NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 131 of 146

ude baki NUAB yayi da wata muryan data saka tsigar jikin Sarkin fada tashi gabaki daya yana sake Jin shakkar NUAB na shigarsa yace ‘Ku Bari na ceta rayuwarsa nayi muku alkawarin bawa rayuwarsa data ‘yarsa kariyar da matiqar ina raye sun wuce kowane matsayin da zasu fuskanci kunci ko rashin gata tako ina…….. Girgiza Kai Sarkin gida yayi yana kasa kallan NUAB din Wanda hatta fuskarsa tayi jajir jikinsa rawa yakeyi. Aleey da zufa ke gangarowa umarni me Zafi ya bada Wanda ya saka aka taqa bindigogin zaa fasa kan Sarkin gida NUAB ya daga hannu daidai nan Maa Sakinta ta zube qasa itama tana fasa sabon kukan daya saka kowa juyowa ya kalleta ahankali da jajayen idanuwa Banda NUAB daya rintse ido hannuwansa dake dauke da Abaas suna wata irin rawar dake bayyanarda halinda zuciyarsa take ciki. Cikin tsananin kukan data jima batai irinsa ba sakinah ta bude baki tareda dagowa ta kalli NUAB tace ‘NUAB Ka aureta kodan cika alkawarin daka daukanwa mahaifiyarka zaka kawo mata Abaas, Ka aureta sbd cetan rayuwar Abaas da zuciyoyi da dama bazasu iya jurewaba idan aka rasashi, Alkwari ne da aka dauka anan cikin masarautar GHAZ tin kafin sanin yaya kaddarar zata taho ba a tsakanin mahaifiyarka da Abaas Wanda idan Ka cikasa Ayau anan inda aka dauki alkawarin zaka cike musu burinsu ne da shi kadai ya rage a tsakaninsu sbd ko baka kaiwa Ayanaah Abaas ba Ka Kai mata auren ‘yarsa dake hannunka Ka cike mata gurbin da Abaas zai bar mata sbd ‘yar Abaas tamkar Abaas dinne a gurinta….. Tsit gurin yayi kowa na shiga sabon mummunan yanayi Banda NUAB da already yake cikinsa idanuwansa a rufe danan. Kallansa su aleey sukai dukkaninsu cikin shock da tashin hankali da firgici sbd babu kowane irin tarihin shigowan nace rayuwar LEUL daya tsara, Bai taba son kowace mace ba sbd baima taba sakasu a tsarin rayuwarsa ba,Amminsa ita kadaice wadda yayi Alkwarin ta ishesa rayuwarsa, Mata uku ne a rayuwarsa kuma su kadai ne wainda zaiyi rayuwa dasu baya buqatan kowace irin mace Bayan ukun nan iyayensa dan haka aleey yasan babu ta yanda zaayi mace ta shigo rayuwar LEUL dan haka dagowa yayi ya dawo da kallansa kan Sarkin fada Wanda jikinsa ya mace da maganganun sakinah da shima sune yake tsaye akansa. ‘A daura mun auren da ita ni zan aureta indai hakan ne kadai zai saka ku Bari mu tafi dashi da ita din…….. Kallansa Sarkin fada yayi da sauri cikin tsananin mamaki da fargaba kafin ya maida kallansa kan sakinah wadda ta fasa sabon kuka tukuna ya maida kallansa kan NUAB Wanda ya bude idanuwansa a hankali ya Dora Akan Sarkin fada din batareda ya kalli kowa ba ya saka hannunsa cikin aljihun wandon kakin dake jikinsa na shigowa daji ya ciro Wani kakkauran awarwaron zinari daya me kaurin gaske dayake dauke da sunan mahaifiyarsa da Abaas din Wanda yake nata ne shine ya bata kyautarsa da hannunsa ya qera sa ya saka sunanta dana Abaas din a yanzu dazai taho yaje har dakinta ya dauko sa sbd nunawa Abaas shedan shi dan Ayanah ne ya miqawa aleey dayake mutuwar tsaye cikeda rudewa da mamaki Abaas shima ya miqawa securities yana dawowa gurin NUAB Wanda ya saka hannunsa daya ya kamo hannun Sarkin gida ya saka masa zinarin ya bude baki da sauti me Kai tsaye da tarin tsananin son cikar Buri daya wato tafiya da Abaas dan ganin likitocin gaggawa. ‘Sadakina,a daura auren a yanzu anan a wannan daqiqar bana buqatar qarin mintina ko kadan batareda an daura ba.’ Jikin Sarkin fada rawa ya dauka sbd shakka da firgici amma hakanan ya tattaro karfin Hali da jarumta ya juya da sauri yace a kira masa Sauran masu dan matsayi a fadar da gaggawa. Aleey matsowa yayi zeyi magana sbd sanin NUAB zaiyi auren ne batareda kaunar ko taba shaawar hakan ba dan haka shi a shirye yake da auren koma yaya take yarinyar sbd LEUL kuma zai rayu da ita komai tsananin yanda lamarin zai kasance dan haka bude baki yayi zaiyi magana, Daga masa hannu NUAB yayi a natse cikin yanayinsa da baya son magana ko daya sbd koina fuskarsa yayi jajir hadda hannuwansa ma duka sunyi jajir. Sauran securities ficewa sukai da Abaas cikin gaggawa zuwa jirginsu na bakin ruwa da akwai Dr a cikinsa dan fara basa taimakon gaggawa kafin a gama daura auren. Sakinah barin gurin tayi ta fito kafafunta da tsananin nauyi ta nufi dakin Ayanaah na baya wainda a yanxu yake na BAHAR din kaman yanda aka fada tana kallan koina a hankali zuciyarta na yanka kuka mara sauti na taho mata hawaye na gudu suna tsiyaya a fuskarta kowane memory na rayuwar da sukai a kowane lungu da sako na gidan suna dawo mata. Inda daidai Baa ya shimfide gawar Ammah a lokacinda sukai ido biyu da gawar tata idanuwanta suka sauka ta rintse idanuwanta tana dafe kirjinta dake Wani irin ciwo hawayenta na tsananta gudu. Fara zagayawa dakunan kowa da aka Bari tana fashewa da sabon kukan baqin ciki me tsanani da kewan rayuwar da suka bari anan wadda koda basuyi arzikin da suke dashi a BOYEM ba ko kadan nan din yafi musu farin ciki da nutsuwa tareda kwanciyar hankali. Koina ya mutu ta zama tamkar ka
🏠