NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 135 of 146

reda shi. Haka ta wuni a dakin batareda kowa Yazo ba aka bata damarta sbd jikin nasa a yanda suke gani ba Sauran hope dan haka aka barta ta kasance dashi a lokutan da suka rage. Kwana biyu da zuwansu asibitin bai farfado ba se a ranar na ukun tsakiyar dare kusan karfe biyu da mintina ya farfado dan haka cikin gaggawa asibitin suka kira waya suka sanar da NUAB Wanda a cikin Daren ya sako babbar jacket din fendi Akan Kayan jikinsa ya fito da hular sanyi Akan gashinsa suka nufo asibitin. Suna isowa Kai tsaye dakin suka isa wanda doctors biyu ne da nurses hudu a dakin yana shigowa dukkaninsu suka jiyo suka kallesa cikeda tausayawa. Takowa yakeyi a hankali zuciyarsa na tsinkewa a Karan farko dayake Jin tsananin tsoro na saka kafafunsa rawa da nauyin daya sakasa kafe Abaas din da idanuwansa da sukai ja yana Jin wata irin kauna me karfin gaske da tsananin so da fatar ya tashi daga ciwon sbd ya basa rayuwa me kyau da nutsuwa da kwanciyan hankali da kaunar da batada sirki. Abaas dayake kwancen kamanninsa sun gama sauyawa daga dukkanin lafiyar da babu ko daya a jiki da jininsa bude idanuwansa Yayi ahankali cikin yanayin daya saka kafafun NUAB sake sarewa yaji kirjinsa yayi nauyin daya sakasa qarasowa da kyar, Akan NUAB Abaas ya kafe idanuwansa masu tsananin Laushi yana Jin dukkanin baqin cikinsa da damuwarsa na yayewa a lokutan sa na karshen rayuwa dan haka Lumshe idanuwansa yayi tareda motsawa a tsananin sanyi ya bude tafin hannunsa na dama da NUAB din yake tsaye, Zaunawa NUAB yayi a natse tareda Dora hannunsa ahankali Akan nasa din tareda kamawa ya riqe cikin nasa cikeda kulawa da kauna mara sirki. Numfashi mara karfi Abaas ya sauke cikin rashin karfi ko kadan ya saka hannunsa daya ya zare oxygen dinsa Wanda NUAB yayi saurin riqe hannunsa shi da aleey a lokaci daya amma Abaas din ya girgiza musu Kai tareda bude baki cikin karfin Hali yace ‘Inason Ayanah tasan labarina a bakina kafin barina duniya idan Allah yasa na tashi zan fada mata da bakina idan ban tashi ba Ka gabatar mata da rayuwar da Abaas dinta yayi sbd kada tarihinmu ya zama ba qarasashe ba a tarihin duniya.’ Aleey baya yaja ahankali tareda fidda iPad dinsa da babu inda yake taba zuwa bada ita ba koman emergency kuwa, Recording na video ya saka tareda tahowa ya ajiyeta a setin gadon Abaas din Wanda hannunsa yake cikin na NUAB yana jinsa har ransa sbd Jin yakeyi kaman hannun Ayanarsa ce a cikin hannunsa hade dan haka baida Sauran regret na rayuwa. Juyawa aleey yayi waje inda securities suke yace suje su dauko BAHAR sbd ganawa da mahaifinta. Yana dawowa wayar sa ya fice da ita dan fara hada tafiyar da zasuyi da asubar komai tsanani suna buqatan dagawa da Abaas din tinda ya farfado sbd likitocin su na gaggawa da suka hada suna can suna jiran isowansu. Kafin Abaas ya fara cewa komai sake qanqame hannun NUAB yayi da dan karfin daya rage masa mara kuzari ko kadan dan ya bude baki ahankali ya furta ‘AYANAH BAHAR’ dago jajayen idanuwa NUAB yayi ya kalli Abaas din Wanda tin daga qasan zuciyarsa sunan ‘yar tasa ya fito harya manta da ita sbd aleey ne yake tsaye Akan kulawa dasu. Ajiyan zuciya me sanyi Abaas din ya sauke kafin ya Lumshe idanuwansa a hankali sbd rayuwar komai ta farko data fara dawo masa radadi da baqin cikin na budewa yana famawa Wanda gashinan dashi zai mutu yabar duniya. Asalin tarihinsu da rayuwar da sukai a qarqashin kulawa da kaunar iyayensu ya fara jerowa ahankali cikin nutsuwa da Wani irin ratsa zuciya da yanda kusrawa suka tarwatsa rayuwarsu suka sauya tarihinsu da kaddararsu zuwa mara dadi da kyau, Yanda rayuwarsu ta sauya ne daga ranar da suka bar garinsu zuwa tafiya qangin bauta yafara zayyana wa Dayan bayan daya daki daki batareda ya boye ko kalma daya zuciyarsa na Kina da radadi me tsananin ciwo da baqin ciki, Yana zuwa daidai inda aka lalata rayuwar Nurat wadda akai komai a cikin kunnuwansu qanqame hannun NUAB yayi cikin wani irin mafi zazzafan baqin cikin da har yanzu sautin kukanta bai fita kunnuwansa da zuciyarsa ba shiru ya dan yi jikinsa na rawa idanuwansa na rufewa cikin azaba… Rawa jikin NUAB yakeyi sosai yana wata irin jijjiga a hankali ya qanqame hannun Abaas din da karfin daya saka Abaas bude idanuwansa yana sauke su Akan NUAB din Wanda yake hango Wani irin radadi da baqin ciki me tsananin karfi a cikin idanuwansa, Rintse ido shima ya sake yi yana cigaba da bada labarin mutuwarta da abinda yaci gaba da biyowa Bayan nan har zuwa inda aka rabasa da yan uwansa, Cigaba yayi da cewa, ‘Bayan an rabasa da yan uwansa anan kasuwar kwana yayi a daure a Wani ice tamkar dabba haka ya kuma wuni a rana babu ruwa babu Inuwa har saida karfinsa ya qare ya dunqule guri daya yana fita hayyacinsa sbd azabar rana da kishirwan dayake fatar ta dauki ransa dan kuwa bazai iya rayuwa babu su Ayanah a tareda shi ba dan haka duk duka da azabar da aka ringa gana masa Qin cin komai ko ruwan da aka basa yayi sbd yunwa yake sonta kashe sa ya huta. Ganin taurin kansa ya sak
🏠