na ciki Zaune yana jiran bayani daga aleey Wanda yake sake kallan iPad din hannunsa da kyau sbd tabbas yaga gari.
Wasu mahaukatan bikes dake shiga daji suka fidda daga jirgin ruwan suka hau tareda kutsawa cikin dajin a shirye da bindigoginsu da wasu manyan wuqaqe masu shegen hadari.
Tafiya sukeyi suna kutsawa kafin sukai tafi me Nisan gaske basu isa garin ba sai yamma lis wanda ya saka sakinah yanke jiki ta fadi tama Dora kafarta a qasar garin ANJOM GHAZ kenan.
Cikin kulawa da bada umarni yace a koma da ita jirgi taga doctor ya dubata abarshi daga shi se aleey su fara ganin lafiyar garin ma tukuna.
Sauran yaran da bikes din tareda Maa sakina Juyawa sukai suka koma.
Kafarsa ta dama ya fara dorawa a cikin garin ANJOM GHAZ daya saka tsigar jikinsa tashi sbd ganin yanda garin ya zama tamkar ba garin da mutane suke rayuwa a cikinsaba sbd duk tsawon shekarun garin bai dawo daidai ba sun rasa niima da tarin albarkar garin nasu.
Akwai mutane sosai da gidaje sosai da kasuwanni a garin amma ba kamar baya ba sbd kusan kowa na garin yasan kowa tinda ba yawa sosai.
Ganin baqi a garin ya saka gabaki daya mutane shiga tsoro da tashin hankali dan haka Kowa ya fara silalewa yana komawa gidansa ya shige ya rufe tinda dai shugaban garin nasu baida lafiyar dazai basu kariya,
Fiyeda shekaru tara yana kwance yana jinyar da ba lallai ya tashi ba sbd yayi mummunan nisa.
Gidan shugaban garin Aleey ya nema a taimaka a nuna musu babu musu kuwa Wani ya kaisu har kofar gidan asalin sarautar GHAZ.
Fadawane suke gadin masarautar amma tsirarru Wanda yake nuni da Masarautar batada karfi ko Kwata kwata tinda garinma duka ba Wani karfi bare Ayi mulki me karfi.
A fada suka zauna nan Sarkin fada ya shigo yana kallansu tareda zubawa NUAB idanunwata kaman zasu gado sbd ganin kammanninsa da jinin GHAZ dayake Neman shafewa daga Yauma kila sbd jikin Shugaba yau yayi tsananin da sai Allah.
Kwarjinin NUAB ya saka shine ya gaidasu yana musu Barka da zuwa maimakon su su gaidasa sbd shine kila me mulkin GHAZ anan gaba.
Aleey cikin nutsuwa shima ya dan gaidasa da yarensu Wanda NUAB yakeji sosai sbd mahaifiyarsa dake masa tin yana yaro hakama Maa sakinah shikuwa ya kullafa saida ya iya yaran shikuwa aleey baya wasa saida ya iya shima sbd uban gidan nasa da idan ta Kama.
Kaman daga Sam Kai tsaye NUAB yace
‘Menene sunan shugaban jinin GHAZ daya rage a yanzu???
Da mamaki Sarkin fada yace
‘ABAAS GHAZ sai ‘yarsa qwalli daya tak AYANAH BAHAR GHAZ sune suka rage jinin GHAZ a duniya…
Wani bawa ne ya fado fadar da sauri yana zubewa qasa yace
‘Sarkin fada jikin Maigirma yana sake tsananta kana buqatan zuwa.
Miqewa Sarkin fada yayi yana barin gurin a rikice Wanda ya saka Kai tsaye NUAB miqewa yabi bayansa sbd kowane Hali Abaas din Amminsa yake yanason ganinsa.
Sarkin fada na saka Kai dakin NUAB ma yana sakawa idanuwansa suka sauka Akan fuskar datake sak da sak data mahaifiyarsa.
Abaas dake aman jini ahankali dagowa yayi idanuwansa na sauka Akan NUAB take ya dauke wuya komai nasa na kokarin tsayawa cak yayi baya zai zube
Taku biyu NUAB yayi ta tarosa jikinsa yana Jin dukkanin nauyin dake zuciyarsa yana qaruwa da ganin sanyin idaniyar mahaifiyarsa a wannan halin.
Feso Wani jini Abaas yai da karfi cikin azabar dayake kasa riqewa NUAB ya katse azabar ciwonsa da cewa
‘NUAB ALMAZZ ‘da ga AYANAH GHAZ……
Rintse idanuwana Abaas yayi cikin wani azababben yanka daya ratsa zuciyansa data gama yanke kauna da yan uwansa har abada musamman yanzu dayake kan gadon mutuwarsa,
Riqosa NUAB yayi cikin rashin bata lokaci sbd kafin komai yana Abaas din na buqatar likita da gaggawa,
Girgiza Kai Abaas yayi cikin wani mummunan rashin kuzari da ciwon da baida sassauci ke kadan ya damqi hannun NUAAB din da karfin gaske yana jan Numfashi da qyar yace
‘Ayanah tana raye???
Cikin sauri NUAB din ya Gyada masa Kai tareda bude baki yace
‘Kana buqatan likitan dazai duba lafiyar Ka da gaggawa daga baya duk zamuyi magana amma Ka sani Amminah tana raye,
Tana son ganinka itama kafin tabar duniya dan haka kada Ka tafi Kabarta zuciyarta bazata iya daukaba sbd kaine hasken zuciyarta da idaniyar Abaas ghaz.
Girgiza Kai Abaas ya sake yi yanajin kaman bazai iya ko minti dayaba a duniya dan haka koma yayane Allah yayi masa rahama ne tinda Sauran ransa daya kawo masa dan Ayanaah zai cika a hannunsa Bayan burinsa na hada jini da Ayanarsa ya cika Akan gadon mutuwarsa.
Sake qanqame hannun NUAB yayi yana bude baki daqyar yace
‘Ka cikawa mahaifiyarka Dani burin da muka tashi dashi na hada zuria da juna Ayau cikin Daren yau na mutu da nutsuwar na bada ‘yata daya tak ga jinin Ayanah……
Wani kallan rashin fahimta NUAB yayi masa yaja kallan aleey yace Ayi gaggawar daukansa dan tafiya dashi ga likita.
Abaas zamewa yayi yana sake dan girgiza Kai daqyar yace
‘Lokaci na yayi Allah ya yanke ganawata da Ayanah bazan Kai koinaba zan bar duniya,
Kokarin daukansa aleey yakeyi amma jikin sa