NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 132 of 146

ngo babu komai da aka sauya,babu komai da aka gyara tin asalin yanda gini d tsarin gidan haka yake haryanzu babu cigaba ako ina dan haka koina a mace yake iya inda suke rayuwa a cikin masarautar yake gyare. A kofar bakin dakin Ayanah ta tsaya cak Wanda yake fes a gyare koina asalin qamshin jinin sarautar GHAZ na tashi yana fitowa daga dakin na flowern Ahlighazania Wanda gabaki daya ahalin shine qamshin da suke amfani dashi tin farko dan haka suka kasance kamshinsu daya me shiga rai da sanyi tareda wata irin nutsuwan kwanciyan hankali da kashe jiki. Lumshe idanuwa sakinah tayi tana Jin bugun zuciyarta na tsananta da Wani irin mutuwan jiki da baqin tareda quncin rashin kasancewan su a rayuwa daya koda duka suka Haifa iyalansu, Idan har mahaifiyar BAHAR bata raye yaya Abaas yayi dawainiyar kulawa da tarbiyantar da ita shi kadai babu dan uwansa ko daya a tattare da ita? Idan yanzu Allah ya kaddara ciwonsa bana tashi bane yaya zasu fuskanci BAHAR dik a matsayin dangin mahaifinta daya rasa shekaru? Yaya zata iya rayuwa a cikinsu batareda tasansu ba ko sabo dasu? Tayaya ma zata iya rayuwan nan babu uwa babu ubanta da shine gatanta, Zata dandana ‘daci da quncin da iyayenta suka dandana na rashin iyaye da tafiya Wani guri rayuwan da batama san yaya zatayi ba, Shi kansa auren da ake daura mata a yanzu basusan a mizanin wace kaddara zai hau ba sbd abu ne da babusa a tarihin GHAZ kuma bazai taba zamaba ga asalin jinin Wanda yake kan mulki kuma Wanda yake magaji bazai taba auren wadda ba jinin BOYEM ba haramun ne ma ga jinin da mahaifinsa ya mulki BOYEM kuma shima Ana sakaran ya mulki BOYEM auren wadda ba jinin BOYEM ba. Tayaya zasu fuskanci wannan auren da zaa kulla yanzu a masarautar da Kai tsaye mutuwarsu ce hukuncin wannan auren da akai indai ya isa gaban sultan da Masarautar BOYEM. Bude idanuwanta tayi ahankali jajir dasu sun kumbura ta miqa hannunta a hankali kofar dakin ta tura a natse bakinta na budewa da disashiyar murya tai sallama tana saka Kai daidai nan kunnuwanta suka jiyo mata sautin FATIHAR da aka shafa ta DAURA AUREN NUAB ALMAZZ BOYEM DA AYANAH BAHAR ABAAS GHAZ Wanda ya ratsa kunnuwan duk Wanda yake cikin masarautar GHAZ din Banda BAHAR wadda bacci takeyi a kishingide idanuwanta a rufe sbd kanta dayake tsananin ciwon damuwan dake zagaye da rayuwarta Akan ciwon BAA dinta Wanda shine gatanta,rayuwarta,hasken idaniya da rayuwarta. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 64 Rufe baki da hannuwa Maa sakinah tayi a lokacinda ta tabbatarda auren ya dauru Wanda hadarine zalla a cikinsa da zai iya raba mutane da yawa da rayuwarsu sbd sun aikatawa masarautar BOYEM gagarumin haram din da zai tono sirri Ka da dama amma koma menene ita saina shirye take da bawa Auren kariya da lafiyarta da rayuwarta har karshen rayuwarta da ba lallai tanada yawa a nan gaba ba. BAHAR da motsi ya sakata bude manyan fararen idanuwanta da suke sak na mahaifiyarta asalin balarabiyar SHEMALI masu daukan hankali da saka baki da jikinka mutuwa sbd Wani irin sirrin kwarjini da nitsatsen kyau dayake cikinsu, Akan sakinah dake kofar dakin tana shigowa ta sauke idanuwan a natse tana qarasa budesu gabaki daya akanta tareda tashi Zaune cikin nutsuwa da jinin mulkin GHAZ dake yawo yawo a jikinta batareda ta bude baki ba tayi magana sbd koma wanene shine yakeda damar bude baki ya sanar da ita shi waye meya kawosa dakinta dan haka kafafunta ta ziro a hankali cikin nutsuwa ta saka a cikin Takarmin dayake bakin gadonta tana kafe idanuwanta Akan sakinah dake qarasa shigowa tana bayyana fa hasken dakin na wutar gargajiya dake dakin take ta bayyana a idanuwan BAHAR din wadda Kai tsaye kukane idanuwanta suka fara cin karo dashi matar na yi Wanda ya saka bugun zuciyarta tsayawa cak sbd babu abinda Yazo ranta sai mahaifinta dan haka ahankali cikin wani irin slow ta maida kallanta kan kofar shigowa dakinta tana miqewa tsaye ta nufi kofa mayafin dake rufe da lafiyayyan dogon gashinta na zamewa bata tsaya ba ta rabe Maa sakina jikinta na wata irin rawa ta fice da gudu tana nufar dakinsa idanuwanta na tara ruwan mummunan tashin hankali da tsoron dayake jijjiga rayuwarta dan kuwa bazata iya rayuwar da babu Baa dinta a ciki ba,mutuwa zatayi idan ta rasashi a rayuwarta sbd shine ginshikin rayuwarta da duka rayuwarta take tangale da soyayyarsa. Saka Kai tayi a dakin tana jefa idonta Akan gadonsa dayake kwance taga babu kowa akai, Wani irin sarawa kanta yayi ta juyo da gudu dukkanin jikinta na wata irin rawar data saka kafafunta suka yanke zata fadi sakinah data biyota da sauri tana hawaye tayi saurin tareta jikinta tana kokarin rungumeta amma ta kasa tsayawa ta nufi fada da gudu idanuwanta basa gani sbd tsananin fita hayyacin data fara ta bude baki da Wani irin sautin daya ratsa kunnuwan duk Wanda yake masarautar cikin wani irin tada tsigar jiki tace
🏠