NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 128 of 146

Dagowa yayi ya kalli LEUL BOYEM da idanuwansa da suke cike da Basira da wata irin kwakwalwa me hasko komai Akan lissafi da nazari, Shima NUAB din gama kallan bayanin da duka suke a rubuce da map din Bayan duk bayanan dayayi masa da baki kuma, Dagowa yayi ya kalli Aleey ya bude baki a natse yace ‘Meye karshen tinani da bayaninka ya hada? Ajiye laptop din hannunsa yayi tareda kallan NUAB din cikeda girmamawa yace ‘Tinda ta ruwa suka iso qasar to dole bangare biyu ne Hagu da dama Wanda yake kudu da arewa kenan dan haka a cikin biyun zaa fara da daya maana a faro binciken daga inda suka fito tin farko ANJOM GHAZ kenan dan kuwa akwai yiyuwar tinda Abaas namijine to tabbas a tsawon shekarun nan indai ya samu yancinsa to tabbas ya koma gida dan sake ginawa da farfado da sunan GHAZ da bazai taba barin ya shafe ba Bayan ya nema yan uwansa be samu ba kenan, Dan haka inaga a fara daga can din Kai tsaye sbd tabbatarwa idan bai komaba Sai a Nemi Sauran qasashen. Kallansa NUAB ya dago a natse yayi cikin yadda da kowane bayanin aleey a koda Yaushe Akan komai sbd baya taba hada lissafin da bai qure kwakwalwansa akansa ba dan haka Numfashi me sanyi ya sake tareda dagowa yace ‘A gobe Inason a shirya tafiya zuwa qasar buharaqs din Wanda a cikinta ANJOM GHAZ take insha Allah. Gyada Kai aleey yayi sbd yanada tabbacin insha Allah haka bayanin yake ba tantanma indai Abaas na raye yana saka ran ya koma dan farfado da GHAZ matiqar shi namijin jinin GHAZ ne dan ‘dan halak ko baida zarra bazai yadda sarautar gidansu ta fadi ta shafe a tarihi ba. Juyawa yayi ya bar gurin yana daga wayar sa dan fara shirin tafiyar tasu da bazata wuce kwana biyu su wuce ba. Bayan barin aleey shiru NUAAB yayi yana Jin Wani irin yanayi na rashin sanin tinanin Kamawa Akan me haduwan mahaifiyarsa da Abaas zata kasance hakama a yanzu da mahaifiyarsa take cikin halin da bazata iya basa labarin cikakken tarihinta ba a bakin Abaas dayake jininta yakeson jin asalin tarihin komai na Amminsa. ******* Cikin kwana biyu aleey bai hutawa ba sbd bai taba wasa da duk abinda yake na LEUL ba dan haka shirin tafiyar ya tsaya tsayin daka saida ya tabbatarda ya hadata a cikin sati guda Bayan ya gama tanadar da komai na tafiyar wadda ya hadata hadda Maa sakinah da zata kaisu har cikin ANJOM GHAZ Bayan sun isa qasar kenan. Tenya batasan da tafiyar ba sai ranar da zaa wuce kai tsaye NUAB ya sanar dasu dan haka jiki a mace da tsananin zullumin daya saka jinin Maa sakinah mummunan hawa sbd komawa inda komai ya faro. Karfe Dayan rana motocinsu a Jere suka fice daga Masarautun zuwa airport Wanda motocinsu na zuwa gate din qarshe daidai nan motocin da suka dauko mai girma YUNAR BOYEM daga airport tareda ‘yarsa LEYLAH YUNAR BOYEM ‘yar amaryarsa ZUHRAH GHAZ BOYEM wadda ya kawo a matsayin tukuicin dawowan MAGAJI LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM ya basa aurenta a matsayinta na jinin BOYEM itama. Ficewa motocinsa sukai tareda securities dinsa Bayan motocin mai girma YUNAR din sun shigo sukuma batareda kowannensu yaga junaba musamman LEYLAH YUNAR data gama mutuwa akansa tin kafin ganinsa a zahiri sbd kallo daya datai masa a hoton labarai ta shirya zama ko mistress dinsa ce ba matarsa ba dan haka wannan tukuicin da mahaifinta ya badata na aure shine abu mafi farin ciki da girma na rayuwarta dan haka batada baqin cikin dawowan su Masarauta da zama. Su kuwa suna isa airport Kai tsaye jirginsu ya daga yabar qasar. Tafiyar awanni masu yawa sukai kafin suka isa qasar bhariqs din wadda saida suka kwana a wata qasar kafin suka sake hawan jirgi suka isa. Tinda suka iso daga shi kansa NUAAB din Wanda baisan kaddarar mahaifiyarsa da zai tarar acan ko tasa sbd zuciyarsa dake Jin rashin nutsuwa da sukuni, Maa sakinah ma sosai ta shiga mummunan halin daya sakata fara ciwo me dan karfin da har saida taga likita kafin suka dauki wasu mahaukatan motoci zuwa tafiya me tsananin tsayin da zata kaisu ruwan dake qasar Wanda tacan zasu bi sakinah ta gane dajin garin ANJOM. Kwana daya da wuni sukai suna tafiya kuma saida suka dauko likita ma musamman sbd ciwon Maa dazai iya tashi koyaushe, Sun iso garin dayake bakin ruwa basu tsaya komaiba Aleey ya siya musu jirgin ruwa gabaki daya suka shiga dan barin gurin. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 62 Tafiyar wuni guda da kwana daya sukai suna zagaye ruwan da tafiya ke tsayi kafin Kaman a mafarki sakinah ta daga hannu tana nuna gurin daya saka idanuwanta jajir hannuwanta na rawa. Bakin dajin suka tsaya su aleey da Sauran Yaransa suka fidda drones dan duba duk abinda yake cikin dajin da gari ma idan akwai. Aleey ne yake riqe da iPad din dayake kallan dajin da drones dinsu suka shiga suna yawo a sama, Sauran yaran kuwa a tsaye suke da mahaukatan bindigoginsu a shirye da harbe ko dabba ce tayi motsi a gurin, NUAB ya
🏠