa kuma har lokacin basu taba sanin shi namiji bane a haka a hakan harya dauki kusan shekara bakwai dasu yana bauta sun samu Wani irin sabo dashi sosai gaske sbd kaf rayuwarsu babu kowa a cikinta baya su kadai uba da ‘ya sai maqota da yan uwan mahaifiyarta dake zuwa akai akai dan haka shine mutum na farko da suka sabo dashi fiyeda kowa da komai duk da har lokacin shi din kurma ne hakama bai taba fita daga qunci da tsananin baqin cikin da zuciyarsa take ciki ba amma daidai gwagwado sbd babu mugunta ba azaba ba tozarwa ba hantara ba qyama a tsakaninsu dashi ya saka suka samu matsayi a zuciyarsa musamman ayshaah dayake kallo kaman yar uwarsa sbd sosai take kaunarsa. Shi Kansa boukar sosai yake da nutsuwa da kwanciyan hankali idan yabarsu tare sbd ya yadda da yarsa zata samu samu kulawa tamkar yananan koma fiye a gurin Nurat kaman yanda ya fada musu sunansa kenan a rubuce da larabci. Bayan sabo shekarun suna dake nitsawa shaquwa me karfi ta shigesu sbd a yanzu ya koma tamkar Wani bangare ja rayuwarsu dan haka a yanzu tamkar ahalin mutum uku suke jinsu duk da haryanzu har gobe shi bawan su ne amma akwai kauna da kulawa tsakanin
🏠