ke rikicewa yakeyi dan haka ba bata lokaci Aleey ya fita ya fidda wayar sa ya saka kiran Sauran yaran yace a kawo Maa sakinah yanzu.
A lokacinda aka iso da Maa sakinah Abaas cikin tsananin ciwo da rashin karfi ya zayyanewa NUAB labarinsu tas Wanda baida dadin ji me tarin qunci da baqin ciki.
Nasa labarin yake kokarin Dora masa Maa Sakinah ta shiga kafafunta na Takawa ahankali cikin sanyi da rawar zuciyar dake gap da bugawa.
Suna kallan juna Abaas ya fashe da Wani irin kukan daya saka dakin yin tsit gashin jikinsu na tashi.
Itama Maa sakinah zubewa tayi qasa tana fasa kuka a gabansa koina jikinta na rawa tana kiran sunansa da sauti me ratsa jiki.
Bude baki yakeson yi ya Ambaci sunata da tambayar yan uwansa amma karfinsa yayi qasa sosai dan haka ta rarrafo da sauri tana bude bakinta dayake rawa cikin sautin daya sake saka gurin daukan tsit ta fara fada masa dukkanin halinda suka shiga har zuwa halinda ake ciki yanzu da Ayanah dake tsananin so da buqatarsa a rayuwarta.
Magana zeyi harshensa ya fara kokarin karyewa dan haka take aleey yace securities su daukesa Ayi gaggawar tafiya dashi.
Riqe hannun sakinah Abaas din yayi da karfin dayake na barin duniya yana kallanta daqyar ya iya furta ‘yata jinina AYANAH BAHAR….
Kasa qarasawa yayi jikinsa na sakewa gabaki daya.
Gaggawar fita dashi suke kokarin yi sbd har lokacin akwai Sauran rai a jikinsa
Sarkin gida na ganin hakan buga tsalle ya tare kofa tareda kiran fadawa yana cewa kada a Bari su fita koina da Shiguba da yarsa har sai ancika burinsa na auren yarsa Wanda hakan zai basu tabbacin kariyarta Bayan tabar nan sbd igiyoyin auren sa zasu tabbatar musu da zaa iya riqe amanarta matsayinta na ‘yar shugabansu hakama basuda tabbacin Ayanah din da gaske tana raye amma tinda ga ‘danta a gabansu bazaa tafi dasu ba saiya aureta koda Abaas ya rasu kafin akai to ta samu gatan zama Inuwar aure.
#MAMUH
HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070
Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee
63
Da Wani irin yanayi me ‘dacin gaske da jajayen ido NUAB da aleey suka dago dukkaninsu suka kalli Sarkin fadar Wanda ya sake tsayawa Akan maganarsa ba tsoro sbd wannan shine gatan da adalcin da zasu wa ‘yar shigabansu jinin GHAZ data rage a duniya a idanuwansu,
Su dai bazasu bi su ba hakama bazasu Hana a tafi da Sugabansu ba dan nema masa lafiya sbd yana tsananin buqatarta amma kuma basuda tabbacin zai rayu ko bazai rayu ba a yanda sukaga jikin nasa yayi nisa dan haka gwara ‘dan Ayanah kaman yanda ya fada ya auri Bahar ‘Dinsu a gaban idonsu ta yanda koda Allah bai tashi kafafun Abaas ba sunsan zaman aure zatayi a cikinsu ba zaman garari ba dan haka tsoro ya cire a zuciyarsa matiqar ba auren BAHAR zasuyiba gwara abar musu shigabansu ya cika a gabansu su dauki amanar yarsa wannan shine tsayuwarsu matiqar ba hakan ba kuma sedai a kashe su a tafi da Abaas da BAHAR Bayan ransu.
Kuka Sosai Maa sakinah takeyi tana Jin zuciyarta kaman zata fashe sbd idan Abaas yabar duniya Zuhrah ce kadai ta ragewa Ayanah wadda tafi tsananin kauna da son Abaas a rayuwarta fiyeda komai,
Tayaya Ayanah zata iya jure wannan rashin?
Sake qanqame hannun Abaas din sakinah tayi dake cikin hannunta tana rintse ido da sabon kuka me tsananin rasa zuciya.
Aleey da ransa ya gama baci gashi ba lokaci da gaggawar gaske suke son tafiya da Wanda shine rayuwar Ammmi,
Kallan Securities yayi da idanuwansa jajir yace su kawar da kowa har sai sun fice dashi.
Sarkin fada na Jin hakan ya sake tare hanyar tareda fidda wata irin mahaukaciyar wuqa a jikinsa me munin da zata zata aikaka lahira ba bata lokaci.
Wuqar sa ba komai bace a gurinsu sbd sunada wainda sukaci uwarta da ubanta a jikinsu Wanda zata katse jijiya take kafin kyaftawar ido kawai banbanci tasa dafin gaske ne a cikinta da shine zai kasheka bama kaifinta ba kila.
Bindiga suka daga cikeda rashin tausayi suka seta Sarkin fadar tareda Yaransa da suka taho suka zagaye kofar dakin da makamai masu hadari a hannunsa.
NUAB da jikinsa ke wata irin fizga sbd tsananin tsoron rasa Abaas Wanda shi kansa bayajin zai iya Hadiye radadin rashin sa sbd tsananin kaunar da son dayake masa tin kafin ya gansa sbd shine mutum daya da Amminsa tafi so a duniyarta da rayuwarta fiyeda kowa,
Ko shi kansa data Haifa baya iya gane tsakanin shi da Abaas wane tafi tsananin so dan haka da kaunar Abaas shima ya tashi a ransa hakama da ita zai mutu dan haka bazai taba iya barin ya mutu sakamakon rashin likita ba indai ba Allah ya Riga yayi anan zai cika din ba lokacinsa yayi kenan ba dan haka dagowa yayi da jajayen idanuwansa da sukai mummunan ja kamar ma hadda hawaye a cikinsu ya kalli Sarkin fada Wanda yaja baya kadan sbd tsananin kwarjini da shakkar NUAB din data dakesa zuciya da kafafu amma duk da hakan bayajin zai iya ja da baya Akan abinda ya fada sedai Ayau ya rasa ransa gurin tabbatarda gyara goben BAHAR.
B