NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 134 of 146

AZ sukai Wanda kila shikenan sun barsa a rayuwarsu, Sakinah tsirawa dajin ido tayi bata kyaftawa zuciyarta na narkewa fiyeda a baya ANJOM shine garin da har su mutu bazasu Dena marmarin dawowa su qarasa rayuwa a cikinsa ba. Bahar ma dake Zaune gaban mahaifinta hannunta ta saka ahankali cikin nasa ta Kama tareda hade tafin hannuwansu tana Lumshe idanuwanta da sukai jajir wasu hawaye masu dumin cikinsu suka gangaro mata Sarkin fada ma kusa da ita su kadai a dakin dayake Sarkin fada na fada mata ‘dan Ayanar mahaifinta ne Yazo ga mahaifin nata dan basa lafiya. Babu kowane irin farin ciki ko Jin dadi ko daya daya sauka ga zuciyarta na abinda Sarkin fadan ya fada sbd babu Sauran kowace kauna ko soyayyar datake Jin zuciyarta nada damar yiwa kowa sbd bata tashi da kowa ba a rayuwarta daga ita sai mahaifinta tayi rayuwa, Rayuwa da zuciyarta a kulle take ga rayuwa da kowa a cikinta sbd kadaici da quncin data taso a cikinsa na rayuwa babu uwar data haifeta wadda ta rasu a ranar data kawota duniya hakama tasowa ta rayu a cikin duhun gidan da babu kowa a cikinsa sai ita da mahaifinta Wanda shima tinda ta bude ido duniya take kallansa cikin qunci da tarin baqin cikin daya hanasa lafiya har yau da rayuwarsa take cikin tsakiyar rayuwa ko mutuwa dan haka zuciyarta da rayuwarta a mace suke ta yanda basuda komai ciki da zata iya farin ciki dan haka rufe idanuwanta tayi ahankali wasu Zafafan hawayen na sake gangaro mata tana fadar idan lokacin mahaifinta ne yayi Allah ya dauki ransu a tare subar duniyar a tare. Tafiya me tsayi sukai kafin suka isa bakin bodar qasar babu bata lokaci aka fito dashi zuwa ambulance da already ankira tana jiransu dan haka take ambulance din ta daukesa tareda Bahar din a cikinta da Sarkin fada su kuma Sauran motocin suka shiga a guje akai asibiti dashi. Suna isa aka karbesa da gaggawa akai ciki dashi suka bisu jikin kowa a mace musamman BAHAR wadda zuwa lokacin ko kuka bata iyayi sbd babu alamar sauki ko kadan a lamarin nasa. A inda ake jira suka zazzauna Banda NUAB da aleey wainda aka kaisu guri kebantacce dan jiran dan hakan har lokacin babu Wanda yayi noticing juna a tsakaninsu. Maa sakinah ce Zaune a gefen Bahar din wadda kanta yake qasa ta dunqule hannayenta guri daya idanuwanta jajir. Hannu Maa sakinah ta Dora a hankali kan na Bahar din tareda kallanta cikeda kulawa da kauna me karfin gaske tareda tausayi itama idanuwanta jajir batareda tace komaiba, Itama Bahar din bata dagoba sedai rintse idanuwanta datai hannuwanta na tsananta rawa Maa Sakinta ta riqe su cikin nata gam alaman bata sassauci. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 65 Zaman da kowace daqiqa take tafiya da tsananin bugun zuciyarsu da zullumi tareda tsoro me tsanani da fargaba sukai na kusan wuni guri kafin aka samu numfashinsa ya dan dawo daidai da oxygen hakama jini aka daura masa Wanda yake na NUAB dinne da kansa aka diba Bayan ya hana Yaransa bada nasu nashin yakeson a sakawa Abaas sbd a shirye yake ga bada jininsa gabak daya idan zaa buqata hakan dan Abaas ya rayu sbd kila Amminsa zata iya juriya da karfin zuciyar rashin sa amma bazata iya daurewa rashin Abaas ba. Idanuwan Bahar sunyi munin da suka sauya kamanninta koina nata yayi jajir sbd kuka da damuwan datake gap da buga zuciyarta da babu kowa a ciki sai BAA din, Sakinah dik da tana cikin mummunan tashin hankalin itama amma ta daure ta fidda karfin halinta a matsayi na uwa dake gurin ta bawa BAHAR dukkanin kulawa da kaunar datake buqata a daidai wannan lokacin Wanda hakan ne ya dan rage zarewan da yarinyar ke kokarin yi a Zaune gurin. Shi kansa NUAB babu Wanda ya gansa a cikinsu dan hakane ma basusan jininsa ne aka sakawa Abaas dinba, Aleey kadai suka gani shima abinci lafiyayye kusan Kala biyar ya saka aka kawo musu Wanda babu Wanda suka saka a Bakinsu Duk yanda Maa sakinah tayi Bahar taci Sam ko sakewa babu a tsakaninsu da zata iya ma cusa kanta dole taci ba dan haka bata ci komaiba fatarta mahaifinta ya tashi ya samu lafiyar da zasu koma inda suka fito suci gaba da rayuwarsu su qarasata a tare su biyu kadai. Dare na yi haka aka daukesu aka kaisu masaukin da yanda Bahar taga rana haka taga Daren batareda ta rintsa ba a Zaune take har asuba idanuwanta sunyi mummunan kumburan da kanta ke tsananin ciwon da ko gani sosai batayi amma Sam ba sassaucin datake ji a zuciyarta. Karfe 8 na safe Aleey ya aiko mota aka maidasu asibiti inda ta tarar da mahaifinta yanda ta barsa tamkar babu rai a jikinsa yayi fayau yayi Wani irin haske ya qarasa bushewa sosai babu Sauran kowace albarkar jiki a tattare dashi. A sanyaye babu kuzari ko kadan a jikinta ta zame gefensa ta zauna idanuwanta na cikowa da hawayen da basu gangaroba ta saka hannunta cikin nasa ta sake hadewa ta qanqamesa cikin wani irin sanyi dayake tabbatarda kaunar datake masa a shirye take da mutuwa ta
🏠